Chapter 74

2.4K 99 24
                                    


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 74*

――――Al-madina hospital muka nufa, dake nan GRA, sanda muka isa duk ya rude ma nurses din wajen, da sauri suke taimaka mun zuwa office din doctor dake duty din dare, naci sa'a macace yer uwata, ba bata lokaci ta soma dubani, lokacin da nurses din ke taimaka mata da dakko wannan dakko wancan, yaya majeed ko sai zarya yake tsakanin one coner to another, tsoro yake wani abu ya faru dani,,,

  kwararriyan likitace, tayi kokari sosai wajen tsaida jinin, lokacin data bani wasu allurai na samun hutu da rage radadi, ta gama dubani, kafun ta fara rubuce rubuce tana a'ikawa da request form din data rubuta wasu test da za amun, sanda aka dawo mata da sakamakon shiru tayi, dama tayi tunanin haka, ta juyo kaina tana kunna nakuran hoto dake gefe, tare da scaning din mahaifata, ta numfasa lokacin da take kallon inda nake kwance idona a rufe, da murmushi take fadin,,,

  Allah sarki, da alama cikin farko ne, Alhamdulillah, an gode Allah, ta kwala ma wata nurse kira, lokacin da take neman relative din patient din, waje ta futa inda yaya majeed ke tsaye tayi mishi iso har cikin office din, ya zuba mun idanu yana zama inda dattijuwan likitan ta nuna mai daya zauna, kafun ya nisa yana kallon doctor da fadin,,,

   doctor hope my wife is safe now, tayi murmushi sanda take fadin,,,

  yes of course, da farko dai ina son sanin kaine mijinta, ya dan daga kai da fadin,,,

  yes maa, tace,,,

  ok, ammm, amma kasan matarka nada ciki, ko a'a, da sauri yake fadin,,,

   what! bansan komai ba akan haka, ta dan jinjinan kanta tana fadin,,,

  hakane, matar ka nada ciki harna tsawon 3months da wasu yen kwanaki, tayaya ba kuje hospital ba, ko batai rashin lfy bane, gashi tayi wasa da lfynta sosai, yai dan shiru da mamaki kafun yace,,,

  am sorry doctor, duk laifi nane, tabbas tayi ciwo, amman lokacin bata kasan, tana saudiya, so sanda ta dawo ba laifi taji sauki, but trust me doctor, bansan matana nada ciki ba, hope dai ba wata matsalan bane ya faru, itama shirun tayi kafun tace,,,

 
    eh toh, yanxun dai ta samu matsalan bleeding, da alama kota fadi, ko kuma she was hit by something, ta kalleshi sanda ya zaro ido tana yer dariya da fadin,,,

  am sorry, ba ina nufin ko kayi ma matarka wani abin bane, abin da nake nufi dai kota bige da wani abin, wanda zai sata cikin raxana haka, ko tashin hankali, saboda ita mai ciki kullum anaso a bata kulawane, musamman cikin idan yana karami, ya dan girgixa kai da tashin hankali yake fadin,,,

  doctor yanxu kina nufin, ta samu matsalan miss carriage kenan, babyna ya futa, ganin yanda yake maganan ne da tashin hankali ya sata saurin fadin,,,

  plss calm down, calm down, ur baby is going to be safe, in sha Allah, ya saki ajiyar  zuciya, jikinsa har rawa yake wajen fadin,,,

   plsss doctor do something, kie taimaka, i really need this child, ta kuma gyara zama da fadin,,,

  karka damu, in sha Allah za muyi kokari, sai dai dole zamuyi admiting dinta, bcos tana bukatar hutu, kuma dole zamu maida mata da jinin data rasa, sannan tana bukatar kulawa na musamman, da sauri yake fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon