Kwana biyun da laurat tayi a hospital din khalid yake kula da ita,ko dogon motsi tayi sai ya tambe lafiya?hakan ba karamin birgeta yakeyi ba ganin yanda yake bata kulawa sosai,kwance take akan gadon hospital din cikin wata silky gown orange mai dogon hannu,rigan ta kama jikinta sosai ga gadon fulaninta har a wuya, zaune khalid yake ya bata baya yana latse latsen sa awaya, ahankali take kokarin tashi zaune,motsinta yasa shi juyowa da sauri,ya aje wayan yace mekike so? cikin muryar shagwaba tace banajin dadin ganin gashina ahaka,ga baki daya atakure nake, murmushi yayi yace mekike so?tace inasan nayi combing dinshi ne,ya mike tsaye ba tare da yace mata komai ba,ya bude durowar da ke gefen gadon,ya dauko wani dan karamin basket daya kawo mata mai combs da ribbons different colors,yace oya come down, ahankali ta cire zanen da aka mata rufa dashi, kaman jiri zai dauketa sai jin tayi khalid ya riko hannunta, ahankali take takawa ya zaunar da ita akan kujeran,ya zauna kan gadon,ya dauki comb yana combing kanta ahankali kaman wanda kejin yanda takeji,
Laurat kuwa murmushi tayi tace kai yaya khalid kaga yanda kake combing ne kaman bakasan yi,bani nayi dakai na,ta miko masa hannunta, smiling yayi yace bazan bada ba,am doing it in this way saboda bakida lafiya,idan kika samu sauki completely zanyi shi in a way that sai kinyi kuka, dariya tayi tace uhmmmm bazaka iya ba,yace tau yayi wait and see, tanajin dadin yanda yake mata combing ahankali,tsit sukayi ba wanda ya kara cewa wani alif,saida yagama yayi mata parking dinsa da ribbon yace tau zo ki kwanta nagama,tace nagani mana ya kunna mata camera din wayansa front camera, ahankali take kallan kanta aciki, smiling tayi tace iyyeeee sannu hair dresser, sannan ta mika masa phone din tace thank you yaya, ahankali ya dagota ta kwanta akan gadon,yasa silky bed sheet din light blue ya rufeta da shi,ba karamin kyau tayi ba, ahankali ta juya face dinta zuwa dayan gefen, ajiyan zuciya mai nauyi yayi sannan yace menene kanwata? ahankali ta juyo, idanuwanta sunyi jawur ta soma zubarda hawaye 😥😥😥😥😥 hakan yasa hankalinsa ya kara tashi, cikin magiya yace menene?menayi maki?kanki ke ciwo ne?na maki da zafi ne?dariya ta bushe da ita wadda batasan da fitowarta ba,tasa hannu ta goge hawayen nata, sannan tace yaya khalid am scared,yace scared of what laurat?tace i killed someone,kaman daga sama yaji Statement din ahankali ya juyo yace what did you just say? cikin rawar murya tace i killed someone, jikinsa ga baki daya mutuwa yayi, ahankali ya mike tsaye ya nufi kofar ya saka mata key sannan ya dawo gefenta ya zauna, ahankali ta tashi zaune tare da taimakonsa,ya saka mata pillow abayanta wanda ya karasa ta zauna comfortable, idanuwanta cike da tears ya dora hannunsa akan nata yace is okay kinji,kara fashewa tayi da kuka,ya mike tsaye ya dawo gefenta ya zauna,tare da rungumota jikinsa kamkam,yana lallashinta yana fadin is okay,calm down okay,am there for you cikin muryar kuka tace yaya khalid nima fah kasheni za'ayi,ya zameta daga jikinsa yace waya gayamaki?no one is going to kill you okay? rungumesa tayi taci gaba da kukanta........
Sunfi 30minutes ahaka sannan tayi shuru ta lumshe idanuwanta makale take ajikinsa kaman wata mage, ajiyan zuciya yayi mai nauyi yace gayaman meya faru,kada ki boyeman komai, gaskiya nakeso okay?ta bude idanuwanta ahankali ta dago kanta sama ta kalle shi,ya lumshe idanuwansa tare da budesu lokaci daya,tasa hannu ta goge dan guntun hawayen nata sannan ta fara magana kaman haka"bayan na barku wurin tare da mairo,naje cen cikin jeji na zauna naci gaba da kukana,kaman daga sama najiyo muryar ibrahim iro dan mai anguwa,yana fadin yau kam dara taci gida saboda dagani sai ke ba ubanda ya isa ya kwaceki hannuna yau,nayi babban kamu,dama nasan kina nan,tunda nabi dake ta lalama bakiji ba,inaga idan nabi ta hanyar tsiya zaki yadda, ahankali na dago kaina na kallesa, nace masa koda za'a dauki raina bazan bari yakai ga jikina ba,ya karaso guna na mike na juya zan gudu sai naga abokanan sa biyu suna dariya,ga baki daya na rikice sai na fara rokonsu akan suyi hakuri na amince zan aure shi,yaceman ina ayyi bada aure yake sona ba,shi kawai na bari ya biya bukatar sa,koda na ankara abokanan sa sun kai ni kasa,haka ya fara kokarin zare zariyar wandonsa,yana dariya yana karasowa guna,na rasa yanda zanyi,gashi banida karfin yin komai saboda ga baki daya jikina lokacin ciwo yakeman saboda dukanda inna larai taman,ya cireman hijabina tuni yakai ga jikina ya fara kokarin cireman riganda ke jikina,sai dariya sukeyi,cikin ikon Allah na samu na cijesu da hannu,suka sakeni,zasu kara kwantar dani ibrahim yace su kyaleni kawai zai iya,su tafiyan su haka suka wuce suka tsaya abakin rafi suna jiransa,haka muka soma kokuwa da shi,yana dukana duk inda ya samu,sai cizonsa nake,haka yaman lugub na kasa ko motsi,ganin yanda yake kokarin ketaman hardi yasa na fara lalabe ko Allah zaisa na samu dutsi,haka nakai hannuna akan wani dutse,na buga masa shi abayan kansa,ya fado jikina,ganin yanda jini ya fita daga kansa yasa na bangaje shi ya koma gefe,haka na mike dakyar na dinga gudu,bansan inda zani ba,saida na tashi na tsinci kaina anan"😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭kuka ta fashe da shi sosai mai tsuma zuciya ta kara shigewa jikinsa,kamkam ya rungumesa tare da lumshe idanuwansa ahankali,tanajin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri,
MRS NOOR'S NOVELS ❤️ ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...