🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H? ~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to mum and dad*
*Ina mika sakon jijina zuwa ga social writers, hakika kuna kokari, fatan da nake muku Allah ya kara basira, zakin hannu da kuma kaifin idanu, yasa a ilimantu fiye da komai, taku meemartjj*
*masoya sakon gaisuwana a gareku*
*don Allah a dauki mai amfani, ayi watsi da wanda ake nuni bashi da amfani, pls a rika ije karatu, lokutan ibada, a'yyuka masu muhimmanci, da kuma makaranta, tnx*
*wattpad@Meemartjj*
Da sunan Allah mai rahma mai jinkai.
*page 35~36*
――――Cike babban masallacin dake samaru yake da jama'a, misalin karfe biyu na rana, anata hidmar daurin aure, major Alkasim da yen uwanshi da manyan mutanan daya tara, suna wajen, haka ma daukacin family malam gidado Abba sun tara jama'arsu iya jama'a, sai ga Alh.basheer tafe da nashi ayarin, sanda ya fada abun da yake tafe dasu, ba karamin tashin hankali su uncle ibrahim suka shigaba, don haka aka dan dakata da daurin auren, shida wani kawunsu da uncle lamido, su kaje daga gefe, suna son suji ta bakin daddy, da har lokacin bai riga ya kariso ba.
*****
Zuciyarta ya shiga mata kuna, tun tana ji kadan kadan, har abun ya tukota, taji gaba daya ta tsaneshi, wanda take kie a da, shi take masifar so a yanxu, tayi hazarin jawo wayanta, tana cire numbern shi data saka a reject list, tare da dialing numbern nashi, kaman kuwa jira yake, ya dauka, kuka take mishi sosai kan yayi hakuri, yaxo suyi aure, ya kasa fahimtar abin da take ciki, yana son shima ya fahimtar da ita, ga sunan, su har sun iso, amma ta katse wayan, tayi barayin daddy da gudun gaskenta, Allah ya taimaka yana shirin futa kenan, shima kukan ta saka mishi, tana fadin, daddy don Allah ni mubash nake so, karku daura mun aure da kowa inba mubash dinaba, shine farin cikina, daddy plss na rokeka, ta rude iya rudewa, duk ta sukurkuce, tana faman rokon daddy ya yafe mata, sai yanxu take dana sanin auran bro.majeed daza tayi, ta tsaneshi bata sonshi, ita mubash dinta take son ta aura, daddy kam yaji dadi kaman yayi me, yana kwantar mata da hankali, kan tayi shiru sai wanda take so zata aura, sanda mummy ta samesu upstairs da wannan labarin, hankalinta fa ya tashi, ta hau Amal da fada, wai zata maida dasu kananan yara, amman da taga irin kukan da haukan da Amal ke musu akan mubash din, sai ya bata tsoro, sannan daddy yana goya mata baya dari bisa dari, ta kama bakinta tai gum dashi, tana bin lamarin da du'ai.sanda su uncle ibrahim suka kirashi, ana case din a gida, don haka ya shiga kora musu bayanin karya cewa, dama can Amal din mubash take so, shine ya takura mata, kan taso da'n yer uwanshi, to gashi kuma yau tana ikrarin in bata auri mubash dinba, zata iya ma rayuwanta koma meye, cikin zafi uncle ibrahim ke fadin, don me bamu saniba sai yau da muka tara manyan mutane, to bari na fada maka, ko kana so, ko baka so, kai da yer'ka saidai kuji kunya, ba dai mu muji kunya ba, aure da A/majeed kaman anyi, daga haka ya kashe wayan, yana kora masu uncle lamido bayani, shiko daddy saka Amal yayi a mota har can samaru, ta gwada musu haukan son da take ma mubash din, har dasu kneeldown tayi, tana rokonsu, kan su daura mata aure da mubash ne, ba bro.majeed ba,,,,,,,,,,
sosai suka tsorata da lamarin nata, uncle lamido da yafi kowa daukan maganan da zafi, ya shiga fadin, sai dai ki mutu, amman aure keda A/majeed kaman anyishi, ta kuma saka kuka, a falon uncle ibrahim da suke zaune ana tattaunawa, tana fadin, don Allah kuyi hakuri, na rantse uncle zan iya rasa rayuwata indai ba mubash na aura ba, kuji tausayina, plss i beg yhu, wannan kalaman nata suka dada basu tsoro, kawunsu na fadin, abar maganan aure tsakanin Amal da A/majeed, a bata wanda take so, in suka cika matsa ma lamarin, to akwai matsala fa, dole aka hakura da batun aure tsakanin Amal da yaya majeed, aka shiga kuma neman mafitan yanda za suyi, da kuma abun da zasu cema major Alkasim da mutanansa, da kuma abokan arxikinsu da suka tara, sanda mahaifiyar su haj. bahba taji maganan, ta saka salati, tana zagawa bayi, kafun ta shigo falon babban d'an nata, tana fadin, dama na sani, duk wanda ya hada abun arxiki da sule sai yaga wulakanci, don nasan za'a rina hakan, ta inda take shiga, ba ta nan take futa ba,,,,,,,,,,,,,,