Chapter 001

6.2K 212 3
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


✍by Haleematu(meemartjj)

*Godiya ya tabbata ga ubangiji sarki ALLAH daya bani baiwa na 📝,ina rokon Allah daya bani ikon isar da gaskiya,yasa al-umma da dama su amfana da abun da na✍cikin dumbin akhairi,,,Amin.*

*Tunatarwa*
*don Allah a rika ije📖a lokutan sallah,makaranta ko kuma a'kin gida,tnx.*

*Da sunan Allah mai rahama mai jin kai*



*page 001*

Yatsu✋🏻na zuba saman takalmin makarantana daya lalace ina kollon irin kodewa da lalacewar da yayi,na ije👠na koma kan uniform dina ba cerk dinba ba uniforn dinba duk sun lalace sun kode ga tsufa da sukayi,idan ban mantaba tun shigata ss one akai mun su gashi harna shiga ss 3 ban samu canjiba,duk dani bani da burin daya wuce in rika sa sutura na alfarma na gani na fada,amma bansan lokacin da wannan buri nawa zai cikaba,na nisa wasu😥masu zafi suka zubo min bisa kunci,nai saurin sa hannuna na goge gudun kada Amal ta gani wanda ke kwance bisa makeken gadonta dake gefen dan madaidaicin nawa.
Waya take latsawa da alama chart takeyi,kanta na bisa daya daga cikin pillow gadonta,rigace da skirt na atampa a jikinta kanta babu dankwali wannan ya bada daman ganin kananan kitson shikun dake kanta,hankalinta yai nisa a chart din da takeyi bata ankaraba sai ganin kira tayi ya shigo,taso tai tsaki don an katse mata hiran da take mai dadi,amma ganin sunan dake yawo a screen din yasata saka ihu tare da mikewa zaune tare da dana answer.
cikin farin ciki take fadin"hellow swt dad really miss u"daga can bangaren shima murmushi yake yana fadin"miss u too my daughter ganu bisa hanyar kd daga jos zan iso gida around 3pm,ku shirya tarban dadyn naki keda momyn naki",wani ihu ta saka tana fadin"ok dad sai ka iso",daganan ta mike ta fuce dakin,kai tsaye falon momynmu ta wuce ta sameta zaune bisa daya daga cikin kujerun da suka zagaye falon kusa da momyn ta zauna tana murmushi,itama momyn cikin fara'a tasa yatsunta ta dago fuskan first born din nata tana fadin"babyn dady da anganki cikin annashuwa to dad zai dawo ko?",Amal tai dan dariya tare fadawa cikin momy tace"momy dama na kosa dad ya dawo don ina son inyi wasu siyayya kafun in fara zuwa school",momy ta zaro ido tana fadin"Amal siyayyan da kika yifa duk bai isaba sai kin karo wata"da sauri Amal tace"cab momy a,i wannan ba abun da zaimun kinga ran friday dana shiga school dinne na raina kaina saboda irin yen matan dana gani sai nayi da gaske imba hakaba ba wanda zaice dad dina senetor ne "murmushi momy tayi tana fadin"lallai yer gidan dady sai da gayu"Amal ta maida kanta bisa cinyar momy tana fadin"sosaimam''。
Haka momy da diyarta suka cigaba da hiransu,bayan momy tasaka masu a'iki su shirya girke girke na musamman。
firgit na mike zaune tare da tashi daga baccin dana fara a sanadin muryan Amal dana ji tanawa dad oyoyo wannan ya bani tabbacin dad ya dawo,nan danan tunanin dana saba a kullum ya fado mun ya kamata ko dan yaya this time inyi kokarin yiwa dad maganan sanjin unifoam dina tunda sun tsufa da yawa,kuma in na koma school yanzu ya kamata amatsayin mu na yen ss3kuma na head girl in rika saka sutura masu kyau koda ba yanda ni nake buri a kullum ba gashi zan rika tsayuwa yanzu a gaban assembly,oh ni dai Allah ya tamakeni a canza mun,,,,,,ban karisa tunanin ba naji momy na kwala mun kira.
Meenal!meenal!meenal!a sukwane na sunkuci dankwalina ina daura wa a kaina na fuce tare da nufa site din momy doguwar rigan dana sa yana tadiyeni,dama tsohon na momyne ta bani da bata so tare da wasuma.a falo na sameta dai dai inda zazai kaika up steps din dad,na isa da fadin momy gani,fuskarta daure tamau take fadin ke baki da kunni ko bakijin ana kiranki ko?,murya na har rawa yake nace momy banji bane don Allah kiyi hakuri,ta watso mun harara da idanunta masu matukar kama da nawa tana fadin,come on kwashi kayan nan ki karisa ma dad dinku up dashi,tunda kinfi karfin ki futo ki masa sannu da zuwa,daga nan ta juya tai up abunta,na jawo trolley din tare da daukan karama na hannu ina hawa sama dashi.nai sallama tare da daga cotton na shiga Amal na fadin come in,na shiga na same su gaba daya a falon momy na zaune kusa da kujeran da dad yake zaune shi da Amal,tana zabga shagwaban da ranta ya so suna cikin walwala da farin ciki,nazo wucewa ina fadin daddy sannu da zuwa,sama sama ya amsa kaman yanda ya saba mun a duk sanda nake mai magana ba kaman yanda yake tattara natsuwrsa ba in yana sauraran damuwa da bukatun Amal,na fice falon na sauka kasa da tunanin mafita a rayuwata.
Dad ya kalli mommy da fadin meenal sunyi hutune?mommy ta yamutsa fuska tana fadin eh next week ma zata koma ,tabe baki yayi yana fadin na kan manta ma ina da wasu yeyen in darling daughter din dad tana kusa ko?yakarisa maganan yana kallon Amal yer shalelen dad,mommy ta numfasa da fadin a'i duk wanda yai baya da kanshi zaiga baya,Amal tai saurin kawar da zancan da fadin dad duk ba wannan ba,kasan na kammala registeration na skull kuma jibi nake so in koma don ranan wednesday za'a fara lectures so!i need money to buy some things,mommy tayi murmushi da fadin a'a Amal kya bari dad din naki ya huta ko,yanzu fa ya dawo,ta zumburo baki tana fadin mommy nifa tsoro nake time ya kure mun kinsan ran monday zan tafi,dad ya mika ma mommy suits dinsa tare da mikewa yana fadin kinga babyn daddy bara na huta sai mu futa ki zabo abun da ki keso Amal tasa ihu tana fadin thank you dad,mommy ma mikewa tayi tana yer dariya tare da fadin lallai dad din Amal kana shagwaba first born dayawa,dad ya karisa shiga bedroom da fadin fadi ki kara first born ne.
Bedroom dinmu Amal ta dawo ina jinta tana waya da kawarta seema wanda zasu fara karatu tare a university daya,tambayata take sunan turaran da tace Amal dan ta siyo musu ina jin tana fadin,karki damu a'i saina kwaso kusan guda biyar tunda dad ya dawo a'u baji,daga nan naji suyi sallama,tare da cigaba da shirya kayanta da zata tafi dasu lodi lodi.na nisa daga kwacan da nake ina kara kallon Amal kyakyawan mace mai ji da class,hutu ya zauna a jikinta sosai,wani tunanine ya fado mun nai saurin fadin,sister Amal don Allah ki taimaka mun gun dad in kun futa kice unifoam dina ya dan tsufa a dan siya mun wasu sababbi,banza taimun kaman bataji me nake cewaba sai da tagama kintsa kayanta sannan ta juyo da wani irin kallo na rainin wayau tana fadin a'u banyi kama da yer a'ikeba kuma in kina suma kina tashi ni Amal bazan maganan canjin unifoam dinki ba bcos u too have the mouth to talk for your self,taja dogon tsaki tare da barin dakin,tuni wasu hawaye masu zafi suka wanke mun fuska,lokaci guda kuma na rushe da kuka na rasa dalilin
da yasa yen gidan mu suka tsaneni harda yer uwata wanda da ita ya kamata mu rika zama muna shawara da juna amma kullum kyarata take Abdul kadai ke sona,na nisa tare da rage sautin kukana ina ci gaba da zubda hawaye tare da tunanin rayuwa,har sai da wani baccin wahala ya dauke ni.
Sosai aka kashe ma Amal kudi tayi siyyaiya mai yawa sai murna take ta zama campus girl ,musamman dad yaki komawa Abuja sai yaga tafiyartaa.kwance nake bisa gado futowa ta wanka kenan na shirya na kudundune cikin blanket a dalilin sanyin da ake tsalawa,ido na kura ma Amal wanda keta shiri cin dinkin riga da skirt na atamfa ta zauna tana tsara make up,ta gama ta jawo dankwali ta fan tama dauri,indan ka ganta kace sabuwar amarya ne don kyan da tayi ta mike tana zuba rangwada ta bude wata jaka ta ciro wani turare kwalban kawai zaka kalla kasan yaji tsada ta feshe jikinta dashi nan da nan dakin ya dauki kamshi ta zaro gyale da takalmi wanda suke kala daya da kayan dake jikinta sababbi tasa,na kalleta ina fadin kai sister Amal kinyi kyau sosai,tana dan tabe baki tace tnx,sai dana ga ta dakko wani dan karamin jaka na gucci mai kyau ta makale kai komai da Amal tasa ranan sabo ne,ta kalleni tana fadin kaimun kayana falo nomis zai zo ya kwasan mun,daga haka ta fice daga dakin,na bita da kallo ina tunanin taji dadinta bani da burin daya wuce in rika sa sutura na gani na fada amma ni nasan bani da wannan gatan.
A tankamemen falonshi ta sameshi dake up steps zaune bisa daya daga cikin kujerun dake falon,laptop ne a gabansa gefe guda kuma ga jarida da yake karan tawa,Amal ta zube kusa da dad din tana zuba shagwaban data saba,yai saurin aje jaridan dake hannunsa tare da kallon yer shalelen nasa ta kwaba fuska tana fadin dad na shirya zan wuce,yai murmushi da fadin Amal yen north west universty,sai kano ko?ta gyada kai tana yes dad,fuskarsa na dauke da fara'a kaman yanda take indai Amal na kusa dashi yace me kike so yer dad,tana murmushi ta daga hannu tana alamar irgan kudi tace money,harya daga kafa sai kuma ya fasa ya kalleta da fadin a'i kisan pin numbern ma,da sauri ta daga kai tana murmushi,yace ok jeki cere ko nawane zai miki,da murna ta mike tana fadin thank you dad,ta shige bedroom da murnanta,ta debi kudin da bata san ko nawa bane ita dai dumamu sosu kawai tayi.
ta futo kenan ta samu mommy a falo,kusa da mommy ta tsaya tana fadin mommy ni zan wuce,mommy ta kalleta da fara'a tace to yer dad da mom zaki mana nisa mom,ta zaro ido tana fadin mom sai kace wanda zan bar kasan ,dad fa yaki kaini outside country ne cos zanyi nisa daku kn din ma baza'a barniba ana korafi,dad na murmushi yace to daughter dan mun nuna kulawan mu akanki ya zama korafi,tai yer dariya da fadin no dad karku damu zan rika zuwa muku weekend,ko da kai dad ba kama cika zama ba sai dai inzo ma mom dina ko mommy,ta kalli mommy tana daga gira,itama mommy ita take kallo tace hakane daughter,daga nan suka rankayo waje dan mata rakiya zuwa gurin mota.
tsaye nake ta window ina kara kallon kwalliyar Amal wanda mommy ke rike da hannunta har gaban katuwar jeep din da zai dauketa dad na biye dasu,cikin annashuwa take fadin mom dad zan wuce,mommy ta kama goshin Amal tana karanta mata adduo'i, itakam sai shagwaba take zubawa tare da mita wa wai har yanzu bata girma ba an daina mata abun yen yara,dad sai dariya yake mommy ta gama addu'an tana fadin a'i addu'a ba babba ba yaro ko kinyi aure sai na miki,dad ya matso Amal taja da baya tana fadin dad kaima addu'an zaka mun,duk suka sa dariya,dad na fadin kwantar da hankalinki i just want to ask you da driver zaki tafi,ta kwaba fuska tana fadin yes dad ba kaki canza mun mota ba yanzu ko ina zanje a kn sai dai na dauki drop,karki damu ina son in siya miki babbar motane mai tsada,nasa an kama miki up k mai tsada ki kula da kanki tana dan tsalle tace dats my dad tnx so much,mommy tace Allah ya tsare ki kula kiyi abin da kikaje yi Allah yi albarka,ta shiga mota driver yaja suka tafi.
yau ta kasance ranan alhamis,ranan data kasance saura kwana uku nai resumeing skull,na samu mommy a site dinta ita da kawarta haj mainat suna zaune suna hira,nai sallama tareda zama ina gaida bakuwar mommy wanda take amsamun cikin fara'a banda mommy data hade fuska tun sanda na shigo falon,na daure duk da rawan bakin da nakeyi ina fadin mommy don Allah dama ina son kudin.....ban karisa ba naji ta kateni da tsawa fadi take,,,,don me zanzo gunta ta bani kudi bani da bakin da zan tambayi dad din mune,nai rau rau da idannun da hawaye suka cika ina fadin,a,a mommy din Allah ki tambayan mun shi zaifu bani ,cikin fushi mommy ta wawuri remote kusa da ita tana neman kwada mun,haj mainat ke bata hakuri,cikin tsawa take fadin,fuce mun daga nan don rainin wayau ni zata maishe yer a'ikenta ki tambayi mahaifinki da bakinki baza ki iya ba kin mai dashi dodonki,maxa bace mun da gani kafun in bata miki rai,da sauri nabar falon ina zubar da hawaye,ina jiyo ta tana ta fada haj maina na bata baki nidai nai daki da hawayen dake zuba a fuska na .Tafe muke bisa titin da yake samaru nida cousins dina samira,ummi da zahra,futowan mu kenan daga baban gidanmu wato a,inihin gidan su dad din mu wanda wanshi baba ibrahim da wasu kanninshi suke zaune a ciki samira da ummi yaran baba ibrahim ne,sai zahra yer kanwan dad ne amma tana zaune da kakanmu haj Hadiza wanda muke cema hajiya sai kuma kishiyarta wanda muke kira mama,muna tafe su samira zasu rakani gidan yar dad ne wanda ke aure a hanwa layout,mommy ta aekeni da kudin zubin da sukeyi,Amal ce ke kaiwa to wannan karon ta makaranta dole yasa ni zan kai,sai dai tana da fada itama shi yasa duk in zani gidan sai na kwaso su zahra don su rakani,Napep muka samu muka dauki drop,ummi dake tsakiyar mu nida zahra tai dan tsaki tana fadin Allah yasa dai gatemen din gidan suna kusa na tsani knowking dinnan,samira dake gaba ta juyo tana fadin,aekam in ba hakaba musha knowking,zahra tace ni dogs din gidanma nafu ji,da sauri cikin tsoro nace dama suna da dogs ne,samira tace manya manya irin na police,na kuma rudewa,ummi na dariya tace ,kai meenal a daure suke da chain fa,samira ta zaro ido da fadin,kinsan meye Allah yasa yaya A/majeed na nan,da sauri zahra tace Amin Allah yasa mu ganshi,ummi tai dariya da fadin,to ae baya nan tunda ba weekend bane,zahra tai saurin fadin,oh nama tuna Hajiya tace baya kasan kinsan ana shirye shiryen bashi commishner,samira ta bata rai da fadin kash ban soba,ummi tace,ae dama ni ban sa rai ba,ta kalli zahra da fadin kinsan,ina son inga bikin waliman da za,a mishi,samira tai saurin fadin,ae kam kinsan akwai shagali momy tace aunty mariya last zuwa dubai din da tayi duk na preparation din waliman ne,zahra tace,hmm suna son dan nan nasu,ummi tai karaf din fadin,ae shi din kalan a soshine guy din yayi,suka sa dariya suna maida hiranshi dana kirkinshi,har muka isa nidai shiru nayi don ban ma sanshi ba da yike ni ba mai shiga cikin family bane sosai.

so ko wahala?
*2018*

✍🏻meemartjj

thanks

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now