Chapter 45

1.8K 87 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

  *Don Allah a rika ije karatu musamman lokutan sallah*

*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*

*page 44~45*

――――Tun sanda ta sauka a motan, ya rasa natsuwrsa, ya kuma rasa abin dake damunsa, haunwa kawai ya iya zuwa ya dawo, sanda ya d'auko ni daga makaranta, driving yake sai a hankali, na kalleshi ina tambayarsa,

  yaya majeed baka da lfy,

   eh kaina ke ciwo, shine amsan daya bani kawai, yana cigaba da driving, ina fadin,

  ehyah, Allah kara lfy, yace,

  Ameen, har gida ya saukeni, ko motan, bai futo ba, ya juya masallaci, don lokacin ana kiran sallah magrib, nie kuma na wuce cikin gida.

 
――wanka nayo bayan sallah isha'i, ina shiryawa, haka kawai yau nake jin yin mishi gayu, inason in fara janyo hankalin mijina gareni, saboda yawan fad'akar damu da akeyi a makarantan islamiya game da aure, na daure ina cire duk wani tsoro da  kunya, inason tabbatar mashi da koni waye, wani zuciyar na raya mun yanda zan cire son wata a zuciyarsa, ina koya mishi nawa,,,,,

   duk wannan tunanin ina yin sune yayin da nake shiryawa cikin wani wando na blue jeans, ya kamani dai dai jikina, duk na lefe ne da aka zuba, barayinsu daban na english wears, na d'auko wata riga light pink, rigan tayi kyau sosai, sai dai bata da hannu kwata kwata, amman daga sama tad'an tsuke, dai dai cibiya kuma sai ta bude, ta d'an sauka, gefen dama tafi na hagu tsawo, rigan tayi kyau amman rashin hannuta ne ya dameni, nadai daure ina sakawa, na zage zip d'in rigan a hankali, wanda keta gefen daman rigan, ina bin kaina da kallo a cikin mirror, kayan sun mum kyau, tare da futo mun da shape sosai, na zuba ma chest din rigan ido, inda aka rubutun baby da wani kyalli, kirjin kaman sayi magana, na rika jin nauyin futa a haka, jawo wani karamin pink veil dina nayi, tare da yafawa, saman gashin da yaji gyara nayi packing dinsa ta gefe, na d'auko trolley d'in turarukan da aunty jidda ta bani, ina feshe jikina, tare da jawo wani wet lips, sai kyalli take, an rubuta sexy, ido na zaro ina mamakin irin wadannan kayayyakin, kafuna na bude ina sawa, sai kanshin coffee yake, yai mun kyai sosai, ban cika wani kwalliya ba a fuskana, na tattara kayan ina kimtsa dakin, ina maida ko wani kaya muhallinsa, na gama ina jawo wani yer pink design silipers, mai dan tudu ina sawa, tare da futa zuwa kitchen inda na shiga shirya dinning d'in.

    ta bayana naji tahowan mutum, ina wajen fridge na bude, ina ciro wani bowl dana yanka fruit salad a ciki, runtse ido nayi tare da kasa juyowa, ya kariso a hankali yana jan kujeran ya zauna, yayin da numfashinsa ke neman d'aukewa, na rufe fridge din a hankali ina juyowa, cike da wani basarwa, bisa dinning d'in, na ije ina fadin,,,,,,

   yaya majeed sannu da zuwa, kai kawai ya kad'a mun yana wani bina da kallon kasa kasa, a gefensa nake tsaye ina jera masa abincin, shiko zuwa wannan lokacin komai ya tsaya mai, daurewa kawai yakeyi, yana faman kauda fuska, wani zuciyar na raya masa,,,,

    wayyoo ashe haka meenal dinshi keda body, irin jikin da yake so ne, komai nata d'an dai dai, yai kokarin daidaita natsuwarsa, tare da yin bismillah ya fara cin abincin,,,,

  niko duk na tsargi kaina, abunka daba a saba ba, na juya zanbar wajen, dai dai lokacin da zuciyarsa ke raya masa,,,,

  a'i ba komai ka gani ba, nayi taku biyu zuwa uku, kawai saiji nayi ana jan gyalen ta bayana, kafun in farga gyalen yabar jikina, nayi wani tsam ina zaro ido tare da juyowa, dai dai sanda ya juyawa, yana ije veil din, saman dayan kujeran dake kusa da wanda yake zaune, zai juyo site dina, nayi saurin juya mai baya, kallo sosai yake bina dashi, tare da tsare bayana daya bayyana a waje, komai na dada rikice mishi,,,,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Où les histoires vivent. Découvrez maintenant