💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕 vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
Da sassafe hajia zaynab ta shirya dan ta koma Nigeria, senorita ita da kanta takaita airport bayan tafiyar ta, senorita ta dawo gida ga baki daya taji batajin dadi,dare yayi ta kasa runtsawa ga baki daya jin kanta take kaman ba ita ba,ta kasa samun sukuni da natsuwa azuciyarta ,haka dai gari ya waye mata ta nemi baccin ta rasa,sai jin take idan ba kuka tayi ba bazata samu sukuni ba,haka bayan ta gabatar da sallah subahin ta zauna tayita zubarda hawaye akan dalilin da itama kanta batasan kanshi ba,💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
Siyama kuwa da sassafe ta wuce school, misalin karfe goma sha biyu na rana ta fito daga school ,take MacDonald taci abinci sannan ta dawo gida,tayi wanka ta dawo fallo ta kwanta cikin wata english wear red har kasa mai hannun shimi rigan ta mata kyau sosai,tana zaune tana kallo akayi knocking, ahankali ta tashi ta nufi kofar ta bude tana budewa taga fawad tayi murmushi ta bashi hanya ya wuce gefe ya dawo yayi tsaye yana kallanta,tana juyowa sai akan kirjinsa taji kanta,kamkam ya rungumota yana saukar da nauyayyen numfashinsa cikin yar karamar murya yace yaushe zamuje Nigeria i want to be yours alone baby?tayi murmushi tana shafar gadon bayansa tace by next month zan gama final exam dina sai muje koh?yace alright then sannan suka karaso fallon suka zauna,zaune take akan cinyoyinsa hannayenta biyu akan kafadarsa sai smiling take tana karawa,yace ina SENORITA?ta lumshe idanuwanta tace tana calfonia wurin aiki,yace uhmmmm she's so hardworking bata zama in one place,siyama tace shiyasa banasan karatun health,nan dai ta kara shiga jikinsa ta kwanta,fawad kuwa harga Allah yau yaso ganin senorita idan yaganta yakan kasance cikin farin ciki da annushuwa,amma dole ce zatasa yamanta da ita tunda she's married already,haka ya rungume siyama tare da lumshe idanuwansa 😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔
Hajia zaynab kuwa bayan isarta Nigeria,driver ta kira yazo daukanta,tayita kiran zain amma wayansa akashe,haka ta isa gida,hanifa da hamdiya sai tsalle suke suna karawa,haka ta shiga tayi wanka ta fito ta zauna a fallo,hanifa ta kawo mata lemu tana sha suna fira,kaman daga sama sukajiyo sallama ga baki dayansu suka juya bakowa bace ta shigo sai Aisha matar khalid cikin hijabinta dogo har kasa, fuskanta dauke da murmushi ta karasa fallon ta durkusa har kasa ta gaida hajia zaynab, HAJIA ZAYNAB tana kallanta ta amsa mata sallamar sannan tace Aisha ko matar khalid?tace eh, sannan tace ma sha Allahu ta shi ki zauna mana,haka Aisha ta mike ta zauna akan kujeran da ke kallansu, sannan suka gaisa sosai,hajia zaynab tace khalid fah?sai lokacin ta saukar da nauyayyen numfashinta tare da sunkuyar da kanta,jin tayi shuru ne yasa hajia zaynab tace talk to me Aisha lafiya kuwa?
AISHA tace uhmmm zuwan da nayi kenan mummy,tuni takai guwawunta kasa ta hade hannayenta biyu cikin rawar murya tace dan Allah mummy ki taimaki rayuwa ta,dan Allah ku rufaman asiri wallahi ban shirya rabuwa da khalid ba dan Allah,mummy ta mikawa hanifa glass cup din hannunta ta riko hannun Aisha tace bangane ba?ki fahimtar dani menene? Aisha ta fashe da kuka,haka hajia zaynab ta dagota ta rungume ta jikinta tana lallashinta ,da kyar ta samu tayi shuru,tasa aka kawo mata ruwa masu sanyi tasha sannan tace gayaman menene? Aisha tace jiya......................ta kwashe komai ta gayawa hajia zaynab , ahankali jiya hajia zaynab ta dago habarta tace zain nawa ya harbi khalid?aisha tace eh mummy yanzu haka yana hospital, cikin rawar murya tace innalillahi wa'innailaihir raju'un har sau uku sannan tace garin ya? meyayi zafi haka?they are friends fah, Aisha tace wallahi mummy bansani naji kawai zain yana maganar yarinya,bansan ko wacce yarinya yake magana ba, ahankali hajia zaynab take nanata yarinya kuma? wannan wacce yarinya ce ta shiga tsakanin su haka zain harda amfani da gun
Hanifa bani phone dina, cikin rawar jiki ta tashi ta shiga dakinta ta dauko mata wayanta,ta mika mata,nan take ta hau dannawa zain kira amma wayansa akashe, tayi dan guntun murmushi tace no wonder ya kira ni jiya yaceman na dawo yasan abunda ya aikata kenan,yanzu ina khalid din?aisha tace yana hospital tare da mummy,tace babu matsala muje mana,nan ta saka mayafinta dake gefenta suka wuce ga baki dayan su harda su hanifa😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔😔
Gun zain kuwa tun jiya daya rufe kansa cikin gidan,bai fito ba,sai kuka yake kaman wani karamin yaro,yanzu kuwa kwance yake akasa, idanuwansa sunyi luhu luhu daga ganinsa kasan yayi kuka na fitar hankali 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
WANENE KHALID?
KHALID A MUHAMMAD matashine dan shekara 30years aduniya,yayi ga baki daya rayuwar sa a kasar uk, yayi karatun medical doctor kuma business man ne,yana aiki karkashin yayan mahaifinsa wanda yake da wani hospital mai suna ZAISUS CLINIC,shine babban Dr a wannan hospital din,mutun ne mai hakuri da hangen nesa,bayada san hayaniya,ga hakuri da tawakalli,tun tashinsa bai taba san wata budurwa ba sai AISHA wacce a yanzu itace matarsa tana dauke da cikin dansu na farin,su biyu ne Allah ya mallakawa mahaifansa da shi da kanwarsa kuma autarsu SIYAMA wacce suke kira siyybaby,mahaifinsa asalin dan kebbi ne cikin garin zuru amma aiki ya kawo su zama garin sokoto,duk wani gata babu wanda busu samu gun mahaifansu ba,sun samu tarbiya sosai, mahaifin babban dan kasuwa ne,hakan yasa bai fiye zama gari ba,amma duk bayan 5month yakan dawo gida,ko lokacin auren khalid yazo,shi ya bada auren LAURAT SHEHU SENORITA AMOUR ga ZAIN ZAYYAN,wacce ya samu labarinta gun mahaifiyar khalid HAJIA NADIYA MUHAMMAD itama haifaffiyar yar sokoto ce cikin ka'oje bafulatana ce gaba da baya, mahaifiyarta ta jima da rasuwa ta tashi hannun mahaifinta ta samu kulawa sosai,ya kasance babban alami ne cikin ka'oje
Khalid bayada wani aboki da ya wuce ZAIN ZAYYAN koda yaushe suna tare hakan yasa mahaifansu busu damu dasu ba saboda ga baki dayansu sun san right and wrong 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕Bayan isarsu hajia zaynab hospital din straight sai dakin da khalid yake kwance suka shiga,kwance yake yana bacci ansaka masa bandage da hannu,hajia nadiya mahaifiyarsa tana gefensa zaune tana karatun al-qur'ani taji sallama, ahankali ta d'ago tana ganin su tayi murmushi tace hajia zaynab tare da mikewa tsaye suka rungume juna, sannan ta zauna akan dayan kujera tace ya mai jikin?tace alhamdulillahi gashi nan ,su hanifa suka gaidata tare da tambayar mai jikin?tace alhamdulillahi,hajia zaynab tace wallahi bansan komai akan wannan lamarin ba saida Aisha tazo take gayaman,hajia nadiya tayi murmushi tace haba dai ayyi wannan bakomai bane kawai bacin rai ne da shairin zuciya kuma kinsan dan adam baya wuce kaddarar shi,hajia zaynab tace wallahi harda hauka acikin wannan lamarin, lokacin khalid ya bude idanuwansa ,yana juyowa yagaida hajia zaynab,tayi murmushi tace ya jikin?murya kasa-kasa yace alhamdulillahi,tace sannu,sun jima a hospital din sosai,duk inda ranta yake inyayi dubu ya bace,ahaka tabar hospital din sai fada take suna kan hanyarsu ta zuwa gida,har suka isa gida kiran zain take amma wayansa akashe sai tsaki take jaaa❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌ ❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌❌
MRS NOOR'S NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Novela JuvenilFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...