ZAIN ZAYYAN PART 1 PAGE 15 & 16

1.5K 78 2
                                    

Ga baki daya daren jiya zain bai samu yayi bacci ba,sai planning and management of yanda zasu samu solution na gyaran garin,tsab yayi planning komai akan cardboard paper,komai ya fito yanda yakesan sa,bayan ya gabatar da sallah subahin, ya kwanta akan sallaya nan bacci ya daukesa,baccinsa yake hankali kwance, khalid yana daki,shima ya gabatar da sallah subahin ya koma ya kwanta baccinsa yake cikin natsuwa da kwanciyar hankali,da misalin karfe goma zain ya tashi yayi wanka,ya shirya cikin kananun kayansa riga da wando,rigarsa fara long slip,wandonsa baki,zaune yake laptop nakan cinyoyinsa sai typing yake, khalid ne ya tashi shima wankan yayi ya shirya tsab shima cikin kananun kaya,rigarsa baka long slip wandonsa baki,sai kamshi yake yayi kyau abunsa,yana fitowa yaji ana knocking cikin harshen turanci yace am coming,ya nufi kofar ya bude,yana budewa yaga ibrahim dan mai anguwa dauke da faranti da kuloli biyu akai,sai dan jug fari kala daya da kulolin, murmushi yayi yace kwan lahiya yallabai? khalid yace aaaah ibrahim kai ne?yace eh wallahi sai watsar hakura yake, khalid ya bashi hanya ya wuce sannan ya mayarda kofar ya rufe ya biyo bayansa,fallo ya shiga ya aje farantin a tsakiyar carfet din,ya zauna gefe suka gaisa da zain, murmushi zain yayi, ya bashi hannu suka gaisa, khalid ya shigo fallon ya zauna suka fara firar garin da ibrahim,sai labarin garin ibrahim yake basu, khalid ne yayi murmushi yace ina laure?jin ya tambi laure ran ibrahim yayi mugun baci, saboda duniya yanda yake kishin laure bama gaskiya bane,karfin hali kawai yayi yace Allah bansani ba,nidai kawai ta kawo abincin gun sarki,shine yace na kawo maku,ni zan wuce, khalid yace tau sai anjima, ibrahim ya mike ya fice daga gidan ransa abace yana nazarin ko meyasa khalid yake tambayar laure?haka yake tafiyansa yana tunanin abubuwa daban daban, khalid yayi murmushi yace da zain ko lafiya yau laure bata zo ba?Zain yace may be tana school,ya zauna ya bude kulolin macroni ce da dafaffen kawai aciki,dayan kular kuma sauce din kwai ne,sai kamshi take tashi,zain yayi serving abincin khalid ya sauko suka soma cin abincin hankali kwance,zain yace ba santi nake ba amma gaskiya na jima banci abinci mai dadi irin wannan ba,kwanan nan biyu, khalid yace nima kaina wallahi,amma kuma kasan wayake girkin? Zain yace aaah, khalid yace laurat ce,zain ya aje spoon din hannunsa ahankali yace gaskiya inasan naga wannan yarinyar, khalid yace aaah haba kaida ko firan mace bakaso,zain yace i can't say but seriously nadamu da nasan ko wacece ita? khalid yace alright if that's the case mu gama cin abincin sannan mu fita koh?zain yace alright then .....

Daren jiya kuwa lauratu na zaune misalin karfe takwas na dare,inna larai da hanne na zaune a tsakiyar gidan,mahaifin su ya dawo malam shehu,yana shigowa ya zauna,inna larai kuwa ko kallansa batayi ba, lauratu ta fito daga kicin ta ganshi zaune a kofar dakinsa,ta isa gunsa har kasa takai ta gaida shi,ya amsa mata cikin sakin fuska ,zata mike yace dawo ki zauna akwai maganar da zamuyi dake, gabanta ne yayi mugun faduwa saboda ta daukar magana ibrahim iro ne dan mai anguwa za'a mata,yace mai anguwa ya kirani dazu majalisar sa yagayaman cewa ya baki wani aiki,hakane?kanta sunkuye a kasa tace hakane abbah,yace ma sha Allahu,zaki iya kuwa laure naga aikin gidan ma yawa yake maki?kaman daga sama sukaji muryar inna larai tace toh bari nagayamaku munafukan Allah ba ubanda zaisa kidaina man aiki,tunda ke makwadaiciya ce kinji kingani zaki iya sai kiyita yi,kai kuma bari tajawo maka abun kunya dan dai bani zata jawowa ba,tashi mu tafi,ta jawo hannun hanne suka shige daki tanata maganganun da basuda gaba bare baya,shuru malam shehu yayi,laure tayi karfin hali tace kayi hakuri abbah,zan iya bakomai bane kuma in sha Allahu zan ci gaba da kare mutuncina da naka,malam shehu yayi ajiyan zuciya mai nauyi sannan yace nagode kwarai laure, Allah yayi maki albarka,ta amsa da ameen, sannan ta mike tsaye ta shige dakinta,malam shehu sai faman girgiza kansa yake dama da hauni 🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗

Laure tana shiga dakin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,kukan take sosai kaman ranta zai fita, misalin karfe uku na dare ta tashi tayi sallah nafila idanuwanta sun rine sunyi jawur kaman wacce tayi fada da barkono,nan bacci yayi awon gaba da ita,da sassafe aka kawomata cefanan bakin,tayi musu girki, macroni da kwai da egg sauce,tayi tsaye tana tunanin yanda za'ayi,haka ko yau ta dauko cikin kulolin da take tariya,farare masu kyau da jug dinsu,haka ta hada komai white in color, sannan tayi komai na gidan kaman yanda ta saba, ta shirya tsab zuwa makaranta,ta makara sosai,dan haka tana fitowa ta wuce gidan mai anguwa takai abincin,nan yasa ibrahim yakai masu abincin ita kuwa ta ficewanta zuwa makaranta,kaman kullun ko yau da mairo suka fito daga makaranta,sai abunda yasata kuka jiya mairo ke tambayar ta, murmushi tayi tace bakomai,mairo tace gayaman mana,laure ta kwashe duk cin mutuncin da inna larai ke mata tagayawa mairo,shuru mairo tayi sannan tace wai sai yaushe zakiyi aure ki huta da wannan bakin cikin?na rantse maki da Allah inna larai kasheki kawai zatayi saboda tafisan hanne dake,idan kika duba hanne ko makaranta bata zuwa,babu boko bare arbiya amma duk abunda takeso inna larai tana mata koda kuwa bashi zata ciyo,ke ke kuma fah?bakida gaba bakida baya,baba ne kawai koshi inna larai ba raga masa takeyi ba,bare ke da aka haifa jiya,kuma kinsan bakomai ya jawa abbah haka ba sai dan baya muzguna maki kaman yanda sukeyi,dan Allah laure kiyiwa kanki karatun ta natsu kizo kiyi aurenki kawai,laure tayi murmushi tace haba mairo kinfi kowa sanin ummah nasan nayi karatu,nazama wata gobe, wannan karatun alkawarin ummah ne kuma zan jure komai dan kawai naga na gama karatun, nidai muje ki rakani masaukin baki zan dauko kuloli anjima zan kai abincin rana dana dare,zaki rakani?mairo tace mai zai hana muje kawai,koda sukaje knocking sukayi, Khalid ne ya fito yana ganin laure yayi wata ajiyar zuciya tare da murmushi yace tun dazu tunanin ki nake,tace toh yaya ya akayi?yace meyasa baki kawo abincin safe da kanki ba?tace na makara ne dazu da safe shiyasa,ya duba agogon hannunsa yace yanzu karfe goma sha biyu kuma ba'a tashi school ba ya akayi naganki?laure ta tabe baki tace aiki zanyi agida ne shiyasa,yace ki wuce mana,tace aaah ka daukoman kulolin zan tafi gida,zan dawo zuwa karfe daya,yace okay then,ya shiga ciki ya fito dauke da faranti da kuloli biyu akai fararen da aka kawo masu abincin safe dasu yace gasu,ta karba ta dora aka, sannan tace yaya khalid bakaga kawalliya dina bace?ya juyo yana kallan mairo data tsareshi da idanuwa, yayi murmushi yace kawalliya dinmu yakike?tace lafiya lau yayanmu,ya aiki?yace alhamdulillahi,yace tau ma sha Allahu,muje na taka muku koh?laure tace aaah zamuje da kanmu yace yau kam bazan yadda ba har gida zan rakaku,haka kuwa akayi,suna tafiya suna firansu, cikin harshen turanci wani abun mairo kan gane wani kuma saidai tayi shuru😍😍😍😍

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now