🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Maamee Ja'afar*sorry wadannan pages din nayi mistake wajen updating dinsu.
*page 39~40*
――――Sosai ya samu ya sagir suna rigima da doctor, ya baffajo ne ke tausan ya sagir din dayai shiru, amman yana faman masifa, da yike shima doctor masifaffe ne, nan suka rika yi, har lokacin da yaya majeed ya iso asibitin, shi yaba ma likitan hakuri, da sauran ma'aikanta da suke lallashin ogansu, sannan ya hakura ya wuce office rai bace,,,,,,
ido yaya majeed ya zuba ma ya sagir dake faman cika kaman zai fashe, ya dafashi a kafada yana fadin,,,,,
haba sagir meye haka kakeyi, inka kwantar da hankalinka, zata samu lfy, cike da tashin hankali yake fadin,,,,,,,
majeed baza kaga gane bane, doctorn nan ya raina mun,wayau, rana saturday, na kawo zarah bata jin dadi, sunyi gwaje gwajen su, su kace, cikine, nida doctorn nan ya fada mun akwai matsala, ni kuma nace, indai da matsala a cire mata kawai ta huta, ya zauna yana mun wasu maganganun ma rasa amfani, da cewa, a'a in mun hakura za'a iya maganin matsalan, drugs masu tsada yasa muka siya, niba duk wannan ya dameni ba, me yasa zaice mun haka, gashi ba'aje ko ina ba, wai matana, zarah na za'a sama oxygen, da sauri ya majeed ke fadin,,,,,
subhanallah, wani irin magana kakeyi haka sagir, karkafa mata shi doctor yana a'ikinshi ne da ilimin da Allah ya wadatar dasu, don su taimake al-umma, amman ciwo da samun sauki duk suna wajen mahaliccin mu, kayi hakuri sagir Allah zai bata lfy, ya baffajo dake tsaye gefe d'aya yana fadin,,,,,,,
gwara dai ka fada mishi, tun dazu abun da nake ta kokarin ya fahimta, amman ya daura ma likita laifi, baiji bai ganiba, yaya majeed yace,,,,,
plss sagir ka kwantar da hankalinka, be a man mana, kaman zai kuka yake fadin,,,,,,,
majeed tun jiyafa yarinyan nan, batai bacci ba, tun asbah kuma ta rasa inda kanta yake, ina tsoron in rasata, oxygen fa zasu sa mata, cike da tausayawa yaya majeed ya rika bashi hakuri, tare da lallashinsa, ya baffajo na fadin,,,,,,,
wannan maganan ma, a'i baza a bari haj. ta saniba, itama sai ta kwanta ma mutane,,,,,
yaya majeed zai magana, dai dai nan su mummyn su, da aunty Nusaiba sai aunty salma suka shigo hankali tashe, suka kariso aunty mariya na fadin,,,,,,,
sagir ashe haka abu ya faru ba dadin ji, yai dan kasa da kai yana fadin,,,,,
eh aunty, yanxu haka tana ciki vip, sun daurata kan oxygen,,,,,,,,
salati suka saka gaba dayansu, jikinsu yayi sanyi, aunty mariya ta kalli aunty Nusaiba dake tsaye kawai, tana fadin,,,,,,
Nusaiba kuje daga can ku zauna keda salma, nizan ga likitan ne, cikin dakiya take fadin,,,,,,,
a'a aunty ni bari ma, ina tunanin zan koma ne kawai, tunda gaku, tace,,,,,,,
nadai ce ki tsaya, kuje ku zauna bari inga doctor, baxai yuyu kiyi ta kaiwa da dawowa ba, duka duka jiya nan da dare kuka dawo daga tafiya,,,,,,,,
ta kalli aunty salma tana cigaba da fadin,,,,,,,,
salma pls kuje gani nan zuwa, daga haka ta wuce inda aka nuna mata office din doctor,,,,,,,,
![](https://img.wattpad.com/cover/169954186-288-k358612.jpg)