🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*dedicated to yhu,,,jamila umar《janaf》marubuciyar 《ma'ikancin kamfani》*
*page 007*
――――Sallama aka yimun na amsa tare da juyowa, wani dan matashin saurayi na gani cikin wata mota kirar pigeot, ya tsaya yana fadin
"meenal manyan mata kin buya abinki kwana biyu'' cike da mamakin inda ya sanni nace "sunnu lfy", yai murmushi yana fadin,,"ina zuwa ne, in baki lift", na daure fuska tare da fadin "no tnx" yai dariya da fadin, "haba meenal irin daure fuska haka nifa neighbor din kune gidan eng.Aliyu" sai lokacin na gane shi jameel ne yaron Haj. Binta, nace "sorry pls bangane kabane" yace hmm kene kin boye dole ki manta kowa, nai murmushi ina fadi, ba haka bane school ya boyeni dat's why, yace, ohk amman yanxu zaki shigo in baki lift din koh?, zanyi magana ya bude motan yana fadin "pls bazan saida keba",ba yanda na iya dole na shiga yana tambayata ina zani nace masa, samaru, haka ya dunga mun hiran school har samaru ya kaini kofan family house dinmu na futo nai mashi godiya mukai sallama sannan na shiga ciki.
sashin Haj.mama na soma shiga na gaisheta sannan na futo nai barayin haj.bahba,
muna gaisawa kuwa ta soma zuba mun kan rashin zumunci,wai kar in gado daddyn mu da wannan figigiyar yayar taki, nace, haj. Amal, tace "eh itafa" nai murmushi ina fadin, indai Amal ce tace a gaisheki, tace, wee wee wee ba dai wannan mai kunnin kashin irin na ubanta ba, na gintse fuska ina fadin, haj. daddy nanefa, tace saura dado,,,dadai da sanda zarah ta shigo dakin ta daga tsalle tare da rungumeni cikin farin ciki take fadin, ke nawan yau muke niyyar zuwa gidan ku sai ga ki, nai murmushi da fadin, uhmm kindai fada ne, nida nai missing dinku a'i gani nazo, tace, lah meenal da gaske nake tunda yanxu munyi candy bama zuwa ko ina,,,kinsan har gida mummyn ku ta a'iko driver da kayan semport dinkin, cikin mamaki nake fadin da gaske, tace, ehmana,,muma munsha namu semport din,, ta sassauta murya tana cigaba da fadin, ke har party muka sha a demo,,haj. ta zaro ido tana fadin, eyye wato sai da kuka yi partyn da aka hana kuko, zarah tai saurin fadin, kai haj. ki rufa mun asiri ina fa bata labarin muce zamu yine aka hana mu,,,,
tace, oho nasha a'i kunyinne yen ba'a isaba masu kunnin kashi, hannuna zarah taja na mike tana fadin, umm zo muje side din su sameera mubar ma wannan tsohuwan dakinta, haj.ta buga tsaki tana fadin, kyaji dashi party dai an hana sai inga ta tsiya, nidai muka futa ina yer dariya.
Sai dana shiga na gaida sauran muta nan gidan sannan muka wuce side din su sameera, sosai mukai farin ciki da ganin juna muka zube nan dakin su muna kwasan hira,,,
ummee ne tace, pls meenal ki cire hijjab dinnan sai kace kinxo bakon waje, sameera na fadin, haka take, ina ko cirewa suka tugemun dankwalina, zarah na fadin, na fada muku, sameera taja gashina tana fadin meenal don Allah wannan duk nakine, nace, karawa nayi, zarah tace,wai Amal muka gani birthday din Nabilan aunty mariya shine suka ga gashinta suka rude nace naki yafi nata sunki yadda, na bisu da ido kowa ya saki baki nace, anyi ma Nabila birthday ne, sameera tace, kinsan su da hada shagali, na dan tabe baki, ummee na fadin, meenal wai me yasa baki gayu kaman na sis.Amal kin ganta ne ranan birthday dinnan ta hadu sosai kallonta kawai akeyi, sameera tace, in kene a wannan dresing din ya kenan, zarah tace, a'i ita sis.Amal din nan haskenta ke taimakon ta,,,,
da sauri zarah ke fadin kai zarah, tace, eh meenal kiyi hakuri yarki ce amma sis.Amal din nanne bata ma mutane kirki,taga mutum tai kaman bata san shiba, sameera tace,a'i ke meenal kinji dadinki ba ruwanki so simple, zarah tace, gashi kin fita kirki wai ko a gida haka take, nai murmushi da fadin,nature dinta ne kuma duk wanda ya fahimce ta bazai ga laifin taba, ummee tace,a'i nee tana mun dai-dai babanta senator gashi ta iya daukan wanka,a'i da nine kekoh meenal da ance sis.Amal bata komai, sameera tace, kuma Allah baiba mai wuka nama, duk muka sa dariya,,,,
![](https://img.wattpad.com/cover/169954186-288-k358612.jpg)