ZAIN ZAYYAN PART2 PAGE77&78

983 56 0
                                    

💕💕💕💕💕💕 MRS 💕 NOOR'S 💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕 vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

Cikin rawar jiki ya dauketa kaman baby sai hospital ganin yanda ko motsi batayi,yana isa nurses sukayi ruuuu kanta sai emergency,haka yake safa da marwa tsakanin dakin da corridor hospital din,ga baki daya a hargitse yake,ya kasa samun sukuni azuciyarsa,sai yanzu kalaman mahaifiyarsa ke masa yawo akai"Dan Allah khalid kada tsautsayi ya saka sanarda laurat cewa tanada aure nasan abun bazai zo mata da sauki ba ka barshi har sai ta dawo nasan ta yanda zan mata maganar"ya dafe kansa yace innalillahi wa'innailaihir raju'un har sau uku na shiga uku,tun 9ja saida mummy tayi warning dina,na kasa hakurin har sai kin dawo ne,yana cikin wannan tunanin wayansa tayi ringing daya alamun text ya shigo wayansa,yana dubawa sai yaga text daga amininsa zain,yana cewa"kayi hakuri na kasa hakurin zama har next week,i have something to do very urgent in Nigeria"na mazurunsa ya fiddo yace ta faru ta kare , wannan wane irin bala'i ne,ya subhanallah,gashi i wanted to prove to laurat cewa tare da megidanta nazo how will i do that?kaman daga sama yaji ance by showing her the invitation card, ahankali ya juya zuwa inda yaji voice din, ahankali yake kallan face din kaman fuskar sani wazan gani?

FAWAD AHMAD ne cikin suit dinsa black, yayi kyau sosai, murmushi yayi sannan ya karasa gun khalid cikin iko da kasaita, gefensa ya tsaya tare da huro iska mai zafi daga bakinsa,yace in law kunyi kuskure babba, khalid yace ya akayi kasan ina nan?wane kuskuren kake magana?fawad yayi murmushi yace naje gida ne na tarar da siyama tana kuka sosai kaman ranta zai fita da kyar na samu tayi shuru,ita take gayaman abunda ya faru, shiyasa nazo kuma nazo naji kana regretting akan abunda ya faru, khalid let's talk man to man yanzu, khalid yayi shuru yana kallansa, sannan yace inajinka,fawad yace uhmm bansan tsakanin ku da senorita ba,amma ga duk kan alamu kun shaku sosai,iya sanin da nayiwa laurat macece mai hakuri,da hangen nesa,try to talk to her in another way round ,zata saurareka ,idan ta nemi da taga mijin nata then sai kazo mata da shi ko kuma ku koma Nigeria tare so that ta ganshi su gana,i think it will be better, khalid yayi nisa yace your right fawad in sha Allahu haka za'ayi,ya mika masa hannu suka gaisa tare da masa godiya

Suna cikin maganar Dr ya fito cikin zanzaronsa da labcoat dinsa sai stethoscopes rataye awuyansa, cikin hanzari suka nufesa khalid yace ya jikin nata? yace ta samu sauki,dama kaman shock ne, khalid yace alhamdulillahi zamu iya ganinta yace eh amma batasan dogon surutu,yace tau sannan ya ficewansa,duk acikin harshen turanci sukayi zancen,haka nufi dakin,tana kwance idanuwanta alumshe alamun mai bacci,gashin kanta ya rufe mata fuska, gefenta khalid ya zauna fawad kuwa yana tsaye bayansa, ahankali yakai hannunsa ya gyara mata gashin nata zuwa gefe tare da shafa gefen fuskarta,nan take cikin rashin fahimta fawad ya fara tunanin wani abu a zuciyarsa kuwa cewa yayi"Anya ba khalid bane mijin nata irin wannan so da kauna"? tambayar da yake yiwa kansa kenan,sunfi 30minute ahaka sannan fawad yace shi zai wuce gida, khalid yayi masa rakiya har parking space ya wuce sannan ya dawo, shigowar sa dakin keda wuya ya hangota zaune ta jingina ajikin gadon kanta a sama sai hawaye take zubarwa,Kai ya girgiza tare da karasawa cikin, ahankali taji an dagota pillow ya saka mata abayanta,tana kallansa, kamshin turarensa yana dukan hancinta sai lumshe idanuwanta tayi ahankali lokacin ya zauna gefenta yace am sorry, ahankali ta bude na mazurunta tare da kirkiro murmushi

Khalid yace kiyi hakuri Laurat,nayi ne saboda nasan you will never disobey me,and kinfi kowa sanin bazan maki mugun zabi ba, sannan wannan dana hadaki da shi he's madly in love with you,"toh fah khalid kacenka daidai saidai bakada labari dagani Mrs Noor",nasan bazai taba cutar dake ba,laurat kuwa a zuciyarta cewa tayi"abun dariyar ka baya karewa khalid in banda abinka akwai Wanda zan so a duniya bayan ZAIN,sai kai saboda kai ne kaman irin gatanda ya jima yanasan yaman, khalid ne ya dawo da ita daga duniyar da taje ta hanyar laurat aure ba abin wasa bane,Ina son, ki gane cewa yau one month da aurenki,ina san kisan cewa akwai abubuwan da kikeman wadanda suka sabawa addini, you are somebody's else wife,ni kuma mijin wata ne,ta rausayar da kanta tace wannan auren da kake magana ba zai dauki lokaci ba zan fito,ta riko hannunsa idanuwanta akan nasa tace me zanyi da wanda bansani ba?, mezanyi da wanda baiman farin sani ba kaman shi?, mezanyi da wanda bazai taba sona ba kaman shi? yaya khalid da shi nasoma rayuwata ta soyayya taya kake tunanin zanso wani fiye da shi?dashi nakesan rayuwa?ka tausayaman ka nemo man shi,ya jinjina kansa bayan ya janye hannunsa daga nata, cikin rashin fahimta yace laurat?

Muryarsa na rawa har lokacin idanuwansu nakan na juna yace laurat shi wa?wanene wannan shi din?wanene wannan daya sace maki zuciya cikin yan shekaru? wanene shi daya rudaki haka?wanene shi da kike tunanin zai maki irin son da nake maki? wanene shi da kike tunanin shi kadai zaki iya rayuwa da shi? ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana zubarda hawaye 😥😥😥😥😥 jin tayi shuru ne yasa ya mike tsaye cikin zafin nama , cikin tsawa yace wanene shi din?saida dakin ya amsa, cikin firgici ta d'ago kanta sama tana kallansa da jajayen idanuwanta jikin har rawa yake saboda wannan ne karo na farko da khalid ya mata tsawa,yake mata magana cikin fada, jikinsa shima har rawa yake ga ac amma sai faman gumi yake kaman teku😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥😥

MRS NOOR'S NOVELS 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now