Chapter 62

1.1K 62 3
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W @H@L@H?~~3*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 62*

――――zaune take a dakin asibitin, bisa wata yer sofa chair dake vip room din, cike da girmamawa kaman koda yaushe yake gaisheta, ta amsa, tare da mishi ya ya kara ji da jiki, ya amsa da,,,

Alhamdulillah mummy, tace,,,

to Allah ya kara lfy, yana fadin,,,

Ameen, yake kallon Abdul dake gaisheshi rike da lab court a hannu, wanda ke sanye cikin wasu tsadaddun english wears, murmushi yaya majeed din yayi yana mika mishi hannu da fadin,,,

babban likita, zo mana ka bani hannu mu gaisa, ba musu ya karisa wajen gadon, suna musabaha, Abdul din ke dada gaishe shi da jiki, shi kuma yana tambayarsa, ya karatu, sun danyi hira, kafun Abdul din yayi musu sallama yana karisowa inda mummyn ke zaune, tare da dan sosa saman kanshi, da key din dake hannunsa, yana fadin,,,

mummy ummm...., kallonsa tayi, kafun ta bude jaka, ta zaro atm card, tana mika mishi da fadin,,,

saura ka kwashe mun kudin duka, cikin dan jin dadi yake yer dariya da fadin,,,

ah, haba mummy, iya wanda nake bukata kawai zan cire, nagode Allah saka da alkhairie, daga haka ya fice, yana wucewa inda zai dauki lectures, shima yana mai farin cikin sauyawan mahaifiyar tasu,,,

mummy ta nisa lokacin da take maida hankali sosai akan maganan da za tayi, tana fadin,,,

A/majeed dama inason mu tattauna wani magana, kan case dinka kaida meenal, shiru yayi, yana tunanin ya akayi meenal ta fada ma mummy wani abu, bayan shi ya fada mata, abun ya wuce a gurinshi, shima hankali ya maida kan maganan yana fadin,,,

mummy a'i na fada mata komai ya wuce, mun riga mun dai daita kanmu, kuma nie komai ya wuce a guna, mummyn tai dan murmushi tana fadin,,,

duk da haka, ya kamata muyi maganan, saboda ta fada mun komai dake faruwa, na lura kuma shaidan na muku wasa da lamarin, gudun kada wani rigiman ta kara bullowa, inason in kashe maganan ne gaba daya, akawo ma lamarin karshe, tayi dan shiru kafun ta cigaba da fadin,,,

A/majeed kai sanin kanka ne, lokacin da meenal ke karama, irin rayuwan da takeyi, bata da hayaniya, tana kuma da zurfin ciki, inason ka gane meenal kwata kwata bata da laifi a lamarin nan, inda mai laifi nine,,,

shiru yayi shima da tunanin, tabbas yana tune da irin nuna banbancin da ake tsakaninta Amal, har kishi yake taya meenal din, ya rika ma mummy korafi kan hakan, amman kuma bai fahimci me mummy ke nufi da laifin ta ba....

kafun ya karisa tunaninsa yaji tana fada mishi, labarin tun daga wajen event din daddy, har yanda ta rika shiga tsakanin nie din dashi, da yanda ta katse yinmun duk wani hidima, har zuwa lokacin da kawa taso takaini ta baro, duk akan son da nie din nake mishi, shine wannan rana da muka hadu dashi, ta fada masa duk yanda akayi, tana karawa da fadin,,,

A/majeed don Allah inaso kayi hakuri, kabar komai ya wuce kaman yanda kace, inaso ku dasa sabuwar rayuwa kaida matarka, idan tayi wani kuskuren kuma zaka iya fada mun, nie zan mata fada ta gyara, mamaki yake sosai, tare da tsantsan nadama da tausayinah, dama duk akan shi wannan abin ya faru, yana jin haushin yanda ya rika zargina, kai zato xunubi, shikam saima yayi istigfari, lokacin da yake cema mummyn,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Où les histoires vivent. Découvrez maintenant