Chapter 11

1.6K 102 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Big sister wannan page din naki ne, aunty jameelatjj(meemeen daughter Afanah)*



vote me on wattpad
*Maamee Ja'afar*

*page 10~11*

――――Ya rage saura two weeks bikin su uncle idris, har lokacin bani da tabbas din za'a barni inje, mummy ta hada gagaru min gudun muwanta aka kai, lokacin kuma yayi dai dai da sanda na fara attending lectures a binki da sabon shiga sai murna nake sosai, tun 8am in na tafi sai 6pm, ranan farko najie jiki daker na dawo gida na samu mummy bata nan sunje kai lefen uncle kabir, kasancewa last week aka kai na uncles idris.

yau satin daya da fara karatu, mun futo lectures 12pm za muyi salla mu koma na 2to 4pm,zaune nake a garden side ina jiran wata course mate dina muhibba, muje muyi sallah, na dan jima a gun sai gata sauri sauri, tace ki taso muje gidan su auntyn kawarmu muyi sallah tace tana can, banso xuwa ba amma dana jie tace ba nisa, dole sai na bita, ba muyi wani tafiya ba, muka riski gidan babba mai kyau dashi,,,,,,,

A falon gidan muka samesu su uku suna kallon tv da yake manne jikin bango,
kwance take bisa doguwar cushion ta daura kanta bisa trust pillow din cushion din, haka ma kafanta na kan pillow din, tana da dan tsawo, sanye take cikin wani shegen lace wanda kyaunsa ya bayyanar da asalin tsadarsa, maroon color an mishi ado da golden, dinki dai dai jinkinta irin na manyan babys dinnan, dan kwalinta ya dan zame wannan yasa naga gashin kanta mai baki da dan tsawo, tayi packing dinsa, kalarta ba baka bace kuma ba fara ba amma yanayin foundation din data sa yai mata kyau, tana da kyau dai dai misali, taimun kyau sosai musamman ma da nake da son gayu, ina son inga mace tayi kwaliya irin top class din nan, na rika binta da dan kallo har aka nuna mun dakin da zanje in salla, naje nayi na futo na same su nan harda hibba wanda ta rigani idarwa ta futo suna hiransu.

Na kalli hibba ina fadin, nie zan koma class muhibba, ta kalle ni tana fadin, ki bari mu futa tare muma yanxu zamu tashi, wata cikinsu tace, hala course mate dinki ne?hibba tace, yes department dinmu daya, wanda na taras kwance bisa kujera ta mike zaune tana fadin, menene sunanta?, hibba tace, meenal s gidado sabuwar student ne, tace, haba shi yasa take wani abu kaman ba campus girl ba, ta zuro da kafafunta kasa tana cigaba da fadin, kin ganni department dinmu daya amma ina 300level ne, in kina irin haka a fadin school dinnan za'a raina ki, wata cikin su kuma tace, gata little pretty kuma lilah, jalila wanda aka kira da lilah, naji tace, yea and she don't deserve dis attitude, ta kalleni tana gyara dankwalin lace din tace, zakie yi kawa dani zan canxa ki for sure, nai murmushi ina nazarin kalamata, a fuska tayi mun but a kalamanta sam bata munba, nace, a'i bazan canxa ba cos haka nature dina yake, naji sunsa dariya ta shiga fadin, ke da kika ganni nan ba karamin kwarewa nayi ba gurin canxa yariya, in nai niyya ko daga village kike sai na canxa kie, hibba ta kalleni tana fadin, kinga wannan ita ake kira da Lilah wonder girl, kowa kika tambaya a campus dinnan ya san da zamanta,,,,,,

tayi dariya da fadin, ke rufamun asiri kince kowa ya sanni banda aljanufa, suka sa dariya, na mike ina fadin, hibba zan wuce kar a fara lectures, jalila ta mike da fadin mene na sauri sister a'i daga yau mun zama friends tare zamu rika shiga school, ko baxa kie friend din dani ba?, nai murmushi nace, Accepted, duk naga sun mike kowa ya dauki jaka, ashe matan gidan ma bata nan sai yer a'kinta, muka futa jalila na barin sakon, in auntyn ta dawo kice na tafi.

Wannan ne sanadiyar zaman jalila kawata indai bamu da lectures sometimes zata zo muyi ta hira ita da wasu kawayen nata don yanda na lura ita mai jama 'a ne, sa'anan tayi ta kashe mana kudi.

SO KO W@H@L@L@H ?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora