🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W @H@L@H?~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 63*
――――A haraban gidan mu, nayi packing motan, na futo tare da bude booth, ina ciro roban cake din guda uku, masu a'ikine suka tareni, suna shiga da kayan, falonta na sameta a site dinta, taji dadi sosai, sanda take fadin nayi kokari, nace,,,
mummy roba daya idan an samu me zuwa kd, na umma ne, sai akai mata, tace,,,
ba matsala in Abdul zai tafi gobe, ya tafin mata dashi, dafatan akwai nasu haj. samaru ko ?nace,,,
eh, daga haunwa can zan biya, tace,,,
ok kinyi ma kokari, sanda take kallon hannuna, da fadin,,,
ina lallin, bakiyi bane, na dan nisa lokacin da nake fadin,,,
mummy a'ikin nan ne, be barni ba, amman yau nake son nayi, tai dan shiru kafun tace,,,
ok kije kie dawo mana tanan, akwai wacce zata xo tamun, saita miki, ta kalli kaina tana cigaba da fadin,,,
kinma wanke kanki?shima kada kai nayi, alaman a'a, tace,,,
ok jeki dawo sai kiyi a nan, yawwa, kima tambayeshi, inason zamu futa, akwai kayanki kuma da auntyn ku, ta a'iko muku dashi, cike da annurin fuska nake fadin,,,
Allah sarki aunty jidda, ita bata gajiya kwata kwata, mummy tace,,,
nima haka nace, na Amal ma na nan, saina samu mai zuwa, aje mata dashi, da sauri nake fadin,,,
mummy a'i sister Amal din, zata xo ko?itama ta kalleni da fadin,,,
a'a bana tunanin haka, meya faru?jiki a sanyaye nake fadin,,,
bakomai inason ganinta, na dade rabon da mu hadu fa, ta dan tabe baki, ba tare da tace komai ba, can kuma tace,,,
tashi kije, saboda kie dawo da wuri, ba musu na mike har wajen entrance door ta rakani.
Daga nan haunwa na wuce, a falo su salima, suke zube robobin cake din, guda hudu, Nabila sai faman tsalle take, tayi site dinsu mummyn su, nikam sai dan dube dube nakeyi, inason inga ta inda zai bullo, sister kausar ne ta futo daga site dinsu, ta zaro ido sanda ta zauna kusa da kujeran da nake zaune da fadin,,,
sister kece kuwa, kinga yanda kika canxa, nayi yer dariya sanda take cigaba da fadin,,,
karfa kisa brother na, yace yau kafanki kafanshi, irin wannan fresh, kinyi kyau fa, ko dai, brother na ya kusa zama daddy ne, zaro ido nayi, da dan murmushi a fuskana ina fadin,,,
kai sister kausar, ta dage da gaske tana fadin,,,
Allah kuwa, a fada mana tun yanxu mu fara murna, dai dai nan sister maryam ta futo daga daki, tana tafe tana yatsina, rike da wayanta kirar ipon, tana daddanawa, ta sami waje ta zauna, sister kausar wace ke magana cike da murna take kallon maryam din da fadin,,,
momma don Allah, sister meenal bata canxa ba, cewa nayi kodai brothern mu ya kusa zama daddy ne, mu sani ko?ta karisa maganan muna dan dariya a tare, banda sister maryam din dake dan dariyan yake, tare da daura kafa daya kan daya, tana karkadawa,
dai dai nan aunty mariya ta shigo ita da yaranta, wanda suka kai mata zancen cake din dana kawo, sai lokacin ma, sister kausar ta lura, murna sosai naga aunty mariyan nayi lokacin da take kallon sister maryam da fadin, ta bata waya ta kira inda tai order cake donta sanar musu ta fasa,,,