Misalin karfe daya khalid ya shigewansa daki ya kwanta sai bacci, misalin karfe biyar na subahin akayi kiran farko,wanda ya tada lauratu daga bacci,ta shiga bandaki ta dauro arwala sannan tayi nafila biyu ta zauna tana lazimi tana cikin lazimin taji fitowar khalid daga daki zai fita masallaci,Nan tayi sallah subahin tayi karatun qur'ani kaman kullun,tare da yin addu'a ta shafa ta mike tsaye komai ta maida shi inda yake,ta gyara gadon tsab sannan ta fito, kitchen ta nufa ta fara hada masu breakfast,arish ne ta fere ta soya da fry egg,ta hada ruwan zafin tea ta saka a flask komai akan dinning table ta jera shi,ko yanzu saida tayiwa baba nashi plate da ruwan tea dinsa,tayi sharar gidan,tayi mopping ko ina tsab ,ta saka turaren wuta sai kamshi ke tashi, misalin karfe bakwai ta gama komai,ta komawanta daki,ta shiga wanka tsab ta shirya cikin arabian dress black,ta zauna jikinta sosai kaman wacce aka auna,ta feshe jikinta da turare,sai kamshi take.....
Gun khalid kuwa karfe 7:30 ya dawo gida,ya shiga dakinsa tsab ya shirya zuwa office cikin coat dinsa baka,yana fitowa yaci karo da laurat ta fito har kasa takai ta masa ina kwana,yana murmushi ya amsa mata sannan suka sauko tare,yace na fita,tace breakfast fah?chak ya tsaya yace har kinyi breakfast? tayi murmushi tace tun dazu kuwa,yace uhmmmm yayi madam, murmushi tayi tace koda yaushe ni cikin cenzaman suna ake,yace you deserve more ne all the time,ta jawo masa kujera ya zauna tayi serving dinsa,itama tayi serving kanta tare sukayi breakfast din,abinda be tabayi ba breakfast agida sai yaje office yake breakfast,yana gamawa ya mike tsaye da issue hannunsa yana goge hannu,mikewa tayi itama tace ina zuwa,ta haura sama cikin hanzari ta fito dauke da arabian perfume hannunta,yana tsaye ya bada bayansa sai gata a gabansa,nan ta hau feshe shi da turare tace oya hold this ta mika masa turaren ya rike ya zuba mata na mazurunsa yana kallanta,kaman wacce zata rungume sa,ta gyara masa tie dinsa daya koma gefe,tace bani ya bata turaren,ta rakoshi har gun motarsa tana masa adawo lafiya,sai smiling yake yana waving dinta,bayan fitarsa ta dawo cikin gida ta dauki breakfast din baba takai masa tare da masa ina kwana,yaji dadi sosai,suka dan taba firar duniya sannan ta komawanta cikin gida,fallo take zaune tana kallan arewa24,inda suke girki adon gari😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊
Misalin karfe goma sha biyu,ta shiga kitchen tayi wanke wanken safe, sannan ta dora girkin rana, shinkafa da miya ce sai cabbage, carrots,cumcumber,da sauran garnishing stuffs dinda tayi a faranti babba,komai ta jera akan dinning hall din,yayi kyau sosai, saboda ko bakomai kulolin na daukar hankalin mutun,ta kara gyara gidan tsab,ta hadeshi da turare sai kamshi yake tashi, misalin karfe biyu ta kaiwa baba nashi abincin rana,shi kam baba hankalin shi kwance yanzu yadaina damuwa da fita sayan abinci,daki ta koma tayi wanka tsab ta shirya cikin wata material gown ready made red,rigan ta zaunu sosai,tayi parking gashin kanta a tsakiyar kai da red ribbon,tayi sallah azzahar sannan ta dawo fallo ta zauna taci gaba da karatun novel dinta kafa daya ta dora akan daya sai smiling take,tana cikin karatun taji ana knocking ta aje littafin ta nufi kofar tana budewa sai naga mahaifiyar khalid cikin atamfa riga da zane da babban mayafinta,sai fashion handbag dinda ke hannunta,daga ganinta kasan matar manya ce, lauratu tana murmushi kaman ta santa har kasa takai ta gaida ta,tare da karban handbag dinta ta bata hanya ta wuce, mahaifiyarsa sai smiling take tana karayiwa gidan kallo saboda sai kamshi ke tashi daga ganin gidan kasan akwai mace mai tsabta acikin sa,fallo ta zauna kan sofa ta dora kafa daya akan daya,laure ta durkusa har kasa ta gaidata tare da mata sannu da zuwa , murmushi tayi tace kina lafiya?tace lafiya lau hajia,ya mutanen gidan?tace duk suna tafiya,tace tau ma sha Allahu,zaune takai kanta a kasa,tunda ta shigo batayi fours da laure ba taki bari saboda kunya, murmushi tayi tace kece LAURAT kenan? lauratu tace eh nice,tace shekarunki nawa laurat?tace sha tara 19years,tace ma sha Allahu Allah ya jikan magabata, lauratu ta amsa da ameeen🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗
Duk shuru sukayi,hajia sai satar kallan lauratu take,shurun ne yasa lauratu ta mike tsaye ta shiga kitchen,ta kawo mata ruwa da lemu,ta zuba mata ta durkusa kasa ta mika mata cikin girma da girmamawa, ta karba tana smiling tana kada kai sama da kasa,bayan yan mintuna taja laure fira,abunku da mai shegen surutu cikin yan mintuna laure ta saki jiki da ita sai fira suke abunsu,kaman wadanda sukayi shekara da sanin juna,suna cikin firar laure tace yanzu ki tashi muje kici abinci,hajiya tace uhmm kin iya girki?laure tace tab muje kici kiji,ta cire mayafinta,suka nufi dinning hall,tayi serving dinta white rice and stew together with coolslow,sai soyayyan naman kazan da tasa mata agefe,hajia tace kefah?laure ta tabe baki tace ba yanzu ba,hajia tace aaah dauko naki spoon kizo muci tare,laure tana smiling ta dauki spoon dinta ta jawo kujera ta zauna,tare sukecin abincin da mahaifiyar khalid,sai smiling take saboda harta fara son lauratu a tare da ita.....

YOU ARE READING
ZAIN ZAYYAN
Teen FictionFollow me i won't mislead you in sha Allah,with your help we will get to know what is about to happen MR ZAIN ZAYYAN, ASMA'U (HUSNA)and so on 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS NOOR'S 💕💕💕💕💕 ZAISUS LIFE WRITTERS...