Chapter 80

1.9K 111 12
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W @H@L@H?~~3*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*

*page 80*

――――Tuni haj. ta wanke baby tas, saiga yarinyan ta kara futowa, cikin tsadaddun kayan sanyi aka shiryata, sai kamshin babys spray take, tako wani barayi ana faman jibgo mana kaya, sanda aka bama mummy yarinyar ta dauka, hankalinta ne ya tashi, saboda tuna kalaman daddy datayi na, lokacin da zaya tafi, wasu kwalla suka kawo idanunta cikin zuciya take raya,,,

  daddy Amal plss ka tashi, finally ka xama grandpa, don A llah ka tashi, Allah ya baka lfy, tayi kokarin maida kwallanta, tare da cigaba da kallon babyn tana murmushi.

Murnan su ya koma ciki, sanda su yaya majeed suka iso da daddy, vip na musamman aka basu kowa da dakinshi, shida drivernsa, wanda yake iya magana da ker, ba laifi nashi da sauki, amman daddy kuwa sai dai  du'ai, kowa na binsa da addu'a,,,

  zuciyarsa azalzala take yaje yaganmu, amman ya tsaya sai da aka kammala komai, yana barin tsoron da suka zuba a wajen, ya nufo ward dinmu, daga shi sai farar shirt din, daya cire suit din a mota, damomma yaci karo a reception din wajan, ta nuna mishi dakin, tana nufa can inda su mummynsu suke, ana tararrabi.

a hankali ya budo kafan, zuba mun ido yayi da mamaki, wai meenal ne da yarinya take breast feeding, lallai rayuwa, duka duka yaushe itama ya dauketa, nurse din da take tsaye gefe nane, tana nuna mun yanda zanyu ta kareshi ban lura daahi ba,,,

itama saida ta dago ta gano wanda sukai artabu ne a dakin haihuwa, dan murmushi tayi kawai ta fuce daga dakin, na dago ido ina zuba mishi, ya kasa magana sannan ya kasa karisowa, banda blushing yana kallon hannuna ba abin da yakeyi,,,

   ya saki wani ajiyar zuciya da hade hannayensa biyu sama, yana kuma gode ma Allah, kafun ya kariso a hankali, gefen mu ya zauna, yana bina da wani kallon so, nima murmushin nake da kallonsa, ta soma dan kuka, da sauri muke maida kallon mu kanta, na zareta, ina maida rigana, tare da gyara showel din da take ciki da nufin mika mai, da sauri yake fadin,,,

   no soyayya nah plss ki barta tasha in bata koshi ba, na mikata da fadin,,,

  karka damu tun daxu ake bata, ya amsheta har hannunsa na rawa da fadin,,,

  bismillah, ya zuba mata idanu na wasu mintoci, kafun ya dago yana kallona da fadin,,,

    she is just like me, can't believe it, dan murmushi nayi da fadin,,,

  of course u are her father, why won't she, ya zuba mata ido da fadin,,,

  duk tunanina dake zatai kama, musamman da mummy ta fada mun baby girl ne, soyayya nah karkiso kiga farin cikin da nayi, har steery na kusan kwace mun, kallonsa nayi ina dan kasa da kaina, ya matso kusa dani yana rungumo kafadana, a tare muka kalli juna da murmushi, zanyi magana yai saurin sa dan yatsanshi bisa lips dina da fadin,,,

  shishsh, shiru nayi, sanda bugun zuciyoyin mu ke kuma daduwa, ya daura bakinshi a hankali bisa lips dina, na kasa yake wani sucking kafun ya hada duka da wani romantic kiss, ya dago kai da wani irin numfashi dake sauka wa junan mu, cikin idona yake bina da kallo da fadin,,,

  baxan iya fasalta miki irin farin cikin da nake ba a wannan ranan, komai nayi baxaki fahimta ba, amman ina son kisan nie A/majeed nayi farin ciki da kasancewa mahaifi ga yeyenki, da fatan kema zaki farin cikin kasancewa uwa ga yeyena, ina sonku, kuma in sha Allah zan rike ku da amana, ya cire hannunsa a kafadana sanda yake kuma daga yarinyar yana kuma mannata jikinsa da fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora