ZAIN ZAYYAN PART1 PAGE 29&30

1K 68 0
                                    

💔💔FLASH BACK💔💔

KHALID sai gudu yake da motan,ga ramu ga titin ba kyau,amma haka yaketa kwasar gudu kaman zai fira a sama,30minutes ya shigo cikin garin sokoto,bai taka birki ko ina ba sai private hospital sokoto clinic,yana zuwa ya fito ya tattaleta kaman wata baby,ya shiga da ita, nurses din suka taso cikin hanzari tare da jawo gado aka dorata akai,da shi ake jan gadon yana gefe idanuwansa sun rine sunyi jawur,daidai emergency room suka ce ya tsaya,haka ya tsaya badan yaso ba, saboda kosu karan kansu da sun san wanene shi bazasu tsayarda shi ba,yayi hiding identity dinsa ne saboda koya shiga babu wani taimakon da zai iya bata saboda hankalin sa baya jikinsa,haka yake ta up nd down,go nd come back,ya kasa ko zama sai kai da komawa yakeyi,kansa ne yayi mugun sarawa ahankali ya jingina ajikin bango ya daga kansa sama idanuwansa alumshe, wayansa ce tayi ringing afirgice ya saka hannunsa cikin aljihun wandonsa yana dubawa sai yaga Aisha ce ke kira,nan take ya dawo hayyacinsa,ya daga bayan tare da cewa hello baby,dayan bangaren cikin muryar shagwaba take magana,haba khalid meyayi zafi haka? you don't even miss me have been calling your number not reachable, yayi murmushi yace am sorry darling wallahi network din garin ne sai ahankali,tace yakke?ya village?yace alhamdulillahi lafy lau,when are you coming back?yace very soon,tace uhmmm Allah ya dawo daku lafiya,yace ameen,i will call you back let me just fresh up,tace alright baby bye,yace luv u, sannan ya kashe wayan yana kashewa na hango wani doctor cikin zanzaronsa da labcoat dinsa fara,sai stethoscopes rataye awuyansa tafiya yake cikin kwanciyar hankali, cikin hanzari khalid ya isa gunsa yana dr how's she?tell me please, doctor ya dafa kafadarsa yace don't worry khalid she's fine, let's go to my office,ya riko hannunsa suka karasa cikin office dinsa

Ya zauna akan kujerarsa sannan yayiwa khalid da kujerar da ke gabansa, khalid ya zauna,zaiyi magana doctor yace is okay khalid she's fine but she's unconscious, khalid yace subhanallah tare da dafe kansa, doctor yace amma fah khalid she is very lucky,ka kawota on time da gaskiya she can't make it, khalid yace i know doctor,kwana nawa zata dauka ahaka? doctor yayi murmushi yace you are also a professional doctor you know what it means for someone to be unconscious  so relax please,saidai i don't know who is ibrahim? before she went unconscious she was saying this statement over and over again, khalid yace what statement? doctor yace"ibrahim stop don't do this please dan Allah kayi hakuri"khalid yace ibrahim? doctor yace of course that was the name she was calling, khalid yace innalillahi wa'innailaihir raju'un doctor can you tell me exactly what happened to her? doctor yace from my own point of view nor matter who that ibrahim was,she was trying to harm her in other way, ahankali khalid yace could it be he was forcing himself on her? doctor yace uhmmmm anything is possible,only Allah knows what happened and them, khalid yace i want you to conduct a medical checkup on her please doctor, doctor yace no problem khalid it will be done, khalid yace can i see her? doctor yace of course but a minute, telephone dinda ke gefensa ya dora a kunne tare da dialing number,cen sai yace nurse come to my office, sannan ya aje telephone din, ba'a dauki wani dogon lokaci ba sai ga nurse ta shigo cikin fararen kaya riga da wando sai attachment dinda ta zubo har gadon baya alamu sun nuna cewa arniya ce,tace afternoon sir,yace afternoon conduct a medical check-up on the patient that is in private ward 1 nd accompany this gentleman to the room,tace okay sir, khalid ya mike tsaye ya mika masa hannu suka gaisa ya masa godiya sannan suka fice, nurse din tana gaba yana biye da ita abaya....

Ahankali ta tura kofar dakin,cen na hango laure kwance cikin rigar assibitin green mai check box kaman uniform din school,sai oxygen dinda ke makale a hancinta,anyi treating duk wani rauni da yake jikinta,saidai jikinta yayi jawur abunku da farar fata, kwance take sai numfashi take sama - sama, dayan hannunta dauke da drip,cikin hanzari ya isa gunta gefen gadon ya zauna, ahankali yakai hannunsa gefen fuskarta ya shafa,ga baki daya tausayin ta ya kamashi, nurse din ta katse shi da i want to take her blood for sample,ya juyo ahankali yace no problem,ta nufi gefen laurat,akan durowar da ke gefen gadon,ta dauki syringe da cottonwood, cikin wani tray mai dauke da kayan treatment,ta bude spirit takai audugar ta dan dagula kadan, sannan ta rufe bottle din,ta goga ahankali a dayan hannunta da bayada drip,tasa wayan drip ta matse hannun nata,ta saka syringe din saida khalid ya lumshe idanuwansa kaman shi ake yiwa,ta dibi jinin ahankali ta cire tasa mata cotton wood ta manne wurin,saida jinin ya tsaya sannan ta dauki syringe dinda ta dibi jinin ta fice daga dakin💔💔💔💔💔💔💔💔

Khalid kuwa har yanzu hannunsa na gefen fuskarta sai shafarta yake ahankali,gashin kanta ya rufe mata gefen fuskarta,yasa hannu ya maida gashin bayan kunnenta sannan ya zuba mata na mazuru yana kallanta,wani abu yakeji ajikinsa wanda ga baki daya ya kasa gane koma menene?amma jin laurat yake tamkar wani bangare na jikin sa😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

MRS NOOR'S NOVELS 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔

ZAIN ZAYYANWhere stories live. Discover now