Chapter 53

1.9K 91 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 53*

――――Bayan tafiyan Amal mummy ta rika saka yanda za tayi ma daddy magana akan abin da yayi, amman bata son bata mishi rai, tana jin haushin wani lokacin yanda take biye ma son zuciyanta ko gaskiya bata iya fada masa, mudim tasan ranshi zai baci, tasan waye mijin nata,,,

duk da haka dai ta daure ta samu daddy upstairs dinshi, tana mishi maganan tare da nuna mishi hakan bai dace ba, maganan da take mishi ko a jikinsa, saima ya shiga fadin,,,

ok, da nace karta fada, shine ta fara fada miki, ya soma waige waige yana nema wayoyinsa, bedroom ya nuna, yana fadin,,

miko mun phone dina ciki, ba musu ta mike tana shiga dakin, tare da futowa da wayan ta mika mai, ya jingina da jikin kujera, yana dialing numbern Amal, tare da sakin wani ajiyar zuciya, mummy ta koma gefenshi tana zama da kallon ikon Allah, daga can bangaren Amal ke fadin,,,

hello daddy, yai saurin fadin,,,

look Amal, ki rufa mun asiri, wato da naje kija bakinki kiyi shiru, shine kika fara fada ma mummyn ki ko, zatai magana yai katseta da cigaba da fadin,,,

bana son wani magana, yanxu ina son ki saurareni, karki sake ki sanar da mubarak wannan maganan, ki kama bakinki ki shiru, inba haka ba, tabbas kika mishi wannan maganan to zai ko.... da sauri mummy ta rufe bakinsa da tafin hannunta, tana zare wayan a kunnishi, kallonta yakw duk wani gumi na keto masa, lokaci daya tausayin daddy din ya biye jikinta, ta dan nisa tana kara wayan a kunni take fadin,,,

hello Amal, kina jinmu ko, tace,,,


eh mummy, mummy na cigaba da fadin,,


kinga dai komai da mukeyi don farin cikin kine, don haka karki sake ki fada ma kowa wannan maganan, karki bari mubarak ya sani, in kuma kika fada masa, to mu babu abin da zamu iyayi game da lamarinki, da sauri take fadin,,,


mummy bazan fada ba a'i, kema don mummyna ne, shi yasa na fada miki, mummy tace,,,


good, Allah miki albarka, daga nan sukai sallama tana bin daddy dake binta da ido da kallo, tare da fadin,,

me yasa za kace mata zai koreta, a'i ita hakan take so, ya numfasa yana fadin,,,


na rude ne game da case din Amal din, daga haka yai kasa da kanshi, yana cigaba da latsa laptop din dake gabanshi, shiru tayi tana son yin masa maganan, ta daure tana fadi,,,

amman nidai kwata kwata, banso hakan ba, idanu ya dago da wani kallon rashin mutunci, saida jikinta yayi wani yam, don ya dade bai mata irin wannan kallon ba, tai kasa da nata kan, yana fadin,,,


sarah!da sauri ta dago tana binsa da kallo, yai wani dan murmushin i don't care yana cigaba da fadin,,,

oh i mean sa'adah karki damu, kaman yanxu zata kara samun wani cikin, fatan mu dai komai ya daidaita tsakanin su, ta dan nisa tana fadin,,,

to Allah yasa, daga haka ta mike ta bar masa falon.


――Tun sanda ya sami kanshi a kasa mai tsarki, ba abun da yakeyi sai ibada zalla, tare da musu addu'an zaman lfy, da daidaituwar al-amura a tsakaninshi da matarsa, yana ma sauran yen uwa da abokan arziki addu'a baki daya, har lokacin daya fara shirye shiryen dawowa.

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now