💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕**********vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018**************
Isar zain zayyan gidansu keda wuya ya tarar da mahaifiyars a fallo su hanifa sun sakata tsakiya sai faman zube suke mata, kamshin turarensa ne ya daki hancinsu, ahankali suka jiyo ga baki dayan,wata harara ya bankawa hanifa wacce tasa ta dauke na mazurunta da sauri,haka sukace yaya sannu da zuwa,yace yawwa,ya gidan hamdiya?tace lafiya lau ,yace okay,nan ya sunkuya har kasa yagaida mahaifiyarsa cikin sakin fuska ta amsa masa,ya koma ya zauna zuciyarsa sai bugawa take uku uku,duniya yanzu yana bakin cikin ganin HANIFA arayuwarsa wallahi,mummy tace ku bamu wuri zamuyi magana,haka suka mike suka fice daga fallon zuwa dakinsu,hanifa sai satar kallan zain take wanda ya wani cumuimuye fuska guri daya ko alamar murmushi babu,suna ficewansu mummy tace oya dawo nan,gab da ita ya zauna,ko ido bayasan su hada da ita,tayi murmushi tace kunyar me kakeji zain? yayi murmushi yace babu mummy tace alright,dama na kira ne nagayamaka cewa idan har baka samu macen da zaka aura ba toh ni na samo maka, zuciyarsa sai bugawa take kaman zata fashe shidai bayasan HANIFA wallahi,kaman daga sama yaji tace yarinyar tanada hankali tana karatu a UK final year student ce,kaga za'ayi auren naku lokaci daya dana abokinka khalid, idan yaso daga baya idan ta gama karatun nata sai ta dawo ko kuma kai ka sameta acen,harga Allah baiji dadin maganar ba amma ko bakomai yaji dadi tunda bada hanifa aka hadashi ba, lokacin ta karasa maganar tace ko kanada wani plan ne?kai ya girgiza mata da sauri tare da cewa babu,tace are you happy?yace very happy tare da kirkiro wani dogon murmushi daga ganinsa kasan bai kai zuci ba,taji dadin hakan sosai,suna gama maganar yace shi zai wuce,ta rakoshi har gun motarsa ya fice abunsa
Kan hanyarsa ta zuwa gida, yayi murmushi yace okay shiyasa khalid yace na amince da ko menene mummy zatazo man da shi, saboda ahada aurena da nashi, uhmmmm wallahi wannan ni agareni ba aure bane,auren neman masoyiyata ne wannan saboda ko a mafalki bata taba ganin irin wannan auren ba,kawai a daura nabar garin nan,wani dogon tsaki yaja mtsww aure ,aure sai ranar da LAURAT MY AMOUR zata shigo gidana sannan za'ayi biki naji da fadi,wannan kam ko maqiyina bazan bawa labari ba,haka ya isa gida yanata maganganunsa shi kadai,a fallo ya tarar da khalid kwance,ya shiga bakinsa dauke da sallama,kamar wanda khalid yake jira yayi hizip ya tashi yana amsa masa sallamar,zain ya shigo ya zauna gefensa ko alama fuskansa bata dauke da damuwa, khalid yace kaje?zain yace naje,taceman ta nema man wacce zan aura,kuma za'a hada aurena da naka,and na amince da hakan, khalid ya rungumesa sai dadi yakeji, khalid yace dama kasan mun jima muna planning muyi aure lokaci daya,zain yace hakane amma gaskiya ni ba wani bikin da za'ayi kawai a daura auren , khalid yace nima haka za'ayi,nan fah suka zauna, khalid sai tambayar sa yake wacce kalar shadda yakamata su saka bayan daurin aurensu,zain kallansa kawai yake amma ga baki daya yana nan yana planning yanda zai fara neman LAURAT SHEHU dinsa🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫
Gunsu senorita kuwa sai kwanan gajia suke,babu wanda yasan miyar da ake sha a kasar Nigeria,suna zaune a fallo suna firansu ,siyama tace yaushe Zaki fara fita aiki? senorita tayi murmushi tace gobe monday,gobe zan fara,siyama tace am so happy for you wallahi,senorita tace duk hakan ya faru ne ta dalilinku,bansan ta yanda zan saka maku ba,amma ina rokon Allah kada ya nunaman ranar da zaku nemi alfarma guna na kasa muku ita koda kuwa ta kama na bada farin cikina ne,siyama ta rungumeta jikinta tace bana tunanin yanzu akwai abinda mummy da yaya keso face farin cikinmu,senorita ta kara rungumeta kamkam ,haka suketa rayuwarsu cikin kwana biyu da ya kasance weekend ne,ranar monday bayan ta gabatar da sallah subahin ta kasa komawa bacci saboda batajin dadin jikinta,ga baki daya jin kanta take wata macen ta daban,haka ta shiga kitchen sai aiki take,ta hada musu breakfast toaster bread da orange juice , sannan ta shiga toilet tayi wanka,ta shirya tsab cikin coat pink,riga da sket,ta cikinta fara ce,hakan yasa ta saka karamin fashion hijab dinta white, takalmanta heels ne 6inches white,ba karamin kyau tayi ba,tana gaban dressing mirror siyama ta fito daga wanka daure da towel iyakacinsa hips dinta,sai karami hannunta tana goge jikinta,tana ganin senorita tace wawww wallahi ba karamin kyau kikayi ba, lokacin senorita ta juyo fuskanta dauke da murmushi tace really?siyama tace ayyi irin haka sai kiyi causing accident ko go slow, tayi wata yar matsakaiciyar dariya tace uhmmm,itama siyama shiryawa tayi cikin kananun kaya riga da sket black,tayi dressing dinta mai kyau,suka fito sukayi breakfast, sannan suka fice, straight sai babban assibitin da ke uk,inda senorita ta samu aiki,koda taje an taru sai jiran ake aga the youngest doctor from Nigeria,haka suka karasa,ana tarbonsu da flowers,suna shiga sai conference room,inda akayi introducing dinta to every employee na hospital din,aka nuna mata lungu da sako na cikin asibitin,bayan angama aka kaita direct sai offishinta,wani hadadden office ne mai dauke da kujeru da katafaren table,sai apple laptop agefe,da dan karamin basket mai dauke da different colors of biro,daga gefe sofa ce biyu,da center table da carfet,sai plasma tv karami,sai dan karamin fridge, wannan shine wurin hutawarta,flowers ga baki daya sun cika office din,ga standard ac biyu,siyama ta zauna tana juyi akan kujera tace wawww,ba karya komai is perfect,sai lokacin ta hango wani dan karamin tag agefe anrubuta DR LAURAT S siyama ta dauki tag din tana kallansa shima kansa abin kallo ne,ta mike tsaye ta da'fa mata shi jikin coat dinta,laurat ga baki daya she's speechless,siyama ta rungumeta jikinta tana tayata murna,harda kukan dadi saida laurat tayi,ga baki daya ranar ba aiki sukayi ba,haka suka koma gida sai firar hospital din suke😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
A Nigeria kuwa yau monday, khalid baije office ba,haka ya wuce kauyensu LAURAT SHEHU shi kadai,yana zuwa mai anguwa ya masa tarbo na musamman sannan suka shiga bangarensa suna magana,haka khalid yayi masa albishirin cewa laurat tana kasar waje tana karatun likita kuma ta samu mijin aure,shiyasa yazo yagayamasu,mai anguwa yaji dadin wannan albishirin sosai,amma yacewa khalid bai zama dole mutanen kauyen nan su samu labarin nan ba,dan haka zan kirawo mahaifinta nagayamasa komai na tabbatar bayada ja akai, khalid yace nima gaskiya da nafi kowa jindadin hakan saboda nafisan sai ta zama likita sai ta zo ganinku,mai anguwa yace tabbas najidadin wannan labarin naka khalidu, ahankali khalid ya saka hannunsa cikin aljihun rigarsa ya dauko bandur din naira dubu daya suka kama 100k ya aje gaban mai anguwa yace ga sadakinta,ya kara aje wasu gefe yace wannan kuma na mahaifinta ne,ya kara dauko wasu yace wadannan kuma naka ne,mai anguwa yayi zugum yana kallan yanda khalid ke fitar da kudi kaman wani safe,sai lokacin yayi murmushi yace ma sha Allahu, mungode kwarai Allah ya saka da alhairi ,yasawa auren nasu albarka,ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyaba, khalid yace ameen, sannan ya baro garin da marece,yaso yaga mairo amma bai samu yin haka ba saboda yasan yanzu suka fara zana jarabawar su ta karshe,haka mai anguwa yasa akaje har gidan malam shehu mahaifin laure aka kira masa shi🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗
Zuciyarsa na bugawa uku uku ya iso fada,daga ganinsa kasan yana cikin damuwa da bakin ciki,a bangaren mai anguwa ya isa,ganin hakan yasan da cewa ba karamar magana zasuyi ba,koda yaje mai anguwa yana dakinsa sai safa da marwa yake, bakinsa dauke da sallama ya shiga,yakai kasa yana mika gaisuwa,sai lokacin mai anguwa ya juyo yana kallansa, sannan ya zauna tare da gyaran murya yace tabbas shehu nasan kana cikin damuwa na rashin laure atare dakai,da kuma rashin sanin inda take yanzu,kada kadamu ka kwantar da hankalin ka,ni da kaina nan ni nasa aka dauki laure aka kaita birni, saboda karatu,naga alamun cewa larai zata kasheta ne kaman yadda ta kashe mahaifiyarta nafisa,dan haka nakesan ka kwantar da hankalin ka,laure tana hannun mutanen kirki,sai lokacin malam shehu ya saukar da nauyayyen numfashinsa yana yiwa mai anguwa godiyar wannan taimakon,yace sannan albishirin ka ,yace goro rankashidade,yace tau abin farin ciki ya sameka ko nace ya samemu ga baki daya saboda laure ta samu mijin aure acen birni,ya saka hannu a babbar rigarsa ya dauko 100k ya mika masa,jikinsa na rawa ya karba,mai anguwa yace wannan shine sadakin laure 'yarka,diyar margayiya nafisa,kab karkarar nan babu wacce aka taba sadakin ta ya wuce dubu biyar,amma gashi laure har dubu dari mace daya tamkar dubu,nan take malam shehu ya fara zubarda hawaye 😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥,mai anguwa yace shiyasa nake yawan gayamaku cewa ko wane yaro da irin baiwar da Allah ya masa,kaga kai Allah ya kara azurtaka ta hanyar auren 'yarda ka hanawa cigaba arayuwa,da lokacin ka koma birni da yanzu ta zama wani abu,da yanzu kana nan tare da iyalinka hankali kwance amma ka tashi ka siyawa kanka rigima da masifa,dan haka ni nace na bada dama a daura auren acen basai munje ba ko sunzo ba, malam shehu yasa bayan hannunsa ya goge hawayen nasa,yace hakan ma yayi daidai nagode nagode,mai anguwa ya kara dauko wasu 100k ya mika masa yace wadan nan kuma sunce abawa mahaifinta dadi kan dadi, malam shehu jin kansa yake tamkar wani sarki,yau kam babu shi babu larai abinda yake fadi kenan azuciyarsa,haka mai anguwa ya dauko nasa ya nuna masa,nan fah sallo ya sauya sai fira ake,farin ciki gun malam shehu kuwa tamkar wani sabon ango 😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂
💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...