ZAISUS LIFE WRITTERS 💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝 story written by MRS NOOR'S NOVEL 💗 BY 💕 MRS 💕 NOOR'S NOVEL 💖 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Misalin karfe bakwai su hanifa suka bar gidan badan sun so tafiya ba sai dan mummy tanata kwala musu kira,goma na arziki laurat tayi musu kayan makeup ta hada musu da kayan bacci ko waccen su haka ta hada mata,bayan tafiyar su siyama tace nima yakamata na wuce gida laurat nasan dai yanzu komai ya wuce right? cikin sanyin jiki tace ina kuwa komai ya wuce?siyama wallahi banasan auren nan,siyama tayi dan guntun murmushi tace com on baby,yanzu toh the best thing shine ki koma aiki ,inaga hakan zai dauke maki hankali ki rage wannan damuwar taki,laurat tace anya hakan zaiyu?siyama tace sosai ma kuwa bari idan na karasa gida zanyi magana da mummy,kinga sai tayiwa yaya khalid magana da kanta, laurat tayi dan guntun murmushi tace hakane kuma ba matsala,nan ta raka siyama har gun motarta ta fice abunta,a harabar gidan tayi tsaye tana kara yiwa gidan kallo,gidan babba ne sosai,sai parking space mai dauke da different kinds of car naji da fadi,daga gefen parking space din kuwa gurin shan iska ne mai dauke da table da kujeru hudu sai wani dan karamin freezer,daga cen gaba kuma gidan generator ne,daga bayanta kuma dakin mai gadi ne,wanda yake zaune akan kujera yana kallan laurat da ta bashi bayanta, cikin sanyin jiki ya karasa gunta har kasa ya sunkuya ya gaisheta , cikin yar karamar muryarta mai dadin sauraro tace ina wuni baba,yace lafiya lau hajia lafiya kuwa kikayi tsaye?sai lokacin ta juyo ta dubeshi tace lafiya lau baba,zan shiga ciki saida safe, cikin girma da girmamawa yace Allah ya bamu alhairi sannan tasa kai ta fice,maigadin tsoho ne wanda a tsofe bazai wuce shekara 55years,fari ne dogo,daga ganinsa kasan bafulatanin daji ne, yayi murmushi yace uhmm ma sha Allahu gaskiya alhaji yayi sa'ar mata wannan kyakkyawa haka,gaske dai baya bari tana fitowa tunda aka kawota wannan ne karo na farko dana taba ganinta, yayi murmushi ya koma bakin aikinsa😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎
Gun laurat kuwa tana karasawa cikin gidan tayi tsaye tsakiyar fallon ta nade hannayenta biyu tana kara kallan fallon,amma ga dukkan alamu nazari ne take,ta saukar da nauyayyen numfashinta tace yaa Allah ka bani ikon yiwa mijina ladabi da biyayya in sha Allahu zanyi duk abunda ya dace wurin ganin na karkato da hankalinsa zuwa gareni dama kowa da koyo ya fara,haka ta karasa cikin kitchen din ta hau shirya girki🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗
Gun zain kuwa tunda khalid ya lallashe shi yagayamasa cewa ya manta da komai ya saki jikinsa yayi duk abunda ya dace wurin ganin ta kusanta da shi,haka yabar gidan khalid jikinsa ba kwari,ga baki daya komai ya chakude masa,ahaka ya isa gidan,yana isa yayi parking sannan ya fito yayi tsaye jikin motarsa yana sake sake aransa, nauyayyen numfashi ya saukar sannan yasa kai ya karasa cikin gidan ,yana karasawa cikin gidan wani turare mai kamshi ya doki hancinsa ga sanyin air condition daya ratsa gidan ga baki daya,bai san lokacin da murmushi ya kubuce masa ba,aduk lokacin da ya shigo gidan yakan tsinci kansa cikin jindadi da annashuwa, ahaka yabi gidan da kallo ko ina dulum,sai wasu hasken candle da yake gani a tsakiyar center table dinda yake fallon,wani iska mai zafi ya huro daga bakinsa, murya kasa-kasa yace itama she's ready to sell herself for me kenan? tambayar da yayiwa kansa kenan😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊
Gun laurat kuwa tana karasa hada girkin sannan ta hada dinning tsab,ta turare gidan ga baki daya da turaren maiduguri mai kamshin gaske,itama kanta yau ta tsinci kanta cikin farin ciki da annushuwa ga baki daya bata tare da bacin rai ko wani nadama,haka ta fada bandaki tayi wanka ta shirya tsab cikin wata silky material gown red,tayi combing kanta ta zubo gashin kanta har gadon baya,ta feshe jikinta da perfumes masu kamshin gaske ,wank light makeup tayi daga powder sai lipstick,tayi kyau abunta,wani nauyayyen numfashi ta saukar lokacin da taji an bude kofar shigowa gidan, ahankali ta saka flat shoes dinta black sannan ta nufi kofar cikin hanzari,ta murda handle din ta leko,bakowa a fallon hakan yasa ta fito tana tako daya daya kaman wacce ake roko ta taka kasa,fallon tsab ba wani haske sosai,bakowa a fallon tuni zain ya karasa dakinsa,dakinsa ta nufa tana zuwa tayi knocking taji shuru, ahankali ta tura kofar dakin ta hango shi cen kwance tsakiyar rairan akan ruwan cikinsa idanuwansa a lumshe,sai wutar da take kunne red marar haske wacce turawa ke kira da romantic light,Kara jawo kofar tayi ta rufe tana murmushi ta juya ta koma dakinta,kwance tayi akan gadon tana ta sake sake aranta,ta rasa yanda zatayi,murya kasa-kasa tace ya zanyi ? wallahi kunya nakeji,ita kadai take zancenta🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Novela JuvenilFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...