Chapter 29

1.4K 89 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Dedicated to mum and dad*

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 28~29*

――――Sameera ne ta shigo dakin da fadin, zarah kije, yanxu naga ya baffajo, yace, in fada miki majinki na nemanki, taja wani tsaki tana fadin, ke kuma kika sani, ta yaya zan futa, gidan nan, kawai sai aga nayi sashin su kuma, dai dai nan aunty karima ta shigo dakin tana fadin, meke faruwa ne, sameera na mata bayani, tana, yer dariya tace, ni da yanxu nake shirin baki turare kije ki fesheshi, ta dan dukad da kai tana fadin, kai aunty nidai ba ruwana, ta dakko wasu turare masu kyau guda biyu, ta miko ma zarah tana fadin, to tashi kikai musu daya na baffah ne, daya kuma na sagir din, uncle dinku yace akai musu, sameera na dan bata rai tace, lah nama manta, shi ya baffajon nan ya takura ma mutane, wai in amso mishi wajenki, ta dauki gyalen data cire, tana maidawa ta yafa tace, bani ki gani in maza in mika mishi, auntyn tace sai zarah ta mike tabi sameera, ta kai ma sagir nashi turaren, tana wani nokewa, sameera ta jata suka futa, tana dada turo baki,,,,,,,,,

ta tura kofan tana shiga da sallama murya kasa kasa, tare daja ta tsaya a dan corridorn falon, yana daga bedroom yana jiyota amman ya wani tsaya salo, ya kammala shiryawa yana futowa falon rike da wata hula arsh da fari mai kyau da tsada, yasha fararen kaya na yadin shadda masu tsadan gaske, sai uban kamashi yake zubawa, yai dan gyaran murya yana fadin, madam ki samu da daman, karisowa ciki, in kuma ba haka ba ki juya, kanta tsaye ta juya zata futa, yai saurin fadin, ke ina wasa dake ne, ta dan juya mishi baya tana fadin, kai kace in futa, ya dan runtse ido irin na takaicin nan, gashi yana jin haushin kanshi, kwata kwata yanxu baya son bata mata rai, cikin lamana yake fadin, to dawo karki tafi, tana tafiya a hankali, ya rika kare mata kallo, tayi kyau matuka, tare da gode ma Allah daya mallaka mishi ita, matsayin matar aure, itama ta kasan ido take satan kallon ango nata, daya sha kyau, ya kariso har inda take yana daga hannu kaman zai rankwasheta, da sauri, ta rufe ido tana fadin, wayyoo, ya sauke hannunshi yana bin idanun data rufe, da bakin data dan turo da kallo, murmushi sosai yakeyi, tana bude ido kuma, ya koma yana wani hada rai, da fadin, wa kike ma rashin kunya a waya daxu, ta bata rai tana son yin masa tsiwa amman kwarjininsa ya hanata, yabi hannuta dake rike da turare da kallo, da biyu yake fadin, ni nace miki ina son ki fesamun turare, har da wani dakkowa, ta zaro ido tana fadin, ni Allah shi kyauta in bata time di..... bata kai karshen maganan taba, yasa hannu yana matse bakinta da fadin, wakike fada ma haka, mijin naki, ta kwace bakinta tana yin baya baya tace, kai ya sagir, ni kadaina tabani, cewa fa kayi zaku daurin auren, bafa cewa kayi kun dawo ba,, ta karisa maganan tana wani kasa da murya, cike da mamaki yake kallonta, zai magana kenan, su ya baffajo suka shigo shida wasu friends dinsu, ya baffajo na kallonta yake fadin, sagir kana fa tsiya!, wani cikin abokan na fadin, amaryan ce, ya sagir yace, matatace, suka sa dariya suna zama da fadin, lallai SG kace wani abu, ita dai taja gyalenta tana rufe fuskanta, ya baffajo na fadin, ke zara'u daina rufe fuska, keda mijinki, cike da kunya ta mika mishi turaren tana futa daga falon, ya sagir din na fadin, zaki mun bayanin kalamanki in muka hadu, ita dai ta fice, mamaki ma yake bata, kaman ba sagir din data saniba, mai gana mata azaba, ta lura kanshi wani rawa yake, tai wani murmushi,, da fadin, ya sagir da sauranka tukuna, ta wuce ciki abinta.

An fara da daura auran ummee da sameera a nan samaru, sannan na zarah da ya sagir a kwarbai city, inda dangin mahaifanta suke, daga nan kuma aka wuce kd, inda aka dauro na ya baffajo, gaba daya daurin auran ya tara abarkan mutane sosai, bakin ummee da angonta baya rufuwa, sanda suka ga sun zama mr and mrs, hakama sameera da mijinta mai sonta, wanda yayi mata gidanta daban dana kishiyarta a kaduna, wacce keda ye'ye uku, zatai na hudu, zarah kuwa, sai lokacin wani kuka yazo mata, tana ganin kaman watan cin mutuncinta ya tsaya, sai da mamanta tayi mata tatas, sannan ta natsu, ana bata hakuri, haj. na faman lallaba yer tata, aka cigaba da gabatar da shagalin biki.

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now