ZAIN ZAYYAN PART 1 PAGE 23&24

1K 72 0
                                    

Mairo tana fita bata tsaya ko ina ba sai gidansu khalid,ko yanzu da taje zain tagani ta bashi abincin ya ficewanta,ta dawo gida tayi wanka ta shirya tsab cikin riga da zanenta ko wane daban daban,ta saka hijabinta red dogo har kasa, sannan ta fito tana fitowa taci karo da wata kawarta mai suna HAULATU da gudu ta shigo gidan,mairo tace me haka haule?tana maida numfashi tace wallahi ina gida kwance na jiyo kuwar laure,inna larai tana cen tana dukanta tana zaginta sai kuwa take,zata kara magana,mairo ta bangajeta ta fice da gudunta,bata tsaya ba sai kofar gidansu laure,koda taje laure ta gama shara tana wanke wanke ko ina jini ne,agidan, jikinta yayi kachakacha da jini, cikin magiya tace laure waya dake ki?waya maki haka?kaman daga sama tajiyo amsar tambayar,nice nan na daketa kuma nayi mata haka ko akwai ubanda zai rama mata ne,mairo ta jiyo a hasale,inna larai ce tsaye ajikin bango kofar dakin, zatayi magana laure ta riko hannunta, ahankali ta jiyo ta kalli laure kai take girgiza mata dama da hauni,mairo tayi ajiyan zuciya ta kwace hannunta daga na laure ta fice daga gidan a hasale,bata taka birki ko ina ba sai gidansu khalid,sai hawaye take,tana isa ta shiga,ko yanzu zain ta tarar a fallo yanayin da yaganta ne yasa shi rikicewa , cikin rawar murya yace lafiya mairo?menene ?waya dake ki? ahankali take girgiza masa kai alamar bakomai,yace taya zakice bakomai gashi kina zubarda hawaye, cikin rawar murya tace ina yaya khalid?Zain ya lumshe idanuwansa yace wuce ki zauna na kira maki shi,ta shiga ta zauna a kasa,tana goge hawayenta da hijab dinta,sai ga khalid ya fito tare da zain,yana karasowa fallon yace mairo? ahankali ta dago kanta sukayi ido hudu, ganinta hakan yasa ya zauna saboda jikinsa bayada nauyi,

Yace gayaman menene?ina laurat ne?meya sameta?irin tambayoyin da khalid keyi akan laure yasa ranta yayi sanyi,zain kuwa shuru yayi yana kallan yanda khalid ya damu da laurat fiyema da yanda ya damu da Aisha, cikin muryar kuka mairo ta kwashe komai ta gayamasa, ahankali yasa hannu ya dafe kansa yana fadin innalillahi wa'innailaihir raju'un har sau uku sannan ya daga kansa sama yace tana ina?mairo tace tana gida tana aiki,zain yace aiki kuma a haka? mairo tace eh wallahi,ku taimakaman banasan ta mutu wallahi, khalid yace ya isa mairo ba abunda zai sameta bazan taba bari ba,ya mike tsaye na mazurunsa sun cika da tears ya shigewansa daki,zain yayi ajiyan zuciya ya dawo ya zauna,yace amma dai mairo ba mahaifiyarta bace koh? mairo tace haba wallahi na tabbatar da ummah nada rai da ba wanda zai taba laure a kwashe lafiya,hakan ya kara tabbatar masa da zancensa akan laure gaskiya ne,kenan marainiya ce?amma meyasa batasan yaga fuskanta, tambayar da yayiwa kansa kenan

💋💋MRS NOOR'S NOVELS 💋 💋💋

Gun laure kuwa tana gama wanke wanken,tayi wanka ta cenza kayan jikinta, jikinta yayi jawur abunku da farin mutun, fuskanta ta kumbura,kamannunta sun sauya sosai,sai wanda yasanta sannan zai san itace,kwance take akan katifarta,labulen dakin aka dago da karfi,Dan ubanki wanene zaiman tallar yau?inna larai ce, cikin rawar jiki ta mike tsaye tace kiyi hakuri,ta fito cikin rawar jiki ta dauki farantin gyada ta fice, jikinta har rawa yake,tana fitowa ta aje farantin taja hijab dinta ta rufe fuskanta,haka take tafiya tana zubarda hawaye 😥😥😥😥,bata taka birki ko ina ba sai bakin rafi inda take zama,ta aje farantin ta zauna karkashin bishiyar ta game kanta da guwawunta sai kuka take abunta😞😞😞😞😞😞😞😞😞😞😞

Gun khalid kuwa yana shiga daki ya kwanta tare da dafe kirjinsa, numfashinsa na fita ahankali sai lumshe idanuwansa yake,zain da mairo na zaune tsit ba wanda yake cewa wani alif, cikin muryar kuka mairo tace yaya dan Allah ka duboman yaya khalid,yace okay ya mike tsaye ya nufi dakin,yana shiga ya hango khalid kwance sai juyi yake, cikin hanzari ya isa gunsa,haka ya taimaka masa tare da dauko masa inhaler dinsa,ya bashi, rungume yake da shi,sai lokacin khalid ya dawo Dede amma idanuwansa sun rine sunyi jawur, ahankali yace zain ka kaini gun laurat dan Allah,zain zaiyi magana yayi shuru ganin halinda abokinsa yake ciki,ya dauki car key suka fito yana rike da hannunsa,kira ya kwalawa mairo da maryam,ta mike ta fito da sauri,haka suka fita,suka shiga motan mairo na zaune abaya,duk ta takure guri daya, cikin yar karamar muryarta tace bayada lafiya ne?zain yace eh amma da sauki,tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace yaya khalid ,zain dai baice mata alif ba,kaman daga sama zain yaji khalid yace bata gida tana bakin rafi,chak zain ya tsaya tare da juyowa yana kallan khalid wanda idanuwansa ke lumshe kansa a sama,yafi 5seconds yana kallansa sannan suka fice zuwa rafin,suna isa zain yace mun iso, khalid ya maido kansa kasa tare da bude kofar,haka ya nufi cikin dajin da gudunsa yana kiran sunan lauratu,chak ya tsaya daya isa gunta ahankali yakai guwawunsa kasa cikin rawar murya yace laurat, ahankali ta dago kanta ta dubeshi tana hawaye,kuka ta kara fashewa da shi tare da rungume khalid kamkam tana kuka kaman ranta zai fita,zain da mairo suka fito ,suka karasa aciki,chak suka tsaya da suka hango khalid da laure rungume da junansu ❤️❤️❤️❤️❤️ laurat kuka take sosai kaman ranta zai fita 😭😭😭😭😭 khalid idanuwansa a lumshe yana shafar bayanta ahankali 😔😔😔😔😔😔

MRS NOOR'S NOVELS 👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now