🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to baby fauzy,,,my Afnah*
*wattpad@Maamee Ja'afar*
*page 18~19*
――――Yau ta kasance ranan saturday, misalin karfe tara na safe nida Amal a dakinmu, ina bisa kan gadona kwance, itama tana kan nata, kwance riginne, ta tayar da kanta da daya daga cikin pillow din dake gadon, waya take yie mai cike da farin ciki,na rasa da wanda take waya,sai dai ka rika jin murya kasa kasa ana kashe murya,,,,,,,,
mummy ne ta shigo dakin tana sallama tare da samun waje gefen gadon Amal ta zauna ta dan dafa kafadan Amal tana fadin, Amal tashi za muyi wata magana ne kuma is so important, itama Amal mikewa tayi tare da kare wayan da takeyi, sukai sallama ta kashe, tana jawo pillow data tada kanta dashi, ta jingina shi da jikin gado, sannan ta zauna da kyau ta jingina bayanta da pillow, ta kalli mummy tana fadin, mummy meya faru?
mummy ta dan nisa kafun tace, babyn daddy gobe fa za'a miki engagement party, zaro ido Amal tayi tare da bayyana a'inihin voice dinta babba, tana fadin, engagement kuma, ni dawa?mummy tai shiru sannan naji tace, ke da mubarak mana bai fada miki bane?ta zaburo daga jikin pillow tana dukan kirji tare da fadin what, mummy har anyi engaged ban saniba, mummy tace, kwarai tun last week, gobe dad dinki keso a fidda date din bikin ma, don haka....ta katse mummy da fadin, no mummy gaskiya bazai yuyuba, baxan taba yarda ba, yaje can ya nemi wata, kaman zatai kuka take cigaba da fadin, nifa mummy bafa na sonshi, ni inada wanda nake so, wanda indai bashi na aura ba bazan taba iya rayuwa mai kyauba, mummy tai shiru tana binta da kallon mamaki sannan tace, kina da wanda kike so a ina, yaushe kuma, sannan donme kuma kika saurari mubarak har yai miki hidima ki amsa, kinsan yaron nan na sonki sosai fa babyna, ta bata rai tana huci tace, so?mummy *so ko wahala*, yana dai wahalar da kanshi a banxa, shi kuma yaga zai iya, dama nifa don ku nake sauraransa, da kuma dad dina dana ga yana ji dashi, amman ni ina da wanda nake so ba mubash ba, na dade da zaban life partner nana, husband to be na kuma, ta kare maganan tana folding hands dinta waje daya tare da kallon can gefe,,,,,,,
mummy ta sauke wata ajiyar zuciya tana fadin, waye wannan wanda kike so?tayi dan shiru can kaman daga sama naji tace, bro. majeed mana, naji gabana ya fadi, tuni wani zufa ya fara ketomun ta ko ina, ina daga kwance, mummy ta dan zaro ido tana fadin, ke Amal rabani, shima yana sonki ne, tana wani bata fuska tana kallon mummy tace, mum dashi fa kika shigo, kika sameni ina waya, mummy tace, what i mean shine, ya fada miki yana sonki ne, shiru tayi kafun tace, a'a mummy kinsan ya cika jan class ne, amman ina da feeling shima yana sona, mummy tace, ok, to kema karki sake ki fara nuna masa kina sonsa, ba kimar ye mace bane, yanda yaja class dinshi, kema ki kama naki, ni zan taya ki da addu'a yanda komai zai zo miki da sauki, kinji babyn mu, murmushi ta saki tana,fadin, thanks mum, amman yanxu dad yabar maganan engagement dina da mubash, saboda ko partyn bazan yi attending ba, don zan iya yinma mubash din duk rashin mutuncin dana gadama a goben, da sauri mummy ke fadin, bana son kina fadin haka kisan waye dad dinki, ki bari cikin ruwan sanyi zan mishi magana, amman kar kice zaki mishi rashin biyayya a, bazai ji dadi ba, a matsayin shi na dadayn ki mai ji dake,,,,,,,
ta nisa tana kallon mummy tare da fadin, ok mum, amman abar maganan engagement partyn nan,bcos in bro.majeed ya sani, ko yana sona baxai nuna ba, ni kuma gaskiya baxan auri mubash ba, don bro.majeed nake so, mummy tace, karki damu, amman karki ma mubarak wulakanci, ba laifin shi bane, don Allah yasa mishi sonki, wanda ya nuna yana sonka, yafi wanda zai kika, don haka karki wulakan tashi, ki bishi a hankali a rabu lfy, mummy ta mike tana cigaba da fadin, hope kinji ni, tace, to, daganan mummy tayi upstairs din daddy da sauri.