💖💖💖💖💖💖💖💖 MRS NOOR'S NOVELS 💖💖💖💖💖💖 vote for me on Wattpad as:mamahanna2018💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
ZAIN ZAYYAN ne zaune a fallo cikin kananun kayansa sai latse latsen sa yake awaya, lokacin call din khalid ya shigo wayansa,yana dagawa yace guy kana gida?zain yace eh , khalid yace ina zuwa,bayan sun katse wayan,zain yaci gaba da latse latsen sa, cikin 30minute khalid ya karaso bakinsa dauke da sallama ya shigo gidan,zain ya juya tare da amsa masa,hannu ya basa suka gaisa,ya zauna gefen zain,yace guess what?zain yace uhmmmm i can't guess gayaman menene, khalid yayi murmushi ya gyara zamansa sannan yace Aisha is two weeks pregnant, zain yayi murmushi yace like serious ? khalid yace Allah,zain yace sharp shooter, khalid yayi murmushi yace bansan wulakanci fah,yawwa ba wannan ba ma,nazo maka da wani albishir ne,zain ya aje wayansa gefe ya tattara hankalinsa zuwa ga khalid yace name kuma?
Khalid yayi shuru na yan mintuna sannan yace nazo maka da albishirin cewa na nema maka hanya mafi saukin mallakar AMOUR dinka,wani mayen murmushi yayi mai dauke da sakonni da dama,yace gayaman menene? khalid yace uhmmmm ka rubuta man takardar sakinta ni kuma na maka alkawarin da naje uk zan nemeta na bata daga nan sai kaje neman AMOUR dinka kaga basai ka gayamata kana da aure ba koda kuwa ka gayamata sai ka sanar da ita cewa bakwa tare,what do you think?
Tunda ya fara maganar zain yake kallansa,amma yana ambatar kalmar saki gabansa yayi mugun faduwa sai yaji ga baki daya ransa ya bace zuciyarsa tana masa zugi da zafi kaman zata fito, cikin rawar murya yace khalid saki fah kace? khalid yace eh mana,dama cen baka sonta,itama bata sonka,auren neman mafita ne ba auren ZAIN ZAYYAN ba, saboda nasan auren ZAIN ZAYYAN sai ranar da aka daura masa aure da LAURAT AMOUR dinsa,zain ya dauke kansa daga kan khalid zuwa dayan gefen nasa ya saukar da nauyayyen numfashinsa yace ko alama khalid naji bazan iya sakin wannan yarinyar ba,bantaba ganin ta ba amma wallahi tausayin ta nakeji,idan zatayi iya hakurin a daura mata aure da wanda batasani ba ,ni meyasa bazan iya hakurin zama da ita ba?i can't bazan iya ba❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌
Cikin rashin fahimta khalid yace mekake nufi kenan?zain yace bazan iya sakinta ba, khalid yace uhmmmm haba zain wannan wacce irin magana ce,dan Allah ka saketa wallahi bata sonka tanada wanda takeso please let her go,kaima sai kaje ka nemi wacce kake so,zain yace wallahi bazan iya ba khalid,nan take hankalin khalid ya tashi,komai ya chakude masa, cikin rawar murya yace dan Allah ka saketa zain,zain ya mike tsaye yana kallan khalid ahankali cikin zafin nama yace meyasa kake son na saketa ne? what's your relationship with her?kana son na saketa meyasa ka bari aka aura man ita? wallahi bazan saketa ba,matata ce , sannan koda naga AMOUR she still be my wife🙄🙄🙄
Khalid ya mike tsaye shima,yace are you okay?nace ka saketa,she doesn't love you,zain yace ita ta gayamaka haka? khalid yace of course yes, she's in love with someone else let her go,kaima kaje ka nemo farin cikin ka,zain ya saukar da nauyayyen numfashinsa ga baki daya yaji bazai iya sakinta ba,gashi bai san ko wacece ita ba, amma yaji ga baki daya bazai iya ba, cikin second daya yaji ta kwanta masa arai, ahankali yake girgiza kansa dama da hauni yace khalid bazan iya ba wallahi, khalid yace kamanya bazaka iya ba?what do you mean by that?zain yace she's my family now, sannan da naje na dawo da AMOUR zanje har uk na dawo da ita nan Nigeria, khalid yasa hannu ya dafe kansa sai kalaman senorita ke masa yawo a kwakwalwar da take kuka tana gayamasa tanada wanda takeso,gashi yayiwa kansa alkwarin sai yasa zain ya saketa ,amma gashi zain ko sauraronsa yaki yi,wai me yake faruwa ne? ZAIN yace she's my wife and i want to be with her let her be, ahankali ya dago kansa sama ya dubi zain sannan yace nagode ,ya juya yayi tafiyansa, Zain kuwa ya koma ya zauna tare da dafe gefen kansa dan ga baki daya ya rasa gane meyake damun sa komai ya shige masa duhu🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
💖💖💖💖 LOVE TRIANGLE 💖💖💖
Halisa ce kwance akan lafiyayyan gadonta sai juyi take tana karawa bakowa yake mata gizo ba face Aryan,ga baki daya taji ta kamu da son Aryan,komai nasa yana birgeta, musamman shigarsa cikin manyan kaya kaftan,gashi da son kamshi,ga daukar wanka, ahankali ta saukar da nauyayyen numfashinta tace ARYAN ,
Tashi tayi zaune tace hmmm anya ahaka nake tunanin ARYAN zeci gaba da bina har lokacin da nagama gayamasa alphabet na sunana?,anya bazai gaji yadaina bina ba? tambayoyin da take yiwa kanta kenan, sannan tayi murmushi tace na rasa ZAIN ZAYYAN sannan yanzu na rasa ARYAN tab i won't let that happen not again,ahaka dai taketa shawaran yanda zata bullowa lamarin ARYAN 🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅🙅MRS NOOR'S NOVEls 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...