💕💕💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕
Misalin karfe takwas na safe laurat ta shigo uk,tana jaye da akwatin ta na gucci pink,coat ce jikinta black Sai fashion hijab dinta baqi,komai black tayi, idanuwanta dauke suke da medical glasses ba karamin kyau tayi ba,waya take tana fadin haba gani nan yanzu na shigo uk,tace uhmmm dagaske kake?bansan abinda aka gayamata ba, ta cire wayan daga kunnenta tana kallan gabas da yamma,tana kara juyawa zuwa gefen damanta sai taga khalid a tsaye yana kallanta yana smiling, cikin kananun kaya riga baka mai ratsen red long sleeve, wandonsa black,tana smiling ta isa gunsa, rungume junansu sukayi cikin so da kaunar juna,ya zameta jikinsa yace wawww my SENORITA kinga yanda kika kara kyau kuwa? ahankali ta juya tace dagaske?yace sosai ma kuwa, yayi murmushi yace so ya operation din?ta fiddo na mazurunta tace ya akayi kasan nafara aiki?yace muje ba tare da yabata amsa ba,ya jawo akwatin ta yana rike da hannunta suka isa gun motar ya bude booth ya saka akwatin ,sannan ya bude mata kofa ta shiga,suna kan hanyarsu sai kallanta yake, tayi murmushi tare da cire medical glass dinta tace lafiya ka kafeni da idanuwa?yace lafiya dr senorita naga sai wani kyalli kike, tayi murmushi tace uhmm na manta kada mu wuce gida direct mu wuce hospital, saboda i have a waiting list patient,yace yes madam,haka suka isa hospital din,suna isa aka dinga morning Dr,duk inda suka wuce haka ake gaidasu cikin girma da girmamawa,yanda take amsa masu abin yayi matukar birge khalid, saboda ga baki daya ta cenza komai nata cikin classic way take yinsa, office dinta direct suka wuce,suna shiga ta zauna, khalid kuwa kallo yabi office din da shi,yana fadin waww my SENORITA wannan ne office dinki? tayi murmushi tace sosai ma kuwa,ya zauna,yana kallanta ita kuwa ga baki daya hankalinta nakan system dinta sai scrolling through take,tsaki ta dan ja mtsww, khalid yace menene?sai lokacin ta dago kanta sama tace bansan meyasa sukeman haka ba,har ankawo patient dina daga nigeria amma ba wanda yagayaman, khalid yayi murmushi yace uhmm kiyi hakuri,ni na hana agayamaki saboda yanayin aikin ki,tace uhmmm tashi muje koh?ta dauki stethoscope dinta,ta rataya awuya sannan ta shige gaba, khalid na biye da ita abaya sai Allah Allah yake aransa saboda baisan yanda reaction dinta zai kasance ba idan taga cewa ba kowa bane patient dinta face ibrahim iro,daidai kofar dakin wata nurse tace excuse me Dr,chak ta tsaya tare da juyowa tace hey CLARA tana karasowa ta mika mata file dinda ke hannunta,ta mata bayanin na patient dinta ne daga Nigeria,ta karbi file din tana sauraren bayaninta,saida ta gama sannan ta turo kofar dakin ta shiga,tana shiga sukayi ido hudu da iro dake zaune an saka masa pillow abayansa,shima yana ganinta kallanta yake amma bai ganetaba,afusace ta juyo zata fita khalid ya girgiza mata tare da rike hannunta,ta lumshe idanuwanta sannan suka karasa ciki,mai anguwa ne zaune akan kujera suka shigo,suna shigowa ya mike tsaye yana gaida laurat tsab ta gane shi,amma ita duk busu gane ta ba,tuni ta cenza harshe zuwa hausa tana yiwa ibrahim iro tambaya yana bata amsa,tana gamawa tace clara i need his transfer file in my office now,ta mika mata file din ta ficewanta, ahankali take cire glass dinta ta maida dubanta gun mai anguwa da yayi tsaye yana kallanta aransa kuwa cewa yake wannan yar karamar yarinya ce zatayiwa iro aiki?wani abu sai kasar turai,
Dr laurat ta katse masa tunanin sa da baba yaushe abun ya fara? sannan menene sanadiyar abun? tambayar da tayi ce tadan taba khalid,dole zai fasa kwan kawai saboda baiso kowa yaganeta ba, murmushi khalid yayi yace laurat baki gane su bane?ta juyo tana kallansa,nan take ta dauke kanta daga garesa tace bangane ba, khalid yayi murmushi yace baba kaima baka ganeta ba?mai anguwa ya mata kallan tsabta sannan yace wallahi bangane ta ba, khalid yayi murmushi yace uhmm rankashidade lauratu ce fah, firgit kamar wadda aka mitsila ta juyo tana kallan khalid, idanuwanta sun rine sunyi jawur dole ta saduda ta rusuna har kasa ta gaida shi,bakin mai anguwa har awuya yace aaaaaaaah laure kece?tana murmushi karfin hali tace eh baba,yace Allah sarki dama kece likitar da ake jira,tace eh baba,yace dare daya Allah kanyi bature ma sha Allahu, wallahi bangane ki ba,ta mike tace nasani baba bakomai, ibrahim iro jikinsa yayi sanyi, cikin murya kasa-kasa yace laure?ta juyo da karfi tare da banka masa wata uwar harara sannan ta dauke idanuwanta kansa tace baba zanje na duba wasu sai na shigo zuwa anjima,yace tau Allah shiyi albarka,sannan ta juya ta fice daga dakin, idanuwanta sun rine sunyi jawur ta cika fashewa kawai ya rage tayi, khalid ya biyo bayanta yana kiran sunanta amma ina cikin hanzari ta shiga office dinta,safa da marwa ta hau yi,tana zubarda hawaye 😥😥😥😥😥 zafafa,
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...