🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 45~46*
――――Ta sauke wayan cike da murmushin nasara, don tana jin sanda yake ma driver magana, tasan yanxu zata ganshi, musamman da tasan shi mutum ne mai tausayi, ta futo bedroom din cikin sauri, tare da futa zuwa falo, inda wasu zaratan samari suke zaune su biyu, daka gansu kaga yen tasha, dayan kunninsa harda dankunni, cike da walwala take sanar musu, gayinan zai iso, don haka tana son su gabatar da a'ikinsu yanda ya kamata, sun bata kuma tabbatarwan cewa zasu yie, iya bakin kokarinsu, suka mike tana komawa bedroom, yayin da daya daga ciki ya futa can wajen bakin gate.
kaman yanda ta fada masa hakane, can ta bayan arean su, gidan karami ne, yaja yana packing tare da futowa daga motan, cikin sauri yake faman knowking gate d'in, ya bude gate din kaman mutumin azziki, tambaryasa yake shi waye, ba bata lokaci, yake sanar dashi, shi dan uwan wacce take gidan ne,,,,,
shin tana ciki ne, ko bata nan, wannan ne tambayar da yaya majeed ya maida mai, ya bashi amsa da cewa,,,,,
eh, madam ne kawai a cikin gidan, kuma tun jiya data dawo kaman bata da lfy, sannan ban kara ganin ta futo ba, bangaje shi, ya majeed yayi da fadin,,,,,
shet!ya wuce ciki yana tunanin, baiga dalilin dazai sa basma tazo ta zauna ita daya ba a gidan,,,,
shiko wancan, gate din ya maida ya kulle, yana kallon yaya majeed din, da wani murmushin mugunta.
sauri sauri ya murda entrance door din, nan ya bude ba shamaki ya kutsa ciki, yana sawo kafa cikin falon, bai ankaraba kawai saiji yayi cikin sauri ta jikin bango anyo fuskarsa da wani farin handkerchief, shima cikin sauri yakai hannunsa wuyan mutumin, tare da shakesa yana juyawa ya hadashi da jikin bango, sai dai duk da haka yamakara, don ko kafun yasa hannun, ya riga da yakai nashi hannun wajen hancin ya majeed din, inda ya shaka masa wani abu, yana kallonsa da wani murmushi,,,,shiko ya majeed har yanxu hannusa na wuyan mutumin, d'ayan kuma yasa yana janye hannun da aka shaka masa abun, yana kallon mutumin cike da mamaki, tare da tunanin mai ke shirin faruwa dashi ne,,,,
dan kan kani lokaci ne, ya rasa tunaninsa, yana ganin komai dishi dishi, sai dai har lokacin da karfinsa yake tsaye, yaki kuma sakin wuyan mutumin, har sai da dan uwansa yaxo suka babare hannun nasa da ker, dai dai nan ta futo falon tana tafiya rangwada, tare da tafa hannu tana fadin,,,,,
good job, hannun ya majeed din ta makale da nata, sanda take kallonsa cikin ido, shima ita yake kallo amman ya koma kaman wani mutum mutumi, tasa yatsanta tana d'ana masa a fuska, cikin wani murya take fadin,,,,,,
stubborn boy, ta zari key dinsa tare da wayansa, ta kalli samarin tana jefa musu key din da fadin,,,,
su shigo mata da motanshi ciki, sannan su jirata daga waje, daga haka suka futa, ita kuma ta janshi har bedroom, tana mai cike da murnan yin nasara.
bakin gado ta zaunar dashi, gaba d'aya tunaninsa ya juya, bashi da wani karfi, ta cire mai takalmi, tare da d'agowa tana zuba mai ido, ba zata iya tuna tun lokacin da take matukar kwadayin kasancewa dashi ba, a hankali takai hannunta cikin suit dinsa, wani sanyi na ratsata, sanda take raya,,,,,