Dariya take harda hawaye,mairo ce da laure zaune karkashin bishiyar da suke zama sai labari mairo ke bata,laure kuwa sai dariya take,laure tace nidai tashi muje mu katso mangwaro,mairo tace tab dake dawa zaki?laure ta wani turo dan karamin bakinta tace da kawalliya dita Mana,mairo tace amma fah yau Allah bazan duba maki ba,laure tace naji nidai mu tafi,suka mike suka nufi wani tree na mango,tafiya suke suna rike da hannun junansu,daidai mango tree din suka tsaya,laure ta juya dama da hauni bataga kowa ba, sannan ta dage sket dinta sama,ta dale tree kaman wani biri,mairo sai murmushi take tana Allah babu ruwana,kiyi maza ki sauko,haka laure ta dinga kabo masu mangwaro tana jefowa mairo,suna cikin haka sukaji maganar maza, ahankali mairo ta juyo,laure na a sama tana fadin su waye?amma taji shuru hakan yasa itama tayi shuru ta natsu,ina juyawa sai na hango khalid da zain tafe suna fira, ahankali mairo tace ma sha Allahu amma saurayin nan ya hadu,gab dasu suka karaso, khalid ya katse mata tunaninta da kawalliya dinmu? murmushi tayi tace yaya khalid kai ne yace eh nine,me kike anan?shuru tayi tana murmushi,yace yanaga mangwaro hannunki,dake dawa kike ne?mairo ta bushe da dariya tace yaya khalid tare da laure nake,tana kan icce , ahankali ya daga kansa sama cen ya tsinkayota kan tree hankalin ta kwance,ko jinsu batayi hankalin ta nakan wani mango data hango, khalid yace sannun ki da aiki? ahankali ta sunkuyo da kanta,ido biyu sukayi da khalid,na mazurunta ta fiddo tare da bude baki,tace yaya khalid? Yace oya come down,tace aaah ni bazan sauko ba,yace nace ki sauko,tace tau naji,mairo mango nawa na katso?mairo tace shida ne,tace tau,ganin kawai sukayi ta tumayyo a kasa,kallan khalid take tana smiling,tace ya akayi kasan ina nan?yace uhmmmm naje gida akaceman bakya nan,kuma nasan bazaki wuce gidansu mairo ba da nan bishiyar ba,ta saka takalmanta sannan tace toh muje? zain yana gefe,yana kallan dramar su,sai smiling yake,yana kallan laure da ta bashi baya ,aransa kuwa cewa yayi i know this voice?but who is she? khalid ne ya katse masa tunanin sa da aboki meet laure?laure ga abokina wanda mukazo tare,ba tare data juyo ba tace yaya aboki ina wuni? khalid yace bazaki juyo ba?tace kunya nakeji yaganni akan tree,dariya suka bushe da ita har shi zain din......
Mairo tace tau muje bakin rafi mu zauna koh?laure ta shige gabansu tana tafiya sauri sauri gudu gudu, khalid yace aaaah wayake binki ne? cikin yar karamar muryarta tace babu tare da girgiza masa kai, yayi murmushi yace aboki kaganta koh?zain yace banganta ba nadaiji voice dinta, saboda taki bari naganta,haka suka isa bakin rafi,suka wanke mangwaron, sannan ta dauki daya,tace laure ki dauki daya ,kibawa yaya da abokinsa daya daya,haka laure tayi sannan tace saura biyu,laure tace bani kayana ,mairo tace aaaah raba daidai zamuyi,laure tace ke kika hau ne koni na hau?mairo tace ke kika hau,amma ayyi ni nake dubawa, khalid da zain sai dariyar su suke,haka suka zauna,zain sai kokarin yaga face dinta yake amma hakan ya gagara saboda ta jawo hijab dinta har a goshi ta rufe fuskanta,saidai kawai yaji voice dinta, misalin karfe 5:30 laure ta mike tsaye tace mairo ni zanje gida nayi aiki,sai mun hadu a dandali kenan?mairo tace aaah ayyi tare zamuje, khalid yace aaah mairo kina nan batta taje tunda batasan zaman mu anan,mairo tace hakane kuma yaya khalid ,laure tace uhmmm ba haka bane,bazaka gane ba,nidai sai nazo anjima,yace tau agaida gida,haka ta ficewanta ba tare da ta bari zain yaganta ba, khalid yayi murmushi yace mairo dama laure tana hawan tree ne?mairo tayi murmushi tace dama nagayamaka she's very funny idan ta tashi,kawai dai dan bata samun yanda take so ne, khalid yace Allah sarki,komai zaizo karshe,mairo tace dagaske zakaje dandali yau?yace eh mana zanje,amma zaki nunaman hanne?tace meze hana kada kadamu,kaifah abokin yaya?zain yayi murmushi yace meze hana idan kun gayyaceni,mairo tace Tau an gayyace ka kazo dandali yau,zain yace tau angama,sun jima mairo tanata basu labarin dandali garin,sai murmushi suke,zain kuwa ga baki daya ya kasa samun sukuni akan rashin ganin laurat,amma har yanzu muryarta yakeji tana masa busar sarewa a kunnuwansa,sai murmushi yake yana smiling 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍
*************MRS NOOR'S NOVEL 🌺🌺
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...