Chapter 59

1.6K 59 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*

_korafi,,,wasu suna ganin, yanda nake tsara labarin bai musu ba, to suyi hakuri, ra'ayina ne, in rubuta labarina yanda na tsara kuma nayi ra'ayi, fatana shine, sakon da nake son labarin ya isar, ya isar yanda ya kamata, tnx, yen uwah ina yinku over,_


*page 59*

――――meenal duk sonki ne, yaja wannan, da kuma kishinki da nakeyi, kie daina cewa bana sonki, ke nake so, kece farin cikina, da sonki na rayu, ina sonki, yanda baki taba tunani ba, runtse idanu nayi, sanda nake jin kaman mafarki nakeyi, na daure ina fadin,,,

   yaya majeed bani kake so ba, nasan wanda kake so, kuma ita kaso ka aura, nafi yarda da maganan ka na farko, ta yaya zaka so yarinya mare class irina, me nake dashi daxan ba....... da sauri ya dagoni daga jikinsa, yana bina da wani irin kallo, har lokacin idanunsa basu sauya kala ba, yake fadin,,,

   meenal kinsan yanda sonki ya wahalar dani kuwa, kece budurwa ta farko, data shafi jikina, na kasa bacci ranan, duk wata sha'awah da bansan ina da ita ba, a ranan sai daya tashi, ba komai ya kawo hakan ba, sai son da nake miki, ina sonki, cos kina da class dinki mai tsafta, kina da respect, kina da hakuri, baki da hayaniya, ga nuna damuwa ga dan uwanki, donme baxan so kiba, na rika binshi da kallon yanda yake magana cike da gaskiya, amma sai nace,,,

   toh me yasa wancan lokacin, kace Amal zaka aura, yai dan shiru yana kauda kai gefe, tare da runtse idanu, sannan ya budesu, tafin hannuna ya kamo cikin nashi, yana dagowa tare da damkewa cikin na juna, yana daura dayan hannun nashi a saman namu, yake kallona da fadin,,,

    meenal kin tuna lokacin bikin su sagir, da muka hadu school dinku, nace inmun hadu bikin zan baki wani labari, kin tuna hakan, jiki a sanyaye, na daga kai alaman eh, ya cigaba da fadin,,,

   toh wannan shine labarin daxan baki, sai dai kuma kafun mu hadu, sai kaddara ta hada mu a wannan wajen, wanda shine yai dalilin sanja wannan labari, amma ke nake so, kuma nayi ra'ayi da burin aure, ba ita ba, saboda ban fiye son mace mai rawan kai ba, na numfasa cike da wani irin farin ciki can kasan zuciyana, da raya,,,

   dama yaya majeed ni yake so, naje ina wahalar da kaina a banxa, nima daura dayan hannuna nayi saman namu, cikin sanyin murya nake fadin,,,

   amman yaya majeed ka yarda, zan iya a'ikata laifi irin wannan, kallona kawai naga yana yie, zuwa yanxu ma tausayina yake jie, a tunaninsa na fada ma kaddara, da sihiri irin na A lh. dido, ga rashin haihuwa daya sameni, ya warware hannayen mu, yana cigaba da fadin,,,

  
  meenal mubar wannan maganan, ya kamata mu manta baya mu daura gaba, nie na amince ko yaya kike, zan zauna dake, ke nake so, ba wani abu naki ba, farin cikina daya da wadannan azzaluman, basu cutar mun dake ba, ya riko shoulders dina, yana bina da kallo, ya numfasa yana fadin,,,

  

   meenal, nayi miki alkwarin nie A/majeed zan zauna dake tsakani da Allah, zan tsare miki dukan hakkokin ki, baxan sa damuwa a rayuwan kiba, zanyi kokarin baki dukan farin ciki, yai shiru sanda kirjina ke wani irin beating, ina kuma binshi da kallo, da raya,,,

  
  shin da gaske ne A/majeed dina na sona, shine tsaye yake fada mun wadannan kalam.... ban karisa tunanin ba, ya katseni da jawo right hand dina, nabi hannu sa kallo, har zuwa inda ya sauke tafin hannun bisa kirjinsa, yana dafewa da nashi hannun, lumshe ido mukayi a lokaci daya, ina rigashi bude nawa, sanda nake jin nashi bugun zuciyan, ya bude nashi idanun, yana sauke su akan fuskana, sanda yake fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang