🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W @H@L@H?~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 61*
――――Hankalishi ya tashi sosai, sanda aka futo da Amal ya ganta, duk da wajen da suka ijeta mai kyaune, amman sai da jikinta ya nuna alaman wahala, to dole hakan, saboda tunda aka sata wajen take faman kuka, tare da kara tsanar mubash, sannan taki taci komai,,,
don haka wannan ya kara bata wa daddy rai, ta kara rikicewa da kuka sanda take fadin,,,
daddy ina mummy na, nie gida zanje, don Allah daddy karka bani a kn, na tsani zama a nan, pls ka tafi dani, kiris daddy ya rage bai zubar da hawaye ba, don maganan gaskiya yana son diyarsa Amal,,,
lokacin daya shiga lallashinta cewa, karta damu kafanshi kafanta, yana dada zagewa akan case din Amal, har lokacin da shima A lh.basheer ya iso wajen, sai gashi ana neman rikicewa da fada, *to dama abin daba a shuka shi don Allah ba* kowa na nuna cewa nashine da gaskiya,,,
abin siyasa da kudi, saiga Amal an bada belinta, amman kuma Alh.basheer ya dage kan baxai saki case dinba, hankalin daddy ya tashi, sai daga karshene aka kirashi daga samanshi, ana tunatar mishi cewa, karya manta takara ya tsaya, to yabi Alh.basheer a hankali, a gama komai cikin sirri, ba yanda ya iya aka zauna ana fitar da maslaha,,,
inda Alh. basheer yace, doctors sun sanar mishi cewa danshi na kan doguwar suma (coma) yana son a bari harsai ya farfado, sannan ayi wacce za'ayi, indai har tilon danshi mubarak Allah ya tashi kafadunsa, to yayi alkwarin kyale case din Amal, amman da sharadi, da mubarak din ya farfado, ya gama auran Amal,,,
zufa ta keto ma daddy, mutuwar auran Amal bashi bane damuwanshi, damuwanshi shine zaman Amal a garin kn gaba daya, daker dai aka dai daita kan zata koma gidan mubarak din da zama, amman ba futa, harya farfado, daddy bashi da yanda zaiyi, dole sukai signing da wannan conclusion,,
sanda Amal taji wannan labarin, kuka ta saka daddyn na rarrashinta, har gidan nata da police biyu da aka hadasu ya rakata, tana faman risgan kuka tare da kara tsanar mubash kaman me a zuciyarta, tunaninta shine sillan shiganta wannan problems din, *_ahhhhhaf, Amal ba mubarak bane, mahaifinki ne silla, don mubarak banda tsantsan so, tsakani da Allah ba abin da yake miki, baxa kuma ki gane ba, saican gaba_*
daddy hankali tashe yaji garin kn yai mishi zafi, yama fasa kwana, da dai yaxo tare da wannan yer rahin mutuncinne, data ki biyoshi, daya kwana, ko banxa yasan ta iya kalaman kwantar da hankali, da baxa su baro Amal na kuka ba, har saita san yanda ta lallasheta tayi shiru,,,
ya numfasa cikin motan, da driver ya dauki hanyar zaria dashi, yana dana sani, tare da tsantsan nadama, na asirin da yayi ma Amal, ina ma ina ma, da bai a'ikata ba, ya barta ta auri wanda take so, kai gaskiya hankalin daddy ya tashi fa, jie yake Amal kamar itace yer daya haifa ita daya, amman yayi alkwari ko mubarak bai tashi ba, saiya san yanda ya cirota daga kangin da take ciki, baxai bari ta wulakanta ba, sai dai ya rasa kujeran shi, koda hakan na nufin baxa a saka mishi kuri'a bane.
――Misalin karfe 4pm ya farfado, jikinshi duk ciwo yake mishi, lokacin da wasu yen uwan suka lura, aka cika da farin ciki, sister kausar ta nufi har office din doctor, inda ta daddako shi, shida nurses din, suka xo suka ga jikin na yaya majeed, tare da mishi abin da zasu mishi, ana cire mishi wani ledan karin jinin daya kare a lokacin, suka futa,,,