Chapter 002

2.6K 145 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻
by Haleematu💕meemartjj💕

*Ina muku fatan alkhairie*

*page 002*

――――Tsaye muke kofar gidan bayan mun sauka daga napep din,samira ce ta dau dutse iya karfinta tana kwankwasa katon gate din amma,shiru kakeji sai hauhsin karnuka da ake ji nikam meenal na gama tsorata,don ina matukar tsoron kare,bana kaunar zuwa gidan da suke da kare,wannan ma don ya zame mun dole ne,muna tsaye sai ga salim yaron aunty mariya shi da friends dinshi sun karyo kwana suna tafe suna big boying sai da ma suka hango yen mata aka dada kwambarewa ana wani taku ba shiba ba abokan nashiba,sai da ya matso kusa ya fara washe baki da fadin, a'a samee da ummi da zahra,ya kalleni yana cigaba da fadin ga kuma wata kaman meenal,naga duk kunyi wani girmane,samira da baki ta soma fadin,ah kaji salim kai baka ga katon da kayi bane sai mu da mun girmeka ma,ya zaro ido yana fadin,a ina karku rainani mana,ummi tace,to sannu gaba daya nan manyun yayyin kane,zahra ma ta taso suna mishi nidai banda murmushi ba abun da nakeyi,dai dai lkacin da gateman ya zage gate din muka kutsa ciki salim na fadin,nidai na yarda da meenal big sister na amman banda ku,haka dai muka karisa ciki inda ya kaimu har babban falon mommyn su,nasira yer a,ikinta ce ta kawo mana kayan drinks don mu jika makoshi ,munfi minti biyar kafun aunty mariya ta futo tana tafe da ker hutu ya zauna a jikinta sosai,ta kalle mu da fadin,a'a yen mata sannunku kunsha zama ko?ta karisa zama da fadin wash(hmm aunty mariya kenan akwai ji da kai tun kan tai aure har tayi gata da yeye)ta kalli su ummi da fadin a'a ummi yamutan gidan,suka amsa da suna lfylau,nan muka gaisheta,tana kallo na kaman bata sanni ba na zage jakata na ciro kudi tare da mika mata ina fadin,gashi inji mommy tace kiyi hakuri Abdul din jiyan bai dawo da wuri bane,sai a lokacin tace, oh meenal ashe kece ae ban gane kiba,ba kwason zuwa gidan mutane Amal ce kawai mai zuwan,ya mommyn taku,na mika mata kudin ina fadin lfylau amsan kundin tayi tare da kwala kiram "maryam "ta maimaita yafi so hudu shiru,kafun ta kwaso wata ashar ta watsa mata,sai gata da sauri cikin yanga tana fadin,mommy gani nan,sanye take cikin wani green din doguwar riga wanda kyaunsa ya baiyanar da tsadarsa tai kyau yer slim da ita,tsaki aunty mariya tayi tana mika mata kudin tare da fadin,come on ansa wannan ki kaimun bedroom,ta amsa tare da kallon inda muke cikin yastuna take fadin,sannufa daga haka ta juya tai ciki,aunty mariya ta kalleni tana fadin,yanxu kina inane a school,na dago kaina da fadin,ni ina boarding sch. ss,tace gud tana kallon su ummi tace kufa?samira ta amsa da fadin muma year dinnan zamu zana weac,ta kada kai tare da fadin,to Allah taimaka,maryam ta wuce ku kenan don ita year dinnan zata fara A level dinta nan A B U samaru chemistry department,zahra tace,lallai to Allah ya bada sa'a,tace amin muka mike zamu tafi,itama ta mike tana fadin,no no ku zauna a kawo muku abinci tukkun,ba yanda muka iya tasa aka jero mana abinci,ni dai ban wani ciba don bani da saurin sabo kafun muka mike mukai mata sallama ta dakko 3k ta bamu muyi transpot ,mukai godiya muka futa,salim ne yai mana rakiya har bakin titi yana dada tsokanan su ummi,kafun mukai sallama ya tafi,sosai zahra ta soma masifa fadi take,samira kinga wulakancin da maryam tayi mana sai kace ba yer uwan muba,samira ta amshe da fadin ba kiga ta zama big girl bane an zama campus girl,tsaki zahra tayi tana fadin campus girl din banza da jumping din,yarinyan nanfa ta cika zafin kai,ummi ta kwashe da dariya tana fadin ku ya dama kun manta wulakanci irin nata kenan,samira tace dama ba kirkine da itaba,Allah dai kawota gidan mu nima zata ga rashin m,nai murmushin ina fadin itama yer aunty mariya ne,ummi tace ehmana duk cikinsu itace mara kirkin,zahra tace,a,ikam don ko sister kausar tana da kirki,samira tace sosai ma,nace but amma ina yawan jin suna waya da sister Amal ,da sauri zahra ke fadin ba hali yazo dayaba,kinga meenal yayanki ne sis Amal amma itama bata da kirk...ummi ce tai saurin katseta da fadin, kai zahra yartace fa,samira tace,tom a,i gaskiya ne,ummi tace shikenan ya wuce abar magana,nan dai suka samu napep suka dauki 1k suka barmun 2k din ,inda sukai samaru nai g r a.
Ana gobe zan koma school nai yanke shawaran yi ma dad maganan unifoam dina,don ina tsananin bukatar unifoam din,don haka ina wanka ina tunani,ina shafa mai ma haka,ina saka kaya ina tunanin kalaman da zanyi anfani dashi gun dad,kai harta breakfast ina yine in tunani har sai da mommy taji haushi tai mun fada don tana magana bana jinta,rai bace take fadin ,kin amsa kudin da kikai mun magana gun dad din naku ,kai na kada alamar a'a ina fadin yanzu dai zanje in amsa ,tsaki tayi tana fadin badai kiji dadin rayuwaba indai kika ce haka zaki cigaba ,shiru nayi tare da mikewa na nufi bangaren dad.
Nai sallama ina tura kofan ,jiyowa yayi yana amsa sallaman ,nan ko ya hade fuska kaman bai taba dariya ba daga inda yake zaune yana kallon news ,wayyo Allah zo kuga rudewa gun yersa ta cikinsa kafana ya soma rawa wata zuciyar na raya mun meenal kije mana sai kace ba mahaifinki ba bafa zai doke kiba ,haka dai nai na mazaje na karisa shiga falon ,bisa lallausar carpet din dake tsakiyar falon na zube bakina har rawa yake gurin gaishesa, ya kuma daure fuska yana fadin amsa mun gaisuwan yace lfy?cikin in ina nake fadin ,dady don Allah dama unifoam dina ne ya tsuf....na kasa karisawa ,ban ankaraba naji wani saukan tsawa a kaina yana fadin yi magana mana ?ba shiri naso ma magana cikin rudewa nace dama mommy ce tace ka bani kudi zan sanja uniform dina saboda nawa sun tsufa da yawa ,shiru yayi na yen mintuna kafun yace ,kira mommyn taku ,na mike jiki a sanyaye nai barayin mommy ina fatan sakon yaxo ta hannunta,ashe tsautsayine don mommy har daki ta biyon nasha marin na hada ta da dad,da nace ita tace ya bani gashi duniya ba abun da ta tsana irin bacin ransa,tai mun tatas ta fuce abinta ,ranan kam nai kuka sosai don ba haka naga ana ma Amal ba amma ni narasa dalilin da yasa aka tsaneni na soma tunani ko akwai wani abu da nake musune na rashin kyautatawa kai ko nadai bar yersu bane ko tsintoni suka yi kai ranan ba irin tunin da ban yiba tare da yi kuka sosai nan da nan ko zazabi ya rufeni dama ba wuya jikina ya dau ciwo don haka salla ma da ker nake mikewa nayi har dare tayi na samu na lallaba nai bacci.
Sosai Abdul dan kanina mai sona ya rude da gani yana yin jikina da ker nake mishi magana na mike ina zama ,cikin tausayawa yake fadin meenal kinsha magani kai kawai na kada mishi alamar a'a ,ya mike cikin sauri ya futa yana fadin bara na kawo miki abinci kisha magani ya futa ni kuma na shiga toilet na watsa ruwa na samu karfin jikina.
naci abincin da Abdul ya kawo mun sosai nasha magani cikin tausayi yake fadin ashe mommy ce ta dakeki meenal mai kikai mata ,idona yai rau rau nace waya fada maka, yace baba talle mana don taji ina tambayar mommy magani baki da lfy ta koroni ,nai shiru hawaye masu zafi na sauka bisa fuska ta na fada masa duk yanda akayi ,cikin fushi yake fadin ,wallahi dad in beji tsoron Allah ba sai Allah ya kamashi da hakinmu ,saboda baiyin adalci ki duba fa ki gani banda Allah ya shiryeni duka duka banfi 15years ba amma sai nayi sana'a sannan zan sami kudin da zan biya bukata ta wata lokacin ,banda school fees bai iya yinma na komai ba har gwanda mommy dad ke sata a hanya amma duk gidan nan nafi ganin laifin dad mai yasa ba'a ma Amal haka sai mu nidai sai Allah ya sak....na rufe bakinsa ina fadin ,Abdul dad dinmu ne ko mai zakace bai wuce Allah yasa ya ganeba ,cikin fushi yake fadin har yaushe meenal bafa yanzu aka faraba ,na rantse kona yi kudi bazan taimaka ma dad ba wa....na kuma katseshi ta hanyar sanja topic din ,kudin dana samo gidan aunty mariya na bashi ya siyo mun takalmi lofas da socks ,nai rau rau da ido ina fadin don Allah in bai kaiba ka cika mun,cikin tausayawa yace baki da school shoe ne nace eh harda school bag da unifoam duk naso na canxa saboda nawa sun tsufa kuma yanzu ba da bane zan rika tsuyuwa gaban assembly matsayina na head girl,Abdul ya mike yana fadin kiyi hakuri meenal wata rana sai labari ,ya fuce da kudin a hannunsa.
gab da mangariba ya dawo ina shirin yin alola ya shigo yana fadin meenal ya jikin nace ,naji sauki ,ya zaro school bag daga bayansa ya miko mun sabo gal dashi yana fadin school shoe din yana ciki,cike da murna nace Abdul duka wannan na wane ,yace eh na zaro takalmin black lofas mai kyau ina fadin Abdul a'i wannan yayi 2k din dana baka waya baka kudi haka ka kashe mun,yana smiling yace Allah ya bani sana'an da na keyi,shiyasa nace kema ki samu sana'a saboda dogaro da kai yafi,cikin sanyin murya nace ,Abdul nima ina son sana'an ,tom mommy tunda ta kaini gun koyan dinki taji irin kudin da za'a kashe shikenan ta fasu ,ba mai biya munma inyi koyi sana'an,tsaki yayi yana fadin to Allah shi kyauta yaushe zaki koma school din ,nace da yaune to banjin dadi sai dai gobe ,ya futa yana fadin ok,Allah ya kaimu,nace amin,thank u so much my little bro,na shige toilet don inyi alola.
karfe shida na safe na tashi na fara shirye shirye ,dama kayan provision a storr nake diba harta sabulu da sauransu akwai a gida kawai sai in diba yanda zai isheni ,nai wanka na jawo trolly dina na shirya kayana tare da cire wanda zansa ,sai dana gama shiryawa tsaf sannan Abdul ya taimaka mun na futa da kayana gun mota inda driver zwi saka mun a ciki ,sashin mommy na nufa do amso pocket money gabana na dukan uku uku ,daki na sameta kwance inda na barta dazu da zan mata sallama ,tana gani na ta tamke fuska tana fadin lfy kuma?muryata kasa kasa nace mommy don Allah pocket money zaki...ta kateni da banda shi futa kiban guri ,na juya jiki a sanyaye zan bar dakin sai naji kuma tace zoki bude drower nan ki dauki 3k na isa inda take nuna mun na dauka tare da fadin ,nagode mommy ,ta kalleni daga kwancan da take tace a'i addu'a a kuma kula da ibada ,nace to in sha Allahu ,daga nan na fuce mukai sallama da Abdul na dauki hanyar basawa.
Tsaye nake gaban admin block da kayana bayan sauke ni da driver yayi akai mun searching kayana na samu wasu juniors nawa suka karisa mun dashi nan,zare ido na shiga yi inga ta inda sadiya zata futo.wani teacher namu na gani ya soma mun fadan wai na dawo late ina headgirl,saiga labour master shima nan ya soma zuba nashi harda cewa sai ya sani punishiment,nikam hakuri na basu tare da fadin uzirina na rashin lafiyar danayi.
Hannah Lamido na hango tafe da zugan kawayenta(toh fa,Asst.headgirl kenan.asali yer jahar gombe ne yarinya mai tashe daji da kai ta tsani taga wani ya fita shi yasa basa shiri da meenal ganin ta fita kokari . )tana wani yanga ta isa wajan,suna ma labour teacher bayani akan wani a'iki da yasa susa wasu juniors ,ganina yaasa annuri fuskarta ya canxa ta shiga wani fisge fisge nikam meenal tsaye nayi ina satan kallonta tana cikin wasu yadin unifoam masu kyau da tsada ,da ka kalla kasan sun amsa kudinsu ,suma sauran duk ba laifu duk sun canxa unifoam suyi sababbi harda wa'inda gidansu bai kai karfin namu ba ,a hankali na sauke idona kan nawa unifoam din don ma Allah yasa na saka dogon hijjab dana sha kunya duk da haka sai danai feeling wani iri ,nan suka kare fi'ilinsu suka shiga kiran juniors don gyara makaranta saboda farkon dawo wane school din yayi dati.

Da gudu naji anzo an rungumeni ta baya ana fadin oyoyo sister ,nima na juya muka rungume juna ,cikin sanyin muryata nace tun dazu nake wurga ido inga ta inda zaku futo ina kika shiga ne?,cikin farin ciki sadiya ke fadin muna ta wajan dining muna raba ma juniors abinci ,nai dariya ina fadin a'a woh ke kitchen prepaid tace woh ke headgirl ,da farko ma sai mun baki purnishiment don kece ya kamata ki fara resumeing school ,nai murmushi da fadin Allah bai nufa zan dawo jiyan bane don kinsan banjin dadin dawowa tym di school hours na kalleta nace kai sadiya unifoam din sun muki kyau ,waya dinka miki,tai far da ido tana fadin yusuf ya dunka mun kefa ina naki?na dan yamutsa fuska nace umm niban samu yiba sai dai next term in Allah ya kaimu,tsaki taja cikin takaici kafun tace dama na sani baxa kiyi magana ba ,shi yasa ina gida kaman in dauki wayan umman mu in kiraki in miki tuni ,raina bace nace to sadiya Allah bai nufaba ya zanyi ,tsaki tayi tana jan trolley dina tare dasa wasu juniors suka dau na provision din muna tafe tana zuba mun wai ko don yen bakin ciki dana canxa ,haka dai har muka isa hostel gun metro ta bude mana dakin mu muka saka kayan.

school area muka dawo inda muka zazzaga daga nan na raka sadiya dining suka raba abinci ko ina juniors suka ganni suna mun sannu da zuwa don ba fariya ba ina da farin jini gurin juniors.
mun koma hostle nan muka kuma karo da karyan cherk ko wacce ta dinko sabo kowa da kalan style din nashi wanu abunma harda iya shege ,nidai nawa ido na ciro yen tsoffafin nawa zansa da nai wanka ,sadiya ce ta miko mun unifoam da cherk kala bibbiyu sabbabi komai iri daya da nata ,na zaro ido ina fadin sadiya a'i wannan unifoam din sun miki yawa ina zaki kaisu,murmushi tayi tare da fadin a'i wannan naki ne musamman nasa a dinkasu don ina tunanin baxa ki taba maganan canjin unifoam dinki ba kuma kinsa mun zama manya ,nace kai sadiya nifa ba haka bane ungo kayanki niban kawo miki bane ke zaki bani,sai data balla mun harara sannan tace lallai meenal wato ni bani da kudin da zan miki dinki sai ke,nai saurin gyara maganana da a'a sadiya ba haka nake nufi ba ,tace to indai ba haka bane ki amsa kuma kice masu fadilan yobe kece kika dinko mana don kin sansu munafukaine nidai shiru nayi don bani da bakin godiya don naji dadin kayan nan sosai sai daga baya ne na rika mata godiya har sai data ji haushi na ,kafun na daina.
Ko gaban assembly bana shayin,tsayawa don ina cikin sutura mai kyau da mutunci ,cikin hostle ma ba raini dai dai gwargwado Allah ya rufa mun asiri ,shi yasa a kullum nake gode ma Allah daya bani mafita.


so ko wahalah?
*2018*
comment&share

✍🏻meemartjj💕

thanks💕

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now