ZAIN ZAYYAN PART2 PAGE 63&64

997 60 0
                                    

💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕.****** Vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018💕💕💕💕

Khalid yana murzan yan yatsunta yace kinsan me?kai ta girgiza masa,yace am getting married very soon,na mazurunta ta fiddo cikin jindadi da walwala tace wawww yaushe? khalid yace in the next two weeks,taji dadin hakan sosai,haka taketa zumudi da tsalle tana karawa,ba haka yayi expecting daga gareta ba,amma ko bakomai yajidadin ganinta cikin farin ciki,tace kashhh saidai damuwata daya ce,yace menene?tace bansan ko wacce irin macece zaka aura ba,inasan wadda zata baka kulawa,inasan wadda zata dinga taririyar ka kaman baby,banasan wadda zata dinga sakaka cikin damuwa,kaman alfarma daya,yana smiling yace tame? cikin shagwaba tace ka hadani da auntyna saboda nagayamata steps dinda zata bi wurin ganin ka zama mijin mace  daya tilo,tamkar yanda nakejin labarin wasu masoya, yayi murmushi yace haka kike so?tace eh,yace i promise da na isa Nigeria zanje wurinta saina hadaku,ya fadi haka tare da jan hancinta,tana murmushi ta rungumesa tace zanyi kewarka sosai yayana, ahankali yake shafar gadon bayanta yace nima haka, wayansa ce tayi ringing yana dubawa sai yaga driver ne ke kiransa,tare da mata dudun yace oya muje ki rakani,tare suka fito yana rike da hannunta,a fallo suka sami fawad da siyama sai fira suke , lokacin suka sauko,siyama ta juyo tana kallansu tana smiling tana fadin yaya nd senorita,yace amebo what? fawad kuwa ga baki daya ganin yanda suka fito tare rike da hannun juna yasa duk yaji wani iri, khalid yace tau my in-law am leaving,nan take fawad ya kirkiro murmushi ya mike tsaye yace alright boss safe journey,dama akwatinsa yana fallo,siyama ta jawo akwatin haka suka fito suka rakasa har fawad, khalid ya juyo yana kallan senorita wadda take kallansa ,cikin tausayawa ya shafi gefen fuskarta yace menene?tace bakomai just going to miss you,ya rungumota jikinsa yace same here,siyama tace nifa?ya hadesu ga baki daya ya rungume, sannan ya zamesu jikinsa yace alright then take very good care of each other okay?suka amsa da yes , sannan ya shiga mota yana waving dinsu ,suma haka saida senorita ta zubarda hawaye,siyama tayi murmushi ta rungumeta tace am here for you baby,haka suka koma cikin gidan fawad na biye dasu abaya, senorita straight daki ta fice,siyama da fawad suka zauna fallo sukaci gaba da firansu,amma ga baki daya firan kawai suke fawad sai son yake yasan menene tsakanin khalid da senorita(laurat)?kasa hakuri yayi dole ya tambi siyama, cikin dadin bada labari tace yayan mu ne,sun shaku ne sosai shiyasa kaga haka,yace alright amma badan ya yarda da zancen nata ba🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Bayan dawowar khalid ya bawa mahaifiyarsa labarin komai,taji dadi sosai,haka suka sha fira sosai,daga nan fah sukaci gaba da hada kayan laifensa,har dubai mummy taje tayi masa shopping lefensa tare da babbar kawarta,akwati set uku akayiwa Aisha,ga baki daya babu kayan raini aciki,ranar da aka kai kayan Aisha kasa bacci tayi, saboda kowa sai yaba kayan yake,ansa mata gwalagwalai har babu iyaka,daga ganin kayan kasan auren diyan manya ne,ranar da aka kai lefen khalid zaune yake a fallon gidansa,rike da wayansa a hannu sai kira yake kwalawa zain, saboda koda ya dawo gidan ba kowa,yau kusan sati daya kenan besa zain a idanuwansa ba,haka yayanke shawarar wucewa gidansu dan ya bincika yaji ko lafiya?ya shiga daki yayi wanka ya shirya tsab cikin kaftan  peach color,ta masa kyau sosai,komai black yayi ,yana fitowa sukayi kacibus da zain ya dawo, ahankali yake kallansa yana hawan staircase din, murmushi yayi yace haba zain,me haka dan Allah?sai lokacin zain ya dago da kansa sama ya kalli khalid,yace da akayi me? khalid yace muje dakinka inasan muyi magana,gabansa ne yayi mugun faduwa yasan dakinsa baya shiguwa saboda kayan mayen da ke ciki,yace muje naka shida ke bude mana, khalid bai masa gardama ba ya juya suka shiga ciki....

Gefen gadon suka zauna, khalid ya cire hulansa,ya maida dubansa kan zain,yace haba abokina, saboda mace daya tilo zaka maida kanka tamkar wani zautacce?me yayi zafi ne?na tabbatar tun ranar da na taka kafa nabar garin nan kabar gidan nan,kuma na tabbatar ba gida kake zuwa ba, you don't have to tell me your whereabout saboda nasan bazai wuce neman LAURAT ba,ka dubi kanka,ga baki daya ka cenza ka dawo wani mutun na daban,ga baki daya ka fita hayyacinka,dubeka dan Allah haba, wannan abun bashine zaisa LAURAT tajika ba,ko ta dawo maka ba,ga 'yan matana kyawawa,masu kyau sosai,wadanda sukafita komai,sai lokacin zain ya tanka masa ta hanyar daga masa hannu..... cikin murya kasa-kasa yace kyau?kana tunanin akwai macen da zata nunawa MY AMOUR kyau,kai kasanta tun tana karama yanda take inaga yanzu data girma, please guy kada ka batamun rai, khalid yace naji am sorry,kwana biyu mummy taceman tana kiranka baka picking why?

Yayi dan guntun murmushi yace kasan me? khalid yace no sai ka fada,yace mummy taceman naje na nemo matar da zan aura cikin two weeks idan ba haka ba zata auraman HANIFA, khalid yace wacce HANIFA?zain yace diyar 'yar uwarta, khalid yace tab ni ko kyauta aka bani ita bazan aureta ba rawar kanta yayi yawa,zain yace kaide fadi,i don't know what to do,am confused, khalid yace kada kadamu jeka daki ka kwanta baza'a rasa yanda za'ayi ba,i will think of a way out,zain ya mike tsaye yace alright aboki nagode, sannan ya fice zuwan dakinsa dama cen atakure yake adakin khalid,yasa key ya bude dakinsa ya shiga yamanta bai saka key ba kaman yanda ya saba,ya subhanallah wannan ne dakin classic guy,wanda bayasan kazanta,wanda akoda yaushe dakinsa kamshi yake,lallai so hauka ne,dakin zain ya dawo tamkar gidan giya,ko ina kwalaben giya ne,babu wurin zama,dakin ko numfashin kirki mutun bazai iyaba,ko ina kayane,komai na dakin ya debe albarka,haka ya jaye wasu kwalaben zuwa gefen gadon,ya zauna ya dauki kwalba daya ya fasa,haka ya dinga shan giya kaman yanashan ruwa  hankalinsa kwance, khalid kuwa yayi zugum yana tunanin yanda zai jewa zain da maganar auren senorita, saboda ita kadai ce macen da yasan zata iya zama da irin zain,nan take ya yanke shawarar yi masa maganar,ya mike tsaye ya fice daga dakinsa zuwa dakin zain,yana shiga😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲

Yace innalillahi wa'innailaihir raju'un har sau uku, sannan yabi dakin da kallo, cikin maye zain ke kiran wanene?wayace ka shigoman daki ba sallama?hawaye ne zafafa suka zubo masa,karo na farko kenan tunda yake da zain yaganshi da kwalbar giya a hannu,zain da ko kwalbar lemu bayaso yafisan yasha koma menene a cup,yau shine rungume da kwalbar giya,mikewa yayi tsaye sai tangadi yake kaman wanda ake ja ana dawo da shi,yana isa gun khalid ,sai jin tasss tas tas kayi, khalid ne ya wanke shi da mari biyu masu kyau,saida ya dawo cikin hayyacinsa,yasa hannu ya dafe kuncensa yana kallan khalid, cikin rawar murya yace khalid ni zaka mara? khalid yasa hannun rigarsa ya goge hawayensa,yace na rantse da Allah zan karamaka,haka yabi dakin da kallo sama da kasa, cikin rawar murya yace zain me haka?for God sake what is this? zai kara kai kwalbar da ke hannunsa baki, khalid ya fizgeta tare da jan hannunsa ya fito da shi daga dakinsa kaman rakumi da akala,suna fitowa sai ga mahaifiyar zain hajia zaynab ta shigo dauke da sallama abakinta, khalid yana ganinta cikin hanzari ya turo zain dakinsa,ya fito yana murmushi kaman ba abinda ya faru yace aaaah mummy kece agidan namu? tayi murmushi tace ba dole ba ango,ina abokin naka?gabansa ne yaketa bugawa uku uku,shurun da yayi ne yasa ta kara cemasa khalid lafiya?yace lafiya lau mummy yana daki bacci yake,tace bacci,by this time of the day tare da duba wrist watch dinda ke hannunta,yace eh,tace okay show me his room,yace na'am,tace ina ne dakinsa?,haka ya nuna mata dakinsa bana zain ba,ta shiga dakin nasa yabi bayanta,koda suka shiga baccin yake, ahankali ta isa gunsa,ta shafa gefen fuskarsa,takai bakinta zata sumbace shi akan goshinsa warin giya ya bugi hancinta,da sauri ta dawo da kanta,kai khalid ya dafe saboda yanzu bayada wata mafita sai gaskiya, ahankali ta maida dubanta akan khalid dake tsaye,tace khalid yaushe zain ya fara shan giya?gabansa ne yaketa bugawa uku uku,shuru yayi, cikin tsawa tace am talking to you,ya jawo kujera ya zauna gabanta, sannan yayi ajiyan zuciya mai nauyi yace mummy nima kaina mamakin da nake kenan

Wallahi kusan sati uku kenan yana playing hide and seek dani cikin gida,baya bari nagansa,yau ........haka ya kwashe komai ya gayamata,tasa hannu ta dafe kanta tace innalillahi wa'innailaihir raju'un, khalid zain ya halakani,zain ya gama dani,gabaki daya rayuwarsa a kasar waje yayita ace baisha giya ba sai yanzu saboda wata,kuma ko watan 'yar kauye,haba khalid what have i done to deserve this from him,what?magana take cikin muryar tausayi, khalid ya donar da kansa yana saurarenta,tace if zan iya guessing right,ya fara shan giyar ne tun lokacin da ya baro gida dana masa maganar auren HANIFA,lallai zain sai na nuna maka na isa dakai,ba wanda zai hana aurenka da hanifa,harta mike khalid,ya dago kansa da jajayen idanuwansa yace haba mummy,haba haba, meyayi zafi?bakida kowa sai zain,meyasa zaki masa dole,ki dubi halinda ya shiga saboda mace daya,yakike tunanin rayuwarsa zata kasance idan kika aura masa HANIFA?kalamansa suka kashe mata jiki sosai,haka ta koma ta zauna,tace khalid gayaman wacce macen ce zata yadda ta auri mashayin giya?wacce macen ce zata zauna da shi ahaka?babu ita sai jininsa,duk runtsi nasan HANIFA bazata barshi ba, khalid yace haba mummy kinyi kuskure babba, saboda HANIFA zata iya barinsa bare bata barshi ba,bare zata iya zama dashi ahaka jininsa bai zauna da shi,koda kuwa HANIFA ta amince ta aureshi kema kinsan ba dan Allah bane saidan yanada kudi, Dan Allah kiyi hakuri ,kada kiyi fushi dashi,kinsan fushin iyaye yana tare da fushin ubangiji dan Allah ki tausaya masa, ta saukar da nauyayyen numfashinta sannan tace hakane Khalid kayi gaskiya,wacece kake tunanin zata zauna da shi ahaka? khalid yace SENORITA 😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲

💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now