ZAIN ZAYYAN PART 1 PAGE 35&36

1K 72 0
                                    

❤️❤️ MRS NOOR'S NOVELS ❤️ ❤️

Yau aka sallami lauratu daga hospital, khalid yakaita gidansa ya aje,tayi wanka ta shirya cikin wasu English wears riga da sket pink,ta zubo gashin kanta har gadon baya ba karamin kyau tayi ba sai kamshi take, misalin karfe goma sha biyu na rana tana kwance akan lafiyayyan gadonta tana kallan sillin,ta juya nan ta juya cen,tashi tayi zaune ta zubawa dakin na mazurunta tana kallo,dakin babba ne sosai dauke da Italian bed white ,sai durowar gadon,da bandaki ,ta sauko tare da saka wasu pink flat shoes dake gefen gadon, ahankali take saukowa daga kan staircase din, tsakiyar fallon tayi tsaye tace kai aljannah duniya wannan irin gida haka ,ko ina babba,sai kace cinema, murmushi tayi ta dinga shiga sako da lungu na gidan,ta gama ta dawo fallo tayi zaune ga tv agabanta amma batasan yanda za'ayi ta kunna ba,haka ta dauko remotes dinda ke kan center table ko wanne latsawa take na karshen tana latsawa tv ya kawo murmushi tayi tace iyyeeee,wani Nigerian film ne ake a cine plus,haka ta zubawa tvn na mazurun tana kallo, ahankali ta daga kanta sama idanuwanta busu sauka ko ina ba sai kan agogon bangon da ke fallon wanda ya nuna karfe 1:00 daidai,ta mike tsaye ta nufi kitchen,tsaye tayi a kofar kitchen din tana kallan kitchen din sama da kasa,tace uhmm tabdi toh wai su basa dafa abinci ne?karasawa tayi cikin kitchen din,tayi tsaye ajikin gas,haka ta bude durowar tanata ganin ingredients na abinci kala kala,ta bude fridge taga kayan miya dasu cabbage da carrots,ta dauko ta hau gyaran su sai wakanta take rerawa😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

Tana gama gyaran kayan abincin,ta bude durowar kasa taga pots aciki ta dauko,tsaye tayi tace toh nadaisan wannan gas ne ina matches?cen ajikin bango ta hango wani abu a sarkafe kaman lighter ta dauka,tana latsa wuta ta kawo, afirgice tace kai😲😲😲😲😲😲😲😲 sannan ta kunna gas din,ta dora abinci,cikin minti talatin,tayi jollof rice mai kayan gyara sai kamshi ke tashi,ta saka komai a kula ta rufe takai dinning hall ta aje, sannan ta koma ta gyara kitchen din tsab,haka ta haura sama,harta bude kofar dakinta sai ta rufe ta nufi dakin da yake kallanta nata,tana budewa sai na hango frame babba mai dauke da hoton ZAIN ZAYYAN,zata shiga kenan taji ana kokarin bude kofar kasa da key,da sauri ta jawo kofar ta rufe ba tare da taga hoton ba,ta shige dakinta,ban daki ta fada tayi wanka taci ado cikin wasu English wears sky blue gown,rigan ta zauna jikinta sosai,ta feshe jikinta da turare sai kamshi take,ta gabatar da sallah azzahar,harta karasa bataji shigowan kowa ba,ta fito ta zubo gashin kanta har gadon baya,tana saukowa ta hango khalid zaune a fallo cikin kananun kaya riga da wando,rigarsa sky blue same color da gown dinta,jin steps din mutun yasa shi yayi saurin juyowa idanuwansa busu sauka ko ina ba sai kan laure, ahankali yace ma sha Allahu, kallan ta yake ko kyabtawa babu 😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃 laurat ta katse shi da yaya shine ka dawo bazaka nemeni ba cikin shagwaba ta fadi, murmushi yayi yace am sorry na dauka kina bacci ne,bari naje na dauko car key muje kici abinci koh? lokacin ta karasa saukowa , murmushi tayi tace uhmmm taso muje kaci abinci,yace a ina?ta juya tare da masa nuni da dinning hall,cen ya hango ta jera dinning tsab sai kace wadda ke jiran megidanta injini Mrs Noor,

Na mazurunsa ya fiddo yace ina kika samo abinci? murmushi tayi tace a kitchen mana,ta juya ta nufi dinning hall din,tako take daya bayan daya,duk ta taka sai jikinta ya amsa ma'ana sai jikinta ya juya, flexible body ne da ita duk inda ta juya jikinta tafiya yake,ta bude kullar tayi serving dinsa, ahankali ta dago kanta sama tace yaya fah?yace na'am,ya mike tsaye yana mamakin yanda akayi haka?ta jawo masa kujera ya zauna sannan ta bashi spoon,tace eat your food, yayi smiling yace kefah?tace kaide kaci kawai,idan ka gama zanci,ya aje spoon din yace indai bazakici time daya dani ba nima bazanci ba,tace uhmmmm alright boss cigaba da cin abincin naka bari na dauko ruwa,yace kinsan inda zaki dauko su ne?tana tafiya ta juyo tace may b tare da masa blinking eyes, ajiyan zuciya yayi lokacin ta karasa kitchen din,yace anya laurat tashin wannan kauyen ce kuwa?kai there's something behind this,i need to know something about her, she's definitely hiding something,mairo bakomai ta gayaman ba saboda kwatakwata ba bakauya bace, she's very smart and wise❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Lokacin ta fito daga kitchen dauke da faranti hannunta mai gorar ruwa biyu da lemun kwali daya,sai glass cup's biyu,haka ta karaso ta zuba mishi ruwan,ta aje masa gabansa, khalid sai kallanta yake sama da kasa, tayi serving kanta ahankali takecin abincin kaman wacce akayiwa dole da abincin babu wanda ya kara cewa wani alif, khalid ya katse shurun da laurat? ahankali ta dago kanta sama tace na'am yaya,yace gayaman ya akayi kika iya aiki da gas? murmushi tayi sannan tace uhmmm ina karatun novels sosai,acen na  karanta , yayi murmushi yace that's good badan ya yarda da zancen nata ba,sai yanzu ya tuna da a kunne ya tarar da tvn,yace harda tvn a novel kika karanta? smiling tayi taci gaba da cin abincinta sannan tace eh,yace okay that's good, sannan sukaci gaba da cin abincin nasu😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

Suna gama ta kwashe komai takai kitchen,sauran abincin ta saka a plate har lokacin khalid na zaune akan kujerar dinning yana hangota a kitchen tana wanke wanke,tana gamawa yaganta dauke da plate da abinci aciki zata fita,yace ina  zakije ne?ta juyo tana murmushi tace aaah har yanzu kana nan zaune i thought ka shiga ciki,yace no ina nan dadin abincin ki ya hanani tashi,tace uhmmm zan kaiwa wancen mutun zaune sauran abincin,ya mike tsaye yace ina veil dinki?tace appp  wallahi yana daki na manta,ta aje plate din akan table dinda ke gefen kofar fita ta haura sama cikin hanzari,tana shiga dakin,bata jima ba ta fito saye da wani Arabian hijab black,wanda ya rufemata gadon fulaninta ,ta sauko tsaye ta ganshi kaman wanda ke jiranta,yace yawwa ko ke fah,kinyi kyau?tace thank you tana murmushi,ta dauki plate din ya bude kofar suka fito tare.....

Yana tsaye ajikin mota yana kallan ta tafiya take cikin natsuwa da kwanciyar hankali,kaman batasan taka kasa,ta isa gun gateman din,tsoho ne buzu wanda a haife ya haifeta,zaune a kofar dakinsa ya bada bayansa yana sauraren radio, bakin ta dauke da sallama har kasa takai, ahankali tsohon ya juyo yace ina wuni hajia,na mazurunta ta fiddo tace hajia kuma baba? sunana LAURATU amma da laure ake kirana, murmushi yayi yace sannu laure tace yawwa baba,ga abinci na kawo maka,ta mika masa plate din sai kallanta yake kallo mai cike da mamaki, khalid ne yace ka karba mana baba, ahankali Lauratu ta juyo tana kallan khalid,yasa hannu biyu ya karba yace nagode kinji?tace dame baba?yace da abincin murmushi tayi tace bakomai,ta mike tsaye tace muje toh yaya khalid,yace after you har sun juya,baba yace khalid?chak suka tsaya tare da juyowa lokaci daya, khalid yace take the car key and wait for me,ya mika mata car key din ta karba sannan ta juyawanta, khalid ya dawo ya durkusa har kasa yace lafiya baba?baba yace lafiya lau,yau shekarana goma ina gadi agidan nan wannan ne karo na farko da aka taba bani abinci,ina fatan itace matar da zaka aura? saboda kayi sa'ar mace,banan kusa samun mace mai hankali da kamala irinta ba,tasan girman mutane sosai ,khalid yayi murmushi yace baba labarin mai tsayi ne amma idan na dawo zan gayamaka komai, baba yace toh babu matsala Allah yayi albarka, khalid yace ameen sannan ya mike,cen ya hango laure tsaye tana kallan kanta acikin glass din motar sai wasa take da tongue dinta,sai smiling yake yana kallan ta,yana karasowa ya koma bayanta ya yayi tsaye cikin glass din ta ganshi tayi murmushi ta juyo ta mika masa car key din ta koma gefe tace saika dawo,ya wani ya mutse fuska yace tare zamuje,tace ina?yace i don't know too,ya latsa key din motan tayi unlocking kanta sannan ya jawo hannunta sai gefen mai zaman banza ya bude mata kofar yace shiga,yanayin da ta shiga motar ya kara bashi mamaki sosai, saboda daga ganin hakan yasan da wata a kasa,ya rufe kofar, sannan ya zagaye gefen mai driving ya shiga,ya tada motan tare da yin horn cen na hango baba ya  bude gate din,haka suka fice daga gidan laure tana waving baba maigadi,shima waving dinta yake yana Allah ya tsare,bayan fitar su khalid yace laurat?tace na'am yaya khalid tana kallan sa ta fadi haka,jin yayi shuru ne yasa tace lafiya?yace lafiya lau sunan kawai yaman dadi,tace dama sunan LAURAT unique name ne,ummahna tace HAJIA ta sakaman shi,yace ga sunan ya dace da wadda aka sakawa shi,haka suketa firan su yana driving,amma sai satar kallanta yake,laure kuwa sai kallan gefenta take tana smiling 👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄ko alama babu kauyanci a tattare da ita,Anya ruwa suna tsami banza kuwa?injini Mrs Noor 💋💋💋💋💋💋💋

MRS NOOR'S NOVELS 👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now