Safeeya ce kwance akan sofa cikin fallo tana charting a whatsapp,sai smiling take tana karawa,sanye take cikin riga da sket black english wears kayan sun zauna jikinta sosai,sai fashion cap dinda ke kanta ta mata, Aisha esha ce ta fito daga dakinta taci ado cikin shadda atamfa mai multi colors sosai,dinkin off shoulder ne ya zauna jikinta sosai kuma ya mata kyau,sai daurin dankwalinta da tayi mai suna zata buhari,sai dan karamin mayafinda ke kan kafadarta, kafafuwanta kuwa dauke suke da guccu shoes red,daga mayafinta har zuwa wrist watch dinta komai red ne,handbag dinta karama ce mai kyau, hannunta daya kuma car key ne hannunta, saukowa take ahankali daga kan staircase ba karya tayi kyau harta gaji, ahankali safeeya ta tashi zaune ta tsareta dana mazurunta ko kyabtawa babu, ahankali tace waww ba karya my baby kinyi kyau sosai, smiling Aisha tayi lokacin ne ta ida saukowa daga kan staircase din,ta juya gaba da baya tace yade? safeeya tace ba karya kin dauki na kuti, safeeya ta shiga camera dinta sai daukan pictures take, Aisha kuwa sai post take bata,bayan ta gama tace ina zuwa? Aisha tace ko kin manta yau ne walimar besty,safeeya tace wallahi na manta shiyasa kikaga ko shiryawa banyi ba, Aisha tace tashi ki shirya mu tafi, safeeya ta mike da gudu ta hau staircase din, Aisha esha ta zauna akan sofa sai selfie take tana wani turo na mazurunta da dan karamin bakinta😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
Misalin karfe biyu mai anguwa da Khalid ,zain da sauran mutanen suka zagaye garin,aka nuna masu matsalolin garin,rashin wuta ne da ruwa kuma,komai ya faru teams din na rubutawa a paper,zaune suke a harabar gidan mai anguwa,suka gabatar da sallah azzahar, sannan mai anguwa yasa a masu jagora zuwa masaukin baki,gida ne babba na zamani,dauke yake da three bedrooms,one pallor da toilet da kitchen,idan ka shiga gidan sai ka rantse ba'a kauyen bane,gidan yayi kyau sosai,haka suka shiga dakunan duka suka duba,ko wane daki dauke yake da katuwar katifa mai suna alhaji sauko mu kwanta da zanen gado da pillows uku akai,ko wane daki haka yake,sai standard fan,komai ya kankama agidan gwanin ban sha'awa,an share ko ina,an kawo masu drum na ruwa babba da bucket na wanka biyu,sai abun dibar ruwa shima biyu,haka aka shigo masu da akwatayyan su Michael ne da macen suka shigo da kayan,adaki daya aka sakasu komai da komai,har kayan lemunda suka siyo,tsab aka jera masu kayan adakin,fallon suka shiga gaba dayansu,fallon babba ne mai dauke da sofa uku,sai carfet da kayan kallo,sai fridge karami agefe,suna zaune, zain yayi murmushi yace amma dai wannan gidan aikin gwamnati ne koh? khalid yace ko kuma wani babba agarin ba,zain yace da Micheal ya bashi details din abubuwan da aka rubuta,haka ya hada takardun ga baki daya da nasa dana yan uwansa ya mikawa zain, ahankali zain yake karanta papers din,kai ya girgizawa ahankali sama da kasa, yayi ajiyan zuciya yace but michael babu batun komawarku yau saidai zuwa gobe saboda we have to make plans on this to make it easier, cikin harshen turanci yayi maganar, michael yayi murmushi yace no problem sir,haka sukaci gaba da firan abubuwan,da yake ba bangaren khalid bane shuru yayi yana saurarensu,sai smiling yake, Michael ne ya dauko firar lauratu!!!sai yabonta yake, khalid kuwa ba karamin dadi yakeji ba ganin yanda christian ke yabonta wannan ne ya nuna cewa she's perfect, khalid yace da micheal shima yayi mamakin hakan sosai saboda farko busu dauka tanajin ko zo na kasheka ba da turanci,zain tunda suke firan shuru yayi yana kallan papers din amma duk yanajin firar da sukeyi, ahankali khalid yace that girl is just superb, michael yace she's just an angel guy,haka dai suketa firan tasu😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
Gun lauratu kuwa da mairo,sun sayarda tallar su ta yau,komai babu wanda ya rage, karkashin bishiya suke zaune sai kirga kudin suke,suka hada kudaden suka zama complete,mairo tace yawwa kudin iya sun cika kinga wazobia (50) din sama tawa ce,laure tace uhmmm ni ba kudinda suka hau kan nawa,mairo tace uhmmm zan baki ashirin da biyar na dauki ashirin da biyar,laure tace dagaske?mairo tace eh mana ayyi mun zama daya,kinga tashi mu tafi kan iyya ta dawo ta fara nemana, laure tace wallahi,suka mike suna tafiyarsu suna firansu kaman kullun,yanzu kam har kofar gida mairo ta raka laure, sukayi sai anjima,mairo ta wuce kenan,laure zata shiga gida taji an kira sunanta laure? ahankali ta juyo dan taga waye,mamman ne dan gidan mai anguwa,yana karasowa ya gaidata, sannan yace dama mai anguwa ne yace na kiraki,laure tace yanzu?yace eh,tayi zugum nadan lokaci, sannan tace jeka kace ina zuwa,mamman yace tau yayi,ya juya yayi tafiyansa, sannan laure ta shigewanta gida,tanata tunanin ko meyasa mai anguwa ke nemanta yanzu?tana shiga gidan tsit ba kowa aciki,haka ta rega dakunan cen ta hango hanne kwance tana sharar baccinta,amma inna larai bata gidan, dakinta ta shige sannan tayi wanka,ta dora abincin daren,saida ta gama aikin gidan ga baki daya sannan ta shirya taje gun mai anguwa,zaune yake a fadarsa yana jan charbi,shi kadai bakowa,tana isa tayi sallama sannan takai kasa kan tabarma ta zauna, yayi murmushi yace kiyi hakuri laure daukakace Allah ya maki shiyasa nake nemanki,bakinda sukazo jiya sun sauka yau,kuma sun fara aikin nasu kaman yanda kika fada,yace wata alfarma nake nema gunki yanzu? ahankali ta dago kanta sama tace wacce irin alfarma kenan baba?yace uhmmmm bakomai bane face inasan ki dinga musu girki irin nasu na yan zamani,zan dinga aikowa da cefanan nasu ,da safe da yamma da kuma na daren, laure tayi shuru na dan lokaci sannan tace ba matsala baba,yaushe za'a fara yace ko yau ma,tace tau yayi ba matsala baba zanyi,yace nagode,ya mata godiya sosai, sannan ta mike tsaye tayi tafiyanta hankali kwance,tana isa gida,ko zama batayi ba aka aiko mamman da cefanen nasu,naman kaza ne,da kayan miya sai shinkara da wasu kayan kamshi da gyara,haka ta soma aikin cikin natsuwa sai wakar dandali take,iyyeee yaraye muyi soyayya"ahaka ta gyara kayan miyan ta saka a turmi da dakasu, sannan ta dora sanwar , shinkafa da miyar kaza tayi musu,sai kamshi ke tashi,tana gamawa tayi zugum ajikin bangon kicin din tana tunanin inda zata saka musu abincin,cen tayi nisa tace uhmmmm akace bakonka annabinka bari na dauko kawai,haka ta shiga dakinta bayan kofar dakin,ta jawo wani buhu mai dauke da kwalli babba aciki,haka ta bude kayan kicin dinda take tariya ne,aciki ta dauko kula biyu,data miya data shinkafa,ta wanke sannan ta saka abincin aciki,ta wanke tukanen tsab,sai ka rantse ba'ayi abinci dasu ba,ta dauko plate biyar da spoons harda serving spoons,ta faranti babba,akai ta dora kulolin ta jera komai tsab sai ka rantse kayan wani mai gida,ana jiran ya dawo daga aiki🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...