Da sassafe yau lauratu ta tashi yau ta makara sosai,amma haka tayi aikin gidan,ta gyara gidan tsab tsab,tayi karin kumallo kaman kullun,tana zaune a tsakiyar gidan zaune akan kujera ita kadai ta zuba uban tagumi,tayi zugum 😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏
Misalin karfe 7:30 ta shirya tsab zuwa makaranta,yau kam shuru take,daga ganinta kasan tana cikin damuwa yau,koda ta shiga makaranta kowa yana aji,haka ta shiga ajin jikinta a sanyaye ta zauna,ta dora kanta akan desk din idanuwanta sunyi jawur, mairo ce ta shigo ajin ta isa gun laure,ta aje jakanta akan desk din sannan ta dafa kafadarta a firgice lauratu ta dago kanta,sai hawaye ne zafafa suka zubo mata,mairo takai zaune narainarai tayi da idanuwanta kaman zatayi kuka, rungumeta lauratu tayi kamkam tana kuka kaman ranta zai fita,gaba daya students din juyowa sukayi suna kallansu, ahankali mairo ta dago kanta cikin zafin nama mairo tace menene diyan magulmata?juyawa sukayi da sauri sukaci gaba da abunda take gabansu, ta dinga shafar bayanta ahankali tana lallashinta, shigowar malamar su mai maths yasa laure ta zame jikinta daga na mairo,ta mike tsaye ta dauki excuse daga malamar ta fice cikin hanzari,malamar tabita da kallo harta fice,juyowa tayi ta tambi mairo ko lafiya?mairo tace lafiya lau batada lfy ne,malamar tace Allah ya kyauta,ta juya ta fara masu darasin yau, laure kuwa bayan fitarta daga ajin,gudu take sosai kuma kuka take,batasan ma inda zataje ba, khalid ne na hango yana tafiya da earpieces a kunnensa ga duk kan alamu fresh air ya fito yasha, ahankali ya cire earpieces din kunnensa lokacin da ya hango laure da gudu ta nufi cikin wani daji tana kuka,chak ya tsaya yana kallan kowa ya biyota ganin baiga kowa ba yasa ya nufi dajin da laure ta shigo, ahankali yake tafiya,saida ya shige dajin ga baki daya,ya hango mutun cen zaune gefen gulbi, ahankali ya nufi gunta, gefenta ya zauna, yayi gyaran murya, lokacin ne ta jiyo jin gyaran muryar mutun, idanuwanta busu sauka ko ina ba sai kan na khalid, murmushi ta kirkiro sannan tace yaya good morning? lumshe idanuwansa yayi sannan yace what's good about the morning laurat, menene? mekikewa kuka? lauratu ta kauda idanuwanta zuwa gefen ta na hagu, cikin rawar murya tace yaya khalid kai ne mutun na biyu daya nunaman kulawarsa akaina sai mairo,banida wani gata a duniya daya wuce mahaifina da wannan karatun da nake,i want to be someone in life,i want to be happy in life ,but.....kuka ta fashe da shi
Nan take tausayin ta ya mamaye mashi zuciya, ahankali ya dora hannunsa akan nata dake kan guwawunta,wani tsam taji ajikinta, lumshe idanuwanta tayi saboda wannan ne karo na farko danamiji ya taba touching dinta, ahankali ta zame hannunta daga nasa, ganin yanda tayi tsit yasa khalid yayi murmushi yace kiyi hakuri Laurat, komai na rayuwa nadan lokaci ne,ahaka khalid ya samu ya lallashi laure ,ya dinga bata labari sai dariya take harda sarkewa,hakan ba karamin dadi yayiwa Khalid ba,suna cikin haka yace wanene saurayin ki?baki ta tabe sannan tace saurayi kuma yaya?yace eh mana,tace banida ko daya amma inada miji, gabansa ne yayi mugun faduwa, ahankali yace bangane ba?tace ina da saurayi amma ban taba ganinsa ba,bantaba saninsa ba,ban tabajin labarinsa ba,bantaba ganin mai kamannunsa ba,amma ko tantama banayi wata rana zamu hadu, khalid yayi murmushi yace me sunan wannan soyayyar taki?tace soyayyar gaskiya,yace uhmmmm yanzu ke laurat idan wani yazo zaki manta da wancen ki zauna da wanda yazo? laure tayi murmushi tace ko kadan bazan iya ba,amma kuma koda hakan ta kasance duk ranarda na hada ido da wancen da nakeso sai wanda na aura ya sakeni saboda bazan iya zama da shi ba, khalid yayi murmushi yace rigi rigi kenan, laure ta turo dan karamin bakinta tace menene kuma rigi rigi?yace babbar magana ake nufi da haka, laure tayi murmushi tace rigi rigi,yace eh,tace uhmm ina dan uwanka da kukazo tare ne? khalid yace yana gida bacci yake, laure tace ankawo maku karin kumallon ku kuwa? khalid yace aaah, laure tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace kuyi hakuri laifina ne,banida wata mafita sai wannan amma idan kunada kayan abincin muje ka daukoman sai na maku mana, khalid yace aaah kada kidamu,tace no i insist,yace kinga fah kada wannan abun ya zama wata matsala ta daban, tayi murmushi tace indai wannan ne kowa kallanda yakeman kenan amma tunda Allah yasan niyarka bana tunanin da wata matsala aciki 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔,kuma nasan bazaka taba cutar dani ba, sannan wannan nauyi nawa ne,kuma promise na dauka akan cewa zanyi so please let me go, khalid yayi murmushi yace alright then tashi muje,haka suka jera suna tafiya,ta cikin dajin tabi dashi sai gasu agaban gidanda suke, khalid yayi mamaki sosai,koda suka shiga gidan bakowa aciki,daga julian sai michael,sauran sun fita jogging tare da zain,tana shiga ta gaidasu cikin harshen turanci,suka amsa mata tare da mata sannu da zuwa,tsaye tayi ajikin bango tana kallan khalid dake tsaye yana magana da julian.....
Julian ta mike tsaye ta shiga dakinsu ta dauko mata kayan abincin nasu,kicin laure ta shiga ta hura wutar,sai hayaki ke tashi, khalid na tsaye yana kallan ta,ahaka ta tada wutar ta ruru, sannan ta dora masu breakfast dinsu,indomie ce da dafaffen kwai,ta wanke plate da kulolin jiya tsab,tayi sharan gidan,komai ta kimtsa gidan ya kara haske, khalid dake manne ajikin bango yace sannu da aiki, murmushi tayi tace wane aikin?yace wannan mana,ta tabe baki tace wannan ba aiki bane hutu ne,dakin su zain ta shiga ta gyara masu makwancin su tsab,ta nade masu kayanda suka cire suka aza akan sofa, sannan ta bude windows din,ta saki labulen dakin,har yanzu akwai wuta,haka ta saka indomie da kwai din a kula ta hada komai akan faranti takai musu fallo ta aje, sannan ta wanke tukunyar da tayi aiki da ita,tana gamawa tace yaya ni zan koma school,yace aaah muje kici abinci first kai ta girgiza masa tace aaah ni na koshi kada kadamu,yayi mata rakiya har school sannan sukayi sai anjima ya dawowarsa gida,kan hanyarsa yaketa nazarin kalamanta,yaketasan yasan ko ita wacece?menene tarihin rayuwarta?wanene wannan da take mutuwar so?duk wadannan tambayoyin sune yake yiwa kansa🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Koda ya isa gidan,zain ya dawo har yayi wanka, cikin kaftan ya shirya tsab ruwan omo, yayi kyau abunsa sai kamshi yake,shima wanka yayi ya shirya cikin kaftan green,suma team dinsu sunyi wanka kowa cikin kananun kaya,fallo suka zauna kaman jiya haka Julian tayi serving dinsu,sukaci abinci suka koshi, sannan Michael da team din suka fara shirin komawa cikin gari,suna zaune zain na gayamasu abubuwan da zasu kawo masa gobe,kayan abinci ne shinkafa,macroni,sphegetti,da sauran abubuwa na gyaran abinci, sannan yace su kawo masu jan karami,su masa full sannan su siyo masa a jalka su kawo masa,tsab suka shirya, khalid da zain suka rakosu har gun motarsu sukayi tafiyan su da sunan gobe michael zai dawo ya kawo sakon, cikin gida suka koma zain yace wayayi girkin nan? khalid yace laurat mana,zain yace tazo ne? khalid yace eh tazo i thought kana gidan ashe ka fita jogging,zain yace bansan zatazo ba da banje ba wallahi,yaja wani dan guntun tsaki mtsww, khalid yace saidai wani hanzari ba gudu ba,zain yace menene? khalid yace ta fada tarkon so wanda bata taba gani ba,ayanda take bani labari she can surely die for him,Zain yace kamanya kenan? khalid yace kaman yanda kaji nafada zain, labarin ku yaso yazo daya saidai banbancin daya ne kai kasanta ita batasan shi ba,zain yayi murmushi yace khalid wallahi bansanta a mafalki nake ganinta,kuma duk na kwanta sai nayi mafalkin ta, sannan ta gayaman sunanta a mafalkin, khalid yace me sunanta?Zain yace la.......wayansa tayi ringing ahankali ya dauki wayan dake gefensa ya dora a kunne,sai yes sir yake cewa,bayan yagama khalid yace boss ne?zain yace kaima kasani mana,tashi muje mu gaida mai anguwar sannan mu fara plans din,suka fito tare suna tafiya cikin iko da kasaita,daidai gun motarsu suka tsaya , khalid ya jefawa zain key din motan,suka shiga,zain ke driving yau.
MRS NOOR'S NOVELS 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Novela JuvenilFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...