💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕 vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
Yau aka daura auren AISHA S ABUBAKAR (ESHA) da DR KHALID BASHAR ,daga nan aka wuce gidansu khalid inda magabatansa suka bada auren LAURAT SHEHU ga ZAIN ZAYYAN nan fah aka daura auren ko wannen su,Koda aka daura auren ZAIN ZAYYAN baya wurin,daga wurin daurin auren khalid yayi tafiyansa,Dan haka yan uwan mahaifinsa su suka zama madadinsa,sai tayasu murna ake,kowa yaci yasha,babu wanda yayi complaining,farin ciki gun hajia zaynab mahaifiyar zain ba'a cewa komai,daga ita sai yan uwan mahaifinsa da nata sukayi bikin,gidansu khalid kuwa matsayin mutun biyu aka wanke sai tayata murna ake,bakinta koh rufuwa bayayi,haka khalid ya dawo gida yayi wanka ya kwanta yana hutawa,yana kwance zain ya shigo yana masa tsiya, ahankali ya dago kansa yana kallansa yana murmushi yace uhmm ayyi kai har yanzu gwauro ne,zain yace inama kasani sai an kawota, khalid yace me kace?yace naji dai bakomai ba'a kaina farau ba ,ba akaina karau ba,nan fah suka zauna suna fira, khalid yayi yayi da zain ya bari ya nuna masa hoton senorita ya rufe ido shi akan dole bayaso,abari sai ta dawo ko yaje ya fara ganinta, khalid yace alright then no wahala,
Misalin karfe goma akaje daukar amarya Aisha esha daga gidansu zuwa gidan angonta khalid,tayi kuka sosai, iyayenta sunyi mata huduba sosai mai shiga jiki,ita kuka kawarta safeeya kuka,an rasa wanda zai lallashi wani,haka aka kaita wani katafaren gida da yake cikin gidansu khalid,dama apartment biyu ne ko wane building babba ne sosai ,saidai ko wane gidan da nashi gate,babu mai ganin wani,safeeya da sauran friends dinsu suka tsaya sayen baki, lokacin ango ya shigo da abokanansa biyu da babban abokinsa zain,haka sukata tsula tsiya,akan 100k suka siye bakin amarya sannan kowa ya watse ya tafi gida,ya rage daga khalid sai amaryarsa aisha,sukayi sallah,sukaci kazar amarci,daren ranar khalid ya nunawa aisha cewa nata wasa ne,daren ranar ya nunawa aisha cewa shi namiji ne,ga baki daya saida aisha ta kasa ko dogon motsi,tun tana kuka tana kiran ummah haka ta hakura bakinta ya mutu, banbancinta daya da matacce numfashin da takeyi,sunfi awa uku suna abu daya,haka khalid ya kwanta sai mayarda numfashinsa yake ahankali,har lokacin aisha esha hawaye take zubarwa 🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈
Gunsu senorita da siyama kuwa,kwana biyu ya rage a daura aure,mummy ta kira ta gayamusu saidai bata fadi na senorita ba,sunji takaicin rashin halarta bikin sosai,amma kuma babu yanda suka iya dadinsu ba'ayi wani bidiri ba ko events ba walima ce kawai,siyama tace bakomai idan suka dawo zasu basu surprise dinda yafi nasu,mummy tace nima akwai surprise dinda nakesan na baku,haka suka rabu akan kowa yana surprise dinda zai bawa wani,wasa wasa senorita ta saba da kowa awurin aikin nasu,duk wani operation na manya dr da ita ake shiga saboda itama kanta ba'a barta abaya ba,sun fito wani operation kuma sunyi nasara akai,dadin kan dadi,karo na biyu kenan da take samu nasara akan ko wane operation za'ayi,tana zaune a office dinta tana scrolling through cikin system dinta,wani G-mail ya shigo,tana dubawa sai taga case din patient ne daga Nigeria,tana cikin duba case din akayi knocking cikin yar karamar muryarta tace come in,aka turo kofar office din,wata baturiyar likita ce ta shigo,ta mika mata hannu suka gaisa sannan ta zauna,tace tayi receiving Gmail yanzu?laurat tace eh,tace alright case ne aka turo daga Nigeria,ga baki daya likitocin sunada operation agabansu shiyasa akace aturo mata, cikin harshen turanci take mata bayanin, Laurat tace yanzu Nigeria zataje ko nan UK za'ayi shi?dr din tace ko wanne take so, laurat tace tafisan yinshi anan UK,dr din ta mata godiya sosai suka gaisa sannan ta fice,tana fita senorita tayi murmushi tace uhmm bari na duba case din da kyau,am so tired wallahi,ma sha Allahu DR LAURAT SHEHU SENORITA AMOUR kenan,ga baki daya ta cenza,komai nata na classic doctors ne,tun lokacin ta fara aiki dressing dinta daya ne coat different colors and design,komai designer take sawa🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
Nigeria kuwa wata daya kenan da auren khalid da Aisha, Aisha ga baki daya ta sauya,babu abinda ta sawa gaba da ya wuce kula da khalid dare da rana,biyayya kuwa yanda kukasan rakumin Annabi,itama haka take fita aiki da yake labscientist ce, hospital daya suke aiki da megidanta Khalid, ZAISUS private clinic kenan,komai nasu akan tsari yake,gun zain kuwa shi yanzu yakema cikin damuwa da takura saboda yanzu baisan ta inda zai fara neman amour dinsa ba,zaune yake a office dinsa sai juyi yake akan kujera, khalid ne ya shigo office dinsa yayi jiki yayi kyau sosai,zain yace ango kasha kamshi,haka ya zauna sai fira suke,nan take khalid yace dama nazo ne gayamaka ka shirya zamuje uk , za'a kai yaron mai anguwa,ance akwai wata hadaddiyar Dr wacce ta kware ta wannan bangaren so everything is ready,zain yayi murmushi yace uhmm ba inda zani , khalid yace com on guy dan Allah kasan bazan iya aikin nan ni kadai ba,da kyar ya samu zain ya amince da zaije,haka suka shirya akan tafiyar
Khalid yaje har kauyen ya dauko mai anguwa da iro,ya kwanta a UDUTH na kwana biyu, sannan akayi komai akayi transferring komai zuwa uk, Aisha ga baki daya jintayi bazata iya zama ita kadai ba,da kyar ya samu ya lallasheta ta amince ta zauna,da sassafe suka wuce abuja, sannan suka wuce uk,isarsu UK keda wuya daga hospital aka turo ambulance dinda zata dauki iro dake kwance akan gado daga airport,nan kuma drivern khalid yazo ya daukesu ga baki daya,da mai anguwa, khalid da zain,haka suka karasa hospital din,suna zaune suna jiran ayi admitting dinsa,haka akayi admitting dinsa da komai,amma saidai kash yau Dr laurat bata samu shigowa ba hospital dinba tayi tafiya zuwa Calfonia zata yiwa wani operation,haka suka zauna zaman jiranta, khalid ya sauka agidansu na uk,Zain ma gidan nasu ya sauka dake kallan nasu khalid,koda khalid yaje senorita bata nan,nan fah siyama take gayamasa komai da komai, ba karamin dadi yaji ba, musamman da yanzu ya fahimci cewa itace zata yiwa Ibrahim iro mai anguwa aiki ya fara tafiya,satinsu daya a UK suna jiranta,amma har waya sunayi da khalid saidai bai gayamata abinda ya kawosa ba yadai gayamata missing dinta yayi, tunaninta ga baki daya da matarsa yazo🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
💕💕💕💕💕 MRS 💕 NOOR'S 💕 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Novela JuvenilFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...