ZAIN ZAYYAN PART 1 PAGE 7&8

1.6K 80 0
                                    

Tafiya take sauri sauri gudu gudu kaman wacce zata bar gari da bokitin ruwa akanta,horn din mota taji wanda ya  rikitar da ita,da sauri ta koma gefen titin tayi tsaye, Mercedes-Benz ce baka ba mamaki zain ne tare da khalid,dede ita motan ta tsaya, khalid ne ya fito cikin kaftan dinsa, murmushi yayi yace yi hakuri baiwar Allah naga alamun kaman odarda mukayi ta dan rikitaki,banda kallansa da lauratu keyi babu abunda take, khalid yace dan Allah idan bazaki damu ba gidan mai  anguwa muke nema,sai lokacin ta tanka masa, cikin yar karamar muryarta mai dadin sauraro tace,just go straight sai ka shiga right hand dinka,gida na farko shine gidan nasa,shuru khalid yayi saboda tunda yake bai taba jin murya maidadi irintata ba,babban abinda ya kara birgesa turancin da yaji tayi, murmushi yayi yace okay then thank you,tace your welcome,tasa kai tabi daji ta wucewanta,kallo ya bita da shi mai dauke da sakonni da yawa,a hasale Zain ya fito yana fitowa gabansa yayi mugun faduwa lumshe idanuwansa yayi yace mayya ce hala? khalid ya juyo yana hararan zain yace wannan ta wuce mayya angel ce, Zain yace kamanya kenan? khalid ya kwashe komai ya gayamasa,Zain ya wani tabe baki yace tsarani toh, khalid yace narantse maka da Allah turanci taman, sannan guy yarinyar ta hadu fah, wallahi idan ta fita birni ta zama clean zaka rantse baturiya ce,waww she's just a damsel🧕🧕🧕🧕🧕,Zain yace kana ganin kazamiyar yarinya tana neman abinda zataci zaka wani kiranta da damsel,mtswww kai har yanzu shashane wallahi, Khalid ya juya bayansa koda zaiga sahun lauratu amma wayam baiga kowa ba,ahaka suka shiga mota, direction dinda lauratu ta masa shi sukabi,kuma cikin sa'a suka tarar da mai anguwar karkashin bishiyar da ke gaban gidansa,da mutanen sa  zaune akan tabarma🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴🤴

Lauratu kuwa tuni ta isa gida,wankin baba tayi dana inna larai,ta hada da nata duk ta wanke,tana cikin shanyar kayan sai ga hanne ta shigo gidan ko sallama babu,ko kallan inda lauratu take batayi ba saboda har yanzu bata manta agreement dinsu da ita da mairo ba hakan yasa yanzu babu ruwanta da lauratu,aikin gidan kuwa wani lokacin idan ta kwatanci cewa mairo zatazo,tsintsiya zata dauka tayita sharan karya,abun har mamaki yake bawa inna larai saboda tasan ba aikin hanne bane,sharan gida da sauran ayukan gidan, lauratu tace sannu da zuwa,banza hanne tayi da ita ta shigewanta dakin inna larai, murmushi lauratu tayi tace shairi mairo amma yar masifa ce ke wallahi, Allah nagode maka daka hadani da mairo ta siyaman girma awurare da dama taman gata ako ina,kab ta shanya kayan, sannan tayi sharar gida,ta dora sanwar tuwon dare,haka ta tuka tuwon masara da miyar kubewa,tana cikin gyaran tsakiyar gidan akayi kiran sallah magrib,ta gama aikin tayi arwala sannan ta shiga dakinta ta gabatar da sallah magrib,tana cikin lazimi da charbi ahanunta sai taji ana sallama,inna larai ce dake zaune a tsakiyar gidan akan tabarma ta amsa sallamar,yaro ne ya shigo yagaidata ko amsa masa gaisuwar batayi ba tace lafiya kuwa mamman?yace dama mai-anguwa ne yace yana yana neman laure,wani mugun faduwa gaban laure tayi, cikin rawar murya tace innalillahi wa'innailaihir raju'un ibrahim ka wulakantani,muryar inna larai tajiyo tana kiran ke laure,ke laure,da gudu ta fito daga dakin ta durkusa har kasa tace gani inna,tace aaaah nikam mezakiman, mamman ne aka aiko mai anguwa yana nemanki hala kuma da wane katon aka kamaki a daji yau,tuni idanuwanta suka cika da galla, ahankali ta Lumshe idanuwanta suka zobo tamkar wani fanfo,inna larai tace awww jeki cen ki masu kukan danni bazanje shedun ko wacce yar iska ba dan ban aikeki shiga daji da shi ba, cikin sanyin jiki lauratu ta mike ta saka takalmanta ta fice cikin wani dogon hijabi baki har kasa,tana tafiya tana goge hawayenta da bayan hannunta,tuni idanuwanta suka rine sukayi jawur🙄🙄🙄🙄🙄

Tana isa kofar gidan mai anguwa,ta hango shi zaune da matasa maza biyu sai shi dake zaune akan kujerarsa da rawaninsa da babbar rigarsa fara,tana isa,tayi sallama ta durkusa har kasa takai gaisuwa kanta a kasa tace gani baba? yayi murmushi yace ki zauna mana laure,ta cire takalmanta ta zauna har lokacin kanta a kasa yake bata hada idanuwa da kowa ba,a gefen damanta kuwa khalid ne da Zain, khalid sai kallanta yake ko kyabtawa babu,zain kuwa aransa sai cewa yake "wani sabon munafurci ne wannan ko kuma al'adar garin ce mata basa kallan maza?"mai anguwa ya katse komai da wannan ita ce LAURATU amma mu da laure muke kiranta saboda sunan yamana tsawo,ita ce diyar malam shehu kab kauyen nan babu mai jin yaren nasara sai ita,tanada kokari sosai ako wane bangare,arbiya dana bokon,ko baki mukayi ita nake kira suna fadi tana fassaraman, shiyasa banajin tantamar zuwan kowa garin nan indai daga birni zaizo,tanada kunya sosai,sai yanzu hankalin laure ya kwanta da ta gane dalilin kiran nata,tayi ajiyan zuciya mai nauyi tare da yiwa Allah hamdala a zuciyarta,mai anguwa yace ungo nan laure ki karanta sai ki fahimtar dani abunda takarda ke nufi,sai lokacin ta daga kanta sama tasa hannu biyu ta karbi takardar,ta koma ta zauna, ahankali ta cire takardar daga envelope dinta ta budeta,cikin harshen turanci take karatun takardar sai ka rantse wata baturiya,shima kansa zain din ba karamin tafiya da hankalinsa tayi ba,baki ya saki yana kallanta ahankali though ba wani ganinta suke ba,gefen fuskarta kawai suke gani,mai anguwa ne kawai ke kallanta tsab,tana gamawa,ta juya harshe zuwa hausa tace baba wannan takardar tana dauke da cigaban kauyen nan , sannan da masu aikin gona,da kuma sauran jama'ar garin,wannan takardar tana nuna cewa an aiko wani da yazo yayi aiki acikin kauyen,tare da gano matsalar garin, saboda ataimaka masu da abubuwan da suke bukata na rayuwar dan adam, musamman gefen ilimin zamani, sannan ba daga gwamnati bane,daga wata kungiya ce mai zaman kanta,amma kuma tana aiki dasa hannun gwamnatin,Tau suna bukatar hadin kan yan garin ga baki daya musamman mai anguwar garin Kai kenan,ta nade takardar ta mayar envelope dinta ta mika masa, khalid da Zain kuwa ga baki daya lauratu ta tafi dasu wata duniyar ta daban,mai anguwa yace tau nagode laure jeki gida sai na kara kiranki,ta amsa da toh baba saida safe,ta juya ta saka takalmanta ta fice abunta,kallo zain yabita da shi yana mamakin ko wacece ita? Khalid yayi murmushi yace Allah shi taimakake laure tashin nan kauye ce?mai anguwa yayi murmushi yace sosai ma kuwa khalidu laure anan aka haifeta,anan ta tashi,a kuma nan take karatu,tunda ta tashi da kokarinta muka ganta musamman gefen addini,na zamanin kuma yanzu shekara biyar kenan da aka bude makarantar,masu yiwa kasa hidima(NYSC)sune suke karantar dasu karatun,kuma cikin ikon Allah ita kadai ce ke gane karatun sosai,harta farajin yaran nasara, mahaifinta yanasan tayi aure amma nina hana saboda inaji ajikina cewa itace zata taimaki garin nan namu,shiyasa komai nafisan nasata musamman idan yazo da irin haka, khalid yayi murmushi yace ma sha Allahu, gaskiya kunyi dace saboda babu wanda zaiji abunda tayi yanzu ya dauka anan take karatu,mai anguwa yace hakane gaskiya,toh ko wanene cikin ku aka turo dan yamana wannan abun alhairin?

Khalid yayi saurin amsa tambayar da gaba dayan mu ne ranka shidade,zain kuwa shuru yayi yana saurarensu,amma ga baki daya tunaninsa ya koma akan lauratu,mai anguwa yace tau madalla,yaushe zaku fara ?saboda abayanin ku naji kunce wata shida ne ga baki daya, khalid yace bamuda matsala duk lokacin da kuka bamu dama ashirye muke,mai anguwa yace toh ma sha Allahu na baku damar farawa ako wane lokaci kukeso,zansa agyara maku masaukin baki, khalid yace mungode ranka shi dade mu zamu koma,haka suka mika masa hannu suka gaisa, cikin girma da girmamawa sannan suka mike suka fice abunsu,kan hanyarsu ta koma cikin gari,zain yace guy me sunan yarinyar nan? Kaman daga sama Khalid yaji tambayar yace lauratu,zain yace i know her,wani taka birki yayi da karfi wanda yasa sukaje gaba da baya, Khalid yace kasanta kuma? A ina kenan?zain yayi ajiyan zuciya yace mu isa gida first zan baka labari, khalid yace okay then ba matsala,haka suka karasa gida,sai firan lauratu khalid keyi,shi kadai danko tanka masa zain baiyi ba,aransa kuwa sai cewa yake"anya lauratu mutun ce?side view dinta daya da wacce nake gani a mafalki, muryar su daya?komai nasu daya,what is going on?ko dai gizo ne takeman ko kuma na fara samun tabuwar hankali ne,anya ba gamo nayi ba?"tuni suka isa gida khalid har yayi parking,yafi minti uku yana kiran sunan zain amma shuru ko jinsa ba yayi,dafa kafadarsa yayi afirgice ya juyo,abun saida ya bawa khalid mamaki sosai,yace menene are you okay?zain yace am fine guy,komai normal wallahi,kawai dai ina tunanin yanda zan zauna garin ne nikadai, khalid ya bude door din yana murmushi,saida zain ya fito ya zagayo sannan khalid yace kada kadamu tare zamu zauna garin har sai lokacin da zaka dawo, though dai kasan munayi muna shigowa cikin gari ne,so keep calm,zain yace haba guy dagaske? khalid yace sosai ma,haka suka karasa cikin gidan suka fara shirye shiryen wucewa zuwa kauyen gobe🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄

Laure kuwa tana isa gida,a tsakiyar gidan ta tatarar da inna larai da hanne sunacin abincinsu hankali kwance, ta shigo bakinta dauke da sallama,amma babu wanda ya amsa mata,ta durkusa ta gaida inna larai,inna larai tace toh uwayen gaisuwa nagode,ta mike tsaye zata shiga dakinta,inna larai tace munafuka zonan, lauratu ta juyo cikin sanyin jiki tace gani,inna larai tace je kiyi wankin hanne na makaranta sannan ba ruwa agidan dan haka kada ki kuskura barin gidan nan gobe ba tare da kin cika komai ba koda kuwa robar kasari ce, lauratu tace tau inna Allah ya kaimu,ta mike tsaye ta shigewanta daki,kan katifarta ta kwanta sai hawaye take zubarwa, cikin muryar tausayi take magana, Allah kai ne gatana kabani farin cikin da nake bukata,kasan bakin cikina da damuwata ka yayeman su dan darajarka, sannan taci gaba da kukanta sosai kaman ranta zai fita,tana kwance aka kira sallah isha, cikin sanyin jiki ta fito tayi arwala sannan ta gabatar da sallah isha,Koda ta fito su inna larai sun shige dakinsu,sai dariyar su kakeji da ita da hanne,tana gama sallah taji shigowar mahaifinta yana sallama,ta fito cikin hanzari tana amsa sallamar,ta karbi jakar hannunsa, sannan ta shimfida masa  tabarma,ta kawo masa abincinsa,yaci ya koshi ta kawo masa ruwan wankin hannu ya wanke,ta dauki kwanukan takai gun wanke wanke ta aje,ta dawo gefensa ta zauna, yayi murmushi yace ya karatun?tace lafiya lau abbah,yace ankusa kammalawa kenan?tace in sha Allahu abbah,yace tau Allah yayi jagora,ni zan shiga ciki na kwanta,amma ga wannan,ya saka hannunsa a aljihun rigarsa na gaba ya dauko dari uku,yace ga dari biyu ni zan rike dari, murmushi tayi tace aaah kabani darin sai ka dauki dari biyun,yace aaaah,dakyar ya yarda ya bata dari ya dauki dari biyu,ya shiga dakinsa dake gefen na inna larai,duk maganar da suke da hanne yanajinsu,ya tausayawa laure sosai, laure kuwa ta nade tabarmar ta shiga kicin ta debo  abinci aroba taci sannan ta shigewanta daki danta kwanta,taji dadin kudin nan da mahaifinta ya bata,dama cen tanasan sayan littafi,haka ta boye kudin karkashin pillow ta kwanta,amma bacci ya gagara daukanta,sai tunanin wanda take mafalki take ma'ana ZAIN ZAYYAN 🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄duk ta runtsa shi take gani,ahakan bacci ya dauketa🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔tana mai rokon Allah daya hadata da ZAIN ZAYYAN a fili taganshi yaganta,su kasance tamkar masoyan da suke a mafalki 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍

MRS NOOR'S NOVELS 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now