ZAIN ZAYYAN PART 1 PAGE 43&44

1K 63 0
                                    

Misalin karfe hudu na marece ranar da khalid yabar garin zuwa village wurin zain,tsab laure ta shirya cikin arabian dress sky blue,da veil dinta babba mai dauke da stones,zaune take agaban dressing mirror tana combing gashin kanta ahankali na mazurunta alumshe,siyama ce ta turo kofar dakin ahankali cen ta hangota zaune,shuru tayi tana kallan ta,tana mamakin gashinta ne ko attachment ne, knocking tayi bayan ta shigo, ahankali laure ta juyo da comb din rike da hannunta, smiling tayi tace siyama ?siyama tana smiling ta karaso dakin ta aje handbag dinta kan gadon, sannan ta nufi laure ta tsaya abayanta,tace bani na maki,ko gardama babu laure ta mika mata comb din ahankali take combing gashin, tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace laure ya akayi gashin ki yakeda tsayi da sulbi haka?laure tace uhmm dama haka yake,kinasan kiyi gashi ne?siyama tace sosai ma kuwa, laure tayi murmushi tace kada kidamu zan nuna maki yanda akeyi, haka siyama ta gyara mata gashin nata tare da mata donut a tsakiyar kai,tayi kyau sosai,laure ta feshe jikinta da turare sai kamshi take,ta dauki mayafinta suka fito siyama sai kallan ta take

Haka suka fito,siyama ce ke driving, lauratu na zaune agefen mai zaman banza,tayi shuru bakaman yanda take da khalid ba idan suna tare,ko 30minute ba'ayi ba sai gasu cikin gidan su khalid,siyama ta gyara parking dinta,tana juyawa sai ta hango motar Aisha Accord fara a fake, tayi ajiyan zuciya mai nauyi sannan tace muje, lauratu ta bude kofar ta fito tana biye da siyama abaya,fallo suka tarar da hajia zaune ita kadai tana kallan arewa24, sallama taji ahankali ta juya tana smiling tace iyyeeeeee Laurena,tana smiling ta isa gun hajia,har kasa takai ta gaida,hajia tace zo ki zauna, gefenta ta zauna sai shafar kanta take, siyama dake zaune akan kujera tace Aisha tazo ne? mahaifiyarta tace eh tana daki, siyama taja wani dogon tsaki mtswwwww sannan ta tashi ta nufi dakin nata,haka hajia da laure keta firansu kaman jiya,hajia tace kafafuwana keman ciwo kwana biyu wallahi, laure tace stress ne,hajia tace mekikace?laure tace stress, tayi murmushi tace kinyi makaranta ne?laure tace yanzu haka ina karatun ne yaya khalid ya dauko ni,hajia tace kinasan kici gaba da karatun?laure tace eh inasan na zama babbar likita,hajia tayi murmushi tace kada kidamu bari khalid ya dawo,sai an maidaki school kinci gaba,laure ta rungume hajia saboda murna,wani sanyi hajia taji azuciyarta saboda tanasan yaranta su dinga mata haka amma basayi,tun tana magana harta gaji ta bari,haka suketa firan su laure tana mata massage a kafafuwanta tuni takai kasa zaune👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄👄

Shigar dakin siyama keda wuya ta hango Aisha kwance akan lafiyayyan gadonta tana chrting sai smiling take, bakinta dauke da sallama,amma Aisha bata amsa mata ba juyowa kawai tayi tace in-law kin dawo? siyama ta aje handbag dinta akan dressing mirror da veil dinta sannan tace eh wallahi, Aisha tace gud,ina khalid ne? siyama tace ya koma, Aisha tayi shuru tana kallan siyama wacce hankalin ta ke kan wayanta dake hannunta,tace ya koma fah ki kace?sai lokacin siyama ta dago kanta tace eh yau din nan,zaune Aisha ta tashi tace wannan wacce irin rayuwa ce?he doesn't have my time anymore, abubuwan gabansa suka sha masa kai, ahakan zamuyi auren,fada take sai kace siyama ce khalid, cikin yar karamar muryarta siyama ta mike tsaye tace tsaya nan kina blabbing ,kada ki sauko ki kama mijinki, wallahi da kinyi sakaci snatching za'a maki kinaji kina gani and there's nothing mum or i can do,tasa kai ta fice daga dakin,shuru Aisha tayi tana nazarin statement din siyama saboda komai bata gane ba,haka ta mike tsaye sanye take cikin riga da sket na atamfa,ga baki daya rabin gadon fulaninta a fili suke,dinkin nan ne mai suna off-shoulder,sai fixing dinda ke kanta na attachment har gadon baya,kayan sun matseta sosai,kana ganin shape din pant dinta,haka ta fito bako dankwali akanta,tana fitowa taga siyama zaune akan kujera,hajia ma haka sai dariya suke,cen ta jiyo murya mai zakin gaske kaman ta karamar yarinya tana basu labari,haka ta isa fallon da waya hannunta,tana isa tace mummy? ahankali ta dago kanta tace Aisha kin fito? lokacin lauratu ta dago kanta sama tace ina wuni?wata harara Aisha ta banka mata tare da dan wani guntun tsaki sannan ta zauna gefen hajia,tace new maid ce mummy? hajia ta kalleta da kyau sannan ta juya ta kalli laure wadda ga baki daya attention dinta nakan massage dinda take mata, tayi murmushi tare da girgiza kai tace aaah Aisha ba maid bace, she's my daughter, statement din yayiwa laure dadi hakan yasa ta dago kanta sama sukayi four eyes da hajia smiling tayi hajia ta lumshe mata idanuwanta, Aisha kuwa cewa kawai tayi uhmmm that's good,tacigaba da typing dinta a ways💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔

Shuru sukayi,siyama sai kallan Aisha take sama da kasa, cikin zuciyarta kuwa cewa tayi"TAB LALLAI NA YARDA ZAKI WAHALA HANNUN YAYA IDAN KIKACE A HAKA ZAKU ZAUNA"laure ta kashe shurun da yanzu hajia kamata yayi ki tashi muje kiyi strolling, siyama tace uhmmm ayyi mummy bazataje kullun haka nake da ita, laure tace aaaah yau kam zataje, siyama tace oook wooo za'a man snatching mummy, hajia tayi murmushi tace tashi muje laure,chak suka mike tsaye,hajia ta shiga dakinta danta dauko hijabinta,laure tana tsaye tana jiran fitowar ta, siyama tace inzo muje? laure tace uhmmm anya? siyama tace please,laure tayi smiling tace tau muje,ta shiga daki ta dauko mayafinta ta fito ,hajia ta saka hijabinta dogo har kasa mai hannu,siyama tace aisha bazakije ba?ba tare data dago kanta ba tace no am not going,ta tabe baki suka ficewansu,tafiya suke kan titi suna firansu anguwar tsit bakowa,siyama sai pictures take daukan laure da hajia,sai wuraren karfe shida suka dawo gidan,hajia sosai taji kafafuwanta sun saki,koda suka shigo fallon aisha tana bacci akan sofa,daya daga cikin maid din gidan ce ta fito tayi musu sannu da dawowa,hajia tace sannu dai RABI'A,tace  hajia meza'a dora abincin dare,tace tab kinga na manta ban gayamaki ba, uhmmmm gashi marece yayi,a dafa koda shinkafa ce amma naso naci tuwon semo wallahi

Lauratu ta ari bakin ta tace kada kidamu,ta mike tsaye tace RABI'A ina ne kitchen din,tayi mata nuni da wata corridor,tana gaba laure na biye da ita, smiling hajia tayi tace Allah sarki , Allah siyama i love this girl,siyama tayi smiling tace same here mum,wani mugun motsi Aisha tayi,siyama tace in-law?shuru taji sannan tace nidai mum nayi kitchen naga yanda za'ayi girkin semo,hajia tace to yau kuma da kanki siyama,tana smiling ta wuce straight zuwa kitchen din,hajia ta mike tsaye ta shiga dakinta, ahankali aisha ta bude na mazurunta tace kajiman munafurci da rana tsakiya,wai wacece wannan laure din?ta mike tsaye ta shigewanta dakin siyama,laure tana shiga kitchen tasa RABI'A ta dora ruwan tuwon, sannan suka gyara vegetables da nama da dai sauran kayan gyaran,siyama na zaune akan kujeran da ke kitchen din sai video take masu,laure tace siyama kin iya girki kuwa? RABI'A ta zaro na mazurunta ,siyama tace tab ni Allah banda ruwan zafi ba abinda na iya, lauratu ta tsaya chak tana kallan siyama tace duk girman nan naki?siyama tayi smiling tace har wani girma ne dani,aikin komai RABI'A batayi ba, Laure ita tayi girkin,suka jera komai akan dinning hall, sannan ta dawo suka gyara kitchen din tsab,siyama tace uhmmm tunda nake tare da RABI'A bata taba gyaran kitchen haka ba,Kinga yanda yayi kyau kaman ba girki aka gama ba, Laure tace toh daga yau zamu fara dani dake, siyama ta mike tsaye tace hehehehehhe lallai zakiga shirme,haka suka fito kitchen din,tsab suka gyara gidan ko ina sai kamshi yake, RABI'A itama kanta ba karamin birgeta laure tayi ba, saboda tasan da itace dako girkin bata gama ba,suna cikin haka akayi kiran sallah magrib,laure tace da siyama muje muyi sallah

Siyama tace dama yaya yace ke sallau ce,suna dariya suka shiga dakin,sanyi air condition ne ke tashi,dakin dai yana bukace da gyara sosai, Aisha ce kwance tana sharar baccinta,laure ta shige bandakin tayi arwala,koda ta fito siyama ta shimfida mata sallaya ,haka ta saka hijabin tayi sallah,itama siyama tayi sallah,suna zaune akan sallaya laure tace ki tada aunty tayi sallah da cewanta Aisha,siyama tace so kike a zabgaman zagi ,ko ta tashi bai zama dole tayi sallah ba,laure ta tabe baki tace Allah ya kyauta tashi muje,haka suka nufi fallo ko waccen su sanye da hijabin da sukayi sallah,zaune suke a fallo lokacin da hajia ta fito tayi wanka ta shirya cikin arabian dress black,tayi abunta,tana fitowa tabi gidan nata da kallo sai ga baki daya ya cenza Mata,siyama ce ta katseta da wallahi aikin laure ne bana RABI'A ba, ahankali ta juyo tana kallan laure tana smiling tayi murmushi tace aikin ki ne laure?kai ta daga mata ba tare da tayi magana ba,ta karaso fallon ta zauna tace nagode,laure tace dame?hajia tace for everything,siyama tace ki mata hausa ba mana mummy,hajia tayi smiling tace inaga ko turanci tafiki ji,siyama tace dan Allah? laure tace of course,siyama tayi wani tsalle tace nasamu kawar karatun novel,nan fah Lauratu ta hau gayamata novels dinda ta karanta na turanci,wasu siyama bama tasan da su ba, hajia sai kallansu take tana smiling,karo na farko kenan data zauna da siyama a fallo har zuwa wannan lokacin 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

****************MRS NOOR'S NOVEL

👄👄👄👄👄👄👄
                                   💋💋💋💋💋💋💋
FLASH BACK 💔💔💔💔💔💔

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now