Misalin karfe biyar na subahin lauratu ta tashi kaman kullun tayi aikin gida,tayi komai da komai,tayi karin kumallo kaman kullun,ta debo ruwa,ta kaiwa abbanta nasa abin karin kumallon, sannan ta fito ta shiga wanka tsab ta shirya zuwa makaranta,yau kam har gugar kayan makarantar tayi a dutsin guga na garwashi,tsab tsab ta fito yau,yan faransi ta saka yau,sai littattafan uku da biro,haka ta fito gida yau,tana fitowa ta hango shagon idi a bude cen ta nufi ta siya wata jakar makaranta wadda ake sayarwa hamsin,wadda har zaren goyo ne da ita,ta saka littattafan aciki,ya bata canjinta hamsin ta karba ta ficewanta zuwa makaranta,yau kam tsaye ta hango mairo ajikin bango ajin tana jiranta, saboda yau ta danyi lati,tun daga nesa mairo ke murna data hango laure tafe,sai murmushi take tana tabi tana fadin kawalliya oyoyo kawalliya oyoyo,laure na murmushi ta isa gunta,suka rungume junansu,suka karasa cikin ajin,kaman kullun bakowa zauna akan kujerar su saboda duk sun san mairo ba wani mutunci ne da ita ba,suka zauna,laure ta cire jakarta dake goyo abayanta, murmushi mairo tayi tace iyyeee kawalliya waya siya maki?laure tace abbah ya bani wazobia biyu(100)jiya shine na tsaya na siye jakan shagon idi,mairo tayi murmushi tace kinci abinci?laure ta daga mata kai alamar eh,mairo tace gayaman gaskiya?zatayi magana sai jin sukayi yan ajin sun mike tsaye suna gaida wani malami da ya shigo da morning sir,sanye yake cikin kayansa na bautar kasa,da littafi daya hannunsa na English,yace masu sit down duk suka zauna,ya juya ya rubuta English language,pronoun ya rubuta amatsayin topic dinsu na yau,kowa ya fidda littafinsa,ya fara rubutu kaman yanda yake rubutu akan allon,mairo itama rubutun take,laure kuma ta fiddo littafin da biro hannunta amma ga baki daya hankalin ta na wajen window take kallan motan da ta shigo harabar makarantar su,kaman anyi da mairo ta juyo tare da taba laure,a tsorace ta juyo,mairo tace kin fara tunanin aljanin saurayin naki koh? murmushi laure tayi sannan ta bude littafin ta fara rubutu😋😋😋😋😋😋😋😋😋😋
Gunsu khalid da Zain kuwa tsab suka shirya da safe misalin karfe takwas na safe,suka hada komai aka saka akwatayyan a booth din motan da zasu tafi da ita,tsab Zain ya shirya cikin wasu kaftan brown sunsha aiki daga wuya har hannu,komai black yayi sai kamshi yake abunsa tamkar wani ango, Khalid ma cikin kaftan ya shirya sky blue shima komai black yayi dukansu sunyi kyau,suna fitowa ,zain yace wani hanzari ba gudu ba wazai dinga girki? khalid yace kada ka damu muje dai,ko yanzu Khalid ne zaiyi driving amma yau da GLK zasuyi tafiyar baka ce,tasha tinct sosai,sai air condition ke tashi hadi da kamshin turaren motan,horn daya khalid yayi aka wangame masa gate din,zai fita ya faka,yayi magana da gateman dinsu cikin harshen turanci ,yagayamasa zasuyi tafiya amma zasu dinga yi suna shigowa,ya dauki 50k ya bashi sannan suka fice abunsu,zain bai yadda sukabar garin hannu sake ba,saida suka shiga mall sukayi sayayyar kayan drinks da ruwan gora,da biscuits dasu chocolate,zai fito sai ya hango wata jakar makaranta ta mata pink mai kyau, murmushi yayi yace khalid sakaman jakarcen cikin kayan, khalid yace mezakayi da ita?Zain yace babu ruwanka, khalid ya dauko jakan ya saka a kayan,akayi total din kudin ga baki daya zain ya bada ATM card dinsa aka cire kudin,daya daga cikin masu aikin gurin ne suka dauko masu kayan,booth khalid ya bude aka saka kayan,pampil booth din ya cika, khalid ya bawa wanda ya dauko masu kayan 500, sannan suka shiga suka kama hanyar su,suna kan hanyarsu wayan zain tayi ringing ahankali ya rage wakar motan,ya daga wayan tare da cewa hello Michael,yace alright then on my way,ya katse wayan, khalid yace lafiya? Zain yace aaah Zain ne wai sun kusa shiga garin , khalid yace okay tau yayi kyau 😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎
Suna cikin ajin,malamin yana karantar dasu,yana gama bayanin ya fara tambayar su akan darasin da yayi musu amma kab ajin lauratu ce kawai ke bada amsa,hakan yasa malamin karason shigowa ajin saboda lauratu macece mai hazaka sosai da daukan abu cikin sauri,sai in ba'ayi tambaya ba amma sai lauratu ta samu abin cewa a ajin,1 hour 30minute yayi a ajin, lokacin lauratu ta tashi ta fito dauke da bell hannunta ta kada wanda yake nuna cenjin darasi ne,yanajin hakan ya fitowansa daga ajin,yana fitowa yace lauratu kinyi kyau yau? murmushi tayi tace thank you sir,yace your welcome ya juya yana murmushi ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️,tana juyawa taji ance laure? juyowa tayi da sauri, Ibrahim ne dan maigari tare da wasu mutane abayansa,daga ganin su kasan ba yan garin bane baki ne,hakan yasa bata masa tsiya ba,daga ganin yanda take kallansa kasan da wata akasa,yana karasowa yace baki ne sukazo shine baba yace na kawosu wurinki,tace tau naji,yace ya makarantar?tace bansani ba, yayi murmushi yace Allah ya baki hakuri ni zan koma,tace dama waya tsayar dakai,ya juya yayi tafiyansa tun ransa yana baci idan ta masa wani abu yanzu ga baki daya ransa ya daina baci indai akan laure ne,yana wucewan sa ,mutanen da ke tsaye suna kallan laure,suna mamakin taya za'a kawosu wurin yar karamar yarinya ace ita kadai zata gane abunda suke nufi, ganin yanda suke kallanta yasa tayi murmushi tace yan banza bari naji dame sukazo,ta karasa gunsu tana murmushi tsaye tayi tana kallan su kaman wata bahuwa,su uku ne maza biyu ne mace daya, cikin riga da wando,rigansu kala daya ce red mai dauke da ZAISUS FOUNDATION,haka ta karanta abunda yake jikin rigunan su,ga baki dayan su Christian's ne,macen attachment ne akanta har gadon baya,sauran mazan kuwa facing cap ce red kalar rigarsu,sai wandonsu da cover shoes dinsu black in color,ganin yanda laure ke masu kallan tsabta yasa daya daga cikin su yace,hey?
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Fiksi RemajaFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...