ZAIN ZAYYAN PART2 PAGE 65&66

992 67 0
                                    

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 MRS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOOR'S 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕********vote for me on Wattpad as:mamanhanna2018💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

Cikin rawar murya tace SENORITA kuma?kana nufin sai christian zata iya zama da da'na? khalid yayi murmushi yace ba christian bace mummy ,musulma ce,hannun mahaifiyata ta tashi, she's very beautiful,sweet and educated ta ko wane fanni, sannan kyakkyawa ce mummy ta bugawa a jarida,bazaki taba da kinsanin zama da ita ba saboda batada matsala wallahi,na tabbatar ita kadai ce zata iya zama da zain,kuma zatayi iya bakin kokarinta wurin ganin yamanta da LAURAT,ga baki daya hajia zaynab jintayi har yarinyar ta kwanta mata arai, tayi murmushi ta maida dubanta kan zain ta shafi gefen fuskarsa, lokacin yayi wani dogon motsi ba tare da ya bude idanuwansa ba, ahankali ta rufeshi da silky bedsheet din black,tace banida wata mafita yanzu khalid sai wannan yarinyar, ina zamu sami iyayenta? khalid yace uhmmmm komai yazo gidan sauki magana kawai zakiyi da mummy shikenan za'ayi komai,kinga sai a hada aurena da nashi kawai ayi,ta gyada kanta sama da kasa tace hakane, thank you so much khalid you are indeed a friend, Allah ya maku albarka,haka ta mike ya rakota har gun motarta wata hadaddiyar land rover ce fara,dama key dinta ne kawai hannunta,ta shiga mota tace sai na kiraka khalid,yace tau mummy Allah ya tsare ,baba ya wangame mata gate din ta fice abunta, khalid yayi zugum yana mayarda numfashinsa ahankali,ya lumshe idanuwansa ya kara budewa sannan yace am so sorry senorita,nasan ba irin wannan mijin ne kike nema ba,am sorry please forgive me 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Hajia zaynab bata taka birki ko ina ba sai gidansu khalid,tana zuwa horn tayi aka wangame mata gate din gidan,ta shiga tayi parking sannan ta fito,tana fitowa ta nufi cikin gidan,masu aikin gidan ne kawai keta faman shara da goge goge, ahankali tabi fallon da kallo mai dauke da komai red nd black,sai lokacin daya daga cikin masu aikin ta dago tace sannu da zuwa,hajia zaynab tace yawwa sannu,ina maman khalid?tace tana ciki ki zauna na kirata,tace okay,ta zauna akan sofa royal cushine kafa daya ta dora akan daya,dayan mai aikin ce ta juyo da gaidata ta amsa mata cikin sakin fuska,sai lokacin wadda taje kiranta ta fito,tace  tana zuwa,hajia zaynab tace alright, cikin dan kankanin lokaci aka cika mata gabanta da drinks da snacks,akayi serving dinta lemun,haka take sipping ahankali,bayan 30minute mahaifiyar khalid take saukowa daga staircase din, ahankali take kallan hajia zaynab,kallo kaman nasani,tana karasowa fallon tace haba,nima dai nace maman zain ce, tayi murmushi ta zauna gefenta,suka gaisa cikin sakin fuska sosai,daga ganin yanda sukeyi sun jima da sanin juna,hajia zaynab ta aje cup din hannunta tace maman khalid ?tace na'am mama  zain lafiya naganki da rana tsakiya? tayi murmushi tace ina kuwa lafiya take yaronki zain yanasan ya kasheni, tayi murmushi tace aaaah yarona bazai kasheki ba meyayi?ta kwashe komai ta gayamata,tace innalillahi wa'innailaihir raju'un,meyasa kikayi haka?tace kedai bari wai gata na masa,maman khalid tayi murmushi tace yaran yanzu baka musu gata awurin wadanda suka nuna suna so,

Amma tunda ga mafita khalid din ya kawo ayyi babu matsala,na tabbatar senorita bazataki zabina ba, saboda yarinya ce mai ladabi da biyayya,ga kunya, gaskiya idan kika sameta babu ke babu shiga kitchen ko shiga damuwa saboda komai zata maki,yanzu haka suna uk tare da babynki siyama final year student ce a medical doctor,amma kinga auren khalid yau saura kwana uku a daura aure,in sha Allahu za'a hadasu ga baki daya a masu auren,kada kisamu damuwa ayyi zain da'nane,hajia zaynab tayi mata godiya sosai, saboda ta taimaki rayuwar yaronta daya tilo aduniya,haka suka zauna sai firarsu suke 🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫🤫

Gun senorita kuwa,yau suka rubuta final paper dinsu,ta karbi certificate dinta,ta fito da first class a medical doctor,da kuma offer ta aiki a babban asibitin uk ta shekara biyu,ba  karamin dadi taji ba ranar,farin ciki gunsu da ita da siyama Kam ba'a cewa komai,haka sukayi celebrating in a very big way,da sauran graduate din,agidansu senorita da siyama aka hada bikin,sunci sunsha,sunyi pictures,kowa yajidadin hakan sosai,fawad harda gift ya bata,taji dadin hakan sosai,amma sunce bazasu fada gida ba surprise zasu bawa mummy da yaya khalid, SENORITA ta samu gift sosai awurin abokanansu da kuma neighbor dinsu, tsohuwar baturiya mrs Kate,wadda suke kira budurwa khalid ita tayi mata cake amatsayin gift dinta,taji dadi sosai,haka suka zauna sai fira suke, misalin karfe goma sha biyu na dare kowa ya watse ya tafi gidansu,suna cikin kewar junansu,ya rage siyama da senorita tsab suka gyara gidan,ya dawo kaman ba'ayi komai acikinsa ba,sukayi wanka suka shirya cikin kayan baccinsu riga da wando red,farin ciki ya hana LAURAT SHEHU SENORITA AMOUR ko dogon motsi bakinta ko rufuwa bayayi,haka suka hau unrapping gift dinda aka kawowa SENORITA,daga masu card sai wrist watch,sai chocolate,sai masu gowns,ta samu gift sosai,gift din FAWAD AHMAD itace kadai ba'a bude ba,gift din tana hannun siyama zata bude wayanta tayi ringing tana dubawa sai taga shine ke kira, cikin zumudi ta mikawa senorita gift din ta fice daga dakin ta dawo fallo dan waya da shi, SENORITA ta bude gift din diary ne aciki,pink da biron sa,diary din ya hadu sosai,harda key ne dashi na budewa,tasa key din ta bude diary,babu abinda aka rubuta aciki,har zata rufe wata yar karamar takarda ta fado daga cikinsa,ta rufe diary ta bude takardar,***I LOVE YOU SO MUCH SENORITA,I WISH YOU SUCCESS HERE AND AFTER YOU WILL FOREVER BE IN MY HEART FROM YOURS ALWAYS FAWAD AHMAD***Abinda yake rubuce kenan a takardar tayi murmushi ta mike tsaye ta shiga bandaki tayi flushing dinta, sannan ta fito ta hada gifts dinta ga baki daya ta saka a durowa,ta nade gashin kanta a tsakiyar kai kaman donut ta kwanta,tana kwantawa text yana shigowa wayanta,tana dubawa taga text daga wurin Yaya k, Khalid kenan, cikin zumudi ta bude text din*****MY BABY SENORITA,I LOVE YOU SO MUCH,KINFI KOWA SANIN FARIN CIKIN KI SHINE NAWA,NA YANKE HUKUNCI AKAN RAYUWARKI BA TARE DA NEMAN SHAWARA KO IZININ KI BA,KIYI HAKURI KI YAFEMAN,FROM YOURS ALWAYS YAYA KHALID***Shine text dinda ya mata, murmushi tayi sannan ta masa reply kaman haka***** HABA SWEET YAYA NASAN BAZAKA TABAMA  ZABINDA BAI DACE DANI BA,AM SURE KO WANE IRIN DECISION NE KAYI MAKING MAI KYAU NE,KUMA WANDA ZAI SANYANI CIKIN FARIN CIKI NE,BAKAMAN LAIFIN KOMAI BA DAN HAKA KA DAINA NEMAN GAFARATA,I LOVE YOU MORE YAYA****

Kwance khalid yake a fallo rike da wayansa,yana jiran reply dinta, wayansa tayi kara alamun text ya shigo wayansa, ahankali ya tashi zaune,ya lumshe idanuwansa sannan ya bude text din ya karanta, murmushi yayi sannan yace Allah sarki LAURAT she's just the best,i love you more my baby,farin ciki gun khalid kam ba'a cewa komai,haka yakejin kaman shine zata aura, saboda yasan zain zai samu farin ciki mai dorewa,yana zaune sai kara yiwa Allah godiya yake ta hanyar yi masa hamdala,gun zain kuwa ya tashi daga baccin ya dawo hayyacinsa, ahankali yake kallan dakin, saboda yasan dai ba dakinsa bane,ya lumshe idanuwansa yana kokarin ya tuna abinda ya faru amma kash komai bai tuna ba face fita daga dakin khalid da yayi da rana,haka ya mike tsaye yana mikewa yaji jiri ya dibesa dole saida ya koma ya kwanta,ya dora hannunsa akansa, idanuwansa alumshe, lokacin khalid ya shigo dakin dauke da faranti hannunsa mai plate din abinci da ruwan gora,bakinsa dauke da sallama lokacin zain ya bude idanuwansa yana kallan khalid ahankali, murmushi khalid ya masa yace oya tashi kaci abinci,ya tashi zaune,dama cen wata mahaukaciyar yunwa yakeji,fried rice and chicken ce haka yaci abinci ya koshi, sannan yasha ruwa, khalid bai nuna masa komai ba,yana gamawa yace zanyi wanka, khalid yace alright mummy ta kira tace tana nemanka, gabansa ne ya buga,yace okay,haka ya fice daga dakin khalid ya shiga dakinsa, dakinsa tsab aka gyara shi kaman ba nashi ba,sai kamshin turare yake,an cenza zanen gado komai dai neat,gefen gadon ya zauna ya dafe kansa yana fadin shit, khalid yasan komai kenan,mtswww am done, Allah yasa ba shiyasa mummy ke nemana ba,haka ya mike ya shiga wanka, yayi wanka, yayi shaving gashin bakinda ya fara fito masa,ya shirya tsab cikin kananun kaya riga ash mai dauke da stars golden,sai wandonsa baki, yayi kyau sosai ko bakomai zain akwai daukar na kuti(wanka kenan)
 
Cikin kunya ya fito,fallo ya sami khalid kwance,yace khalid? ahankali ya dago yana kallansa yace lafiya zain?yace lafiya lau sannan ya zauna gefensa yace am sorry about am recent behaviors i was so confused i don't know what to do,am sorry, forgive me please ,khalid yayi murmushi ya dafa kafadarsa yace do you want me to forgive you?zain yace yes ,yace alright then idan kaje gida wurin mummy duk abinda ta gayamaka kayi accepting koma menene,da kayi then for sure i have forgiven you from the bottom of my heart,zain cikin rashin fahimta yace hope all is well? khalid yace over well, just do as i say,zain yace alright then no problem,ya dauki car key akan center table ya fice abunsa, khalid ya koma ya kwanta ya saukar da nauyayyen numfashinsa yace Allah yasa ya amince,nasan mummy zata fito masa ta hanyar da ya dace,ya Allah please bless this union of two stranger's of yours that are coming together for your sake please ya rahmar rahimin 🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲

💕💕💕💕💕Ga wata sabuwa,dagani MRS NOOR'S NOVELS 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕ya take ne?hakan take ko Kuma yaaa?

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now