Chapter 20

1.4K 101 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Dedicated to jjs family* 

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 19~20*

――――Rike da hannun Nuwairah na karisa gun, ina gaishe dasu yaya baffajo, duk suka amsa mun banda shi daya zuba mun ido yana kallona, nima ta gefen ido nake kallonsa, hannusa rike wayane yana a'ikin na dannawa, sanye yake cikin yadin shaddan daya saba sawa masu tsadan gaske, light green, rigan mai karamin hannu, ko yaya yasa kaya sai ya mishi kyau, kanshi ba hula, ya cire hulan  mai kyau da tsada, ya ije gefe daya bisa table, ya harde bisa kujran dake na kusa da yaya baffajo,,,,,,,

Na gaji da yanda yake faman bina da kallo, tun daga sama har kasa, na dauke nawa idon ina fadin, sai anjima, da sauri naji yace, ina zaki ba kiranki nayi ba, ya kara da fadin, ina kwaliyar?, nai kaman banji me yace ba, kawai sai na dan zaro ido ina kallon gefe daya, naji uncle idris na fadin, kut, yaran nan angama sangartasu , jubi yanda ake ma yarinya magana, tana wani salo, ya kalleni yana kuma fadin, ko sai ya samiki dukane, zaki bashi amsa, uncle kabir ya kara da fadin, a'i an gama sangarta su, ba ita ba, ba Amal dinba, da sagir na nan shine dai dai ku, a rashin jin nan naku, uncle idris yace, a'i sagir ya huta, ya kalli ya majeed da fadin, kuma ya kamata ku fara daukan matakin sagir, yaya majeed dake murmushi yake fadin, no uncle ita wannan yer yangace, bata magana ba tare datai yanganta ba, ya dan nisa yana cigaba da fadin, yanxu ma da ba kuyi magana ba, sure, nasan zata ban amasa, ya kalkeni yana fadin, ko?,nai dan shiru sannan nace, a'ini yanxu gida zanje inna tafi kuma bazan dawo nan ba, yana danna waya yake fadin, no plss ki dawo, ina so naga taki kwalliyar kaman na kowa, na dan bishi da ido ina nazarin kalaman sa, sometimes he sound so different, a karo na biyu kuma na kara cewa, sai anjima, da sauri ya dago yana fadin, zaki dawo, har zan juya na fasa na tsaya, ina tunanin inda zan samu kaya masu kyau irin na Amal, amman nasan bani dasu,bazan taba samu ba, ni rabon da a bani kaya ma tun salla, sannan yen sabbabin dasu nake shiga class, don haka bani da wasu sabbin kaya masu kyau a yanxu, na dan nisa zanyi magana ya katseni da fadin, come on, don't u see how Amal dressed up?, uncle idris na fadin, yara nan basa ji fa, tuni nai watsi da kalaman uncle idris, ina maimaita na yaya majeed a zuciyata, ina jin wani irin zafin maganan,,,,,,
  dai dai lokacin da Amal ta iso wajen tana zama kusa da maryam dayan site din, ta kalli inda nake tsaye, site din su yaya majeed tana fadin, oh wai dresing zata koma gida tayi, ta ije jakanta, tana cigaba da fadin, hmmm, ba dai wannan meenal dinba, ita kullum tafi son ta ganta haka, like a bush girl, suka sa dariya ita da maryam, Amal na kuma fadin, Allah kuwa, bata son kwalliya kwata kwata,,,,,,,

wani irin juyawa nayi ina kallon Amal da mamaki, kaman ba ita ake siyawa suturan ba, ana mantawa dani, kalaman tane suke,dada amsa mun a kunni, like a bush girl, raina ya baci sosai, ko banxa taci mutunci na, a gaban wanda nake so, na kasa motsi, ji nayi anja hannun Nuwairah da nake rike dashi, Abdul ne cikin wasu bakaken suite masu tsadan gaske, muka hada ido ransa bace yake fadin,  meenal muje kawai driver ya maida ke gida, banda zabi daya wuce nabi dan kanina, muka bar wajan har lokacin ba'a fara program ba.

Gida aka mai dani, na cire viel din jikina ina fadawa kan gadona tare da sakin wani kuka maicin zuciya, ina tuno irin wulakanci, da aka mun yau, na sani a rayuwata ina son gayu ina son tsafta, nakan iya yin wanka sau biyar a rana duk in zanyi alola sai nayi wanka, wata lokacin kuma sau uku, nakan so na ganni cikin kaya masu kyau, na kanyi  kwalliyana dan abin da Allah ya bani, gashin kaina, jikina,skin dina kullum cikin gyarasu nake, duk da basa samun mayuka masu tsada irin na Amal, amman kullum tsaf tsaf zaki ganni, ina matukar son gayu, ita kanta takan burgeni idan naga tayi kwalliya, amman ni zata cewa haka don an maisheni bora a gidan, na kuma sa kuka, burina a rayuwa in burge wanda nake so ita kuma burinta kullum shine ta kuntatamun, kaman ba yer uwanta ba, na mike da hanzari na shiga bathroom ina sakin ma kaina shower kona ji dan sanyi sanyi,,,,,,,,

Na futo wanka sanye da towel na saka wani dogon hijjab dina, saboda sanyin da nake ji, knowking naji daga kofan site dinmu, na futa zuwa bakin kofan, daya daga cikin house maid dinmu, na gani tsaye, ta sanar dani akwai wata bakuwa da aka bari tun dazu zata ganni, tace inzo, cikin mamaki nake fadin, a ina?kuma wacce?tace, tana falon baki, wanda dai tayi masu Amal kwalliya ne, tace sauri take zataje wani gurin biki ne, da mamaki na nufa barayin baki, ina tunanin ko wacece,,,,,,,

Zaune a falo na sameta babban mace yer gayu da ita daka kalleta kasan yarene, sai kuma yaranta enmmata guda biyu, da take tare dasu, ta dubeni tana fadin, kece meenal?, na zauna ina  fadin, eh nice, ta mike muna shiga bedroom dake site din baki, tana jawo akwatin kayan kwalliya take fadin, haba tun dazu nake jiranki, akwai wani gun event dazan je, don auntyn kima ta kara mun kudine yasa na tsaya, ta zauna kusa dani tana fadin mu fara make up?cikin sanyin murya nace, nifa bana son make up,mai yawa, tace, karki damu indai make up dina ne zaiyi miki kyau, ta fara mun, naji tayi ma daya daga cikin yaranta magana da yare, ta kariso ta zame mun wuyan hijab tare da cire band din dana kama gashina, shima gyara na musamman aka fara yi,

ba a wani jima ba,aka kammala komai, za'a miko mata eyelashies, tace a barshi nawa ya wadatar, sosai naga suna shiryani, cikin black  din doguwar riga na material yadin mai kyaun gaske yaji adon stones, sai spakling yake, da farko dana ga rigan baki, nai tunanin bazai mun kyauba, sai kuma dana sa, naga ya dada futowa da haskena sosai, kayan dai dai jikina, daga wajen cibiya rigan ta bude sosai har kasa tana ja da kasa, sai hannu rigan da yake pencil, na material lace din, ta isa dani gaban mirror, ina zama bisa stool din mirror, ido kawai na zuba ma kaina, ina kallon yanda na sanja, na rika kallon red lips din data kara gyarashi da wani red lipstick, so cute dashi, kai gaba daya na futo nai kyau fiye da yanda bana tunani, ta bude wani karamin dan box, ta ciro wasu dankunni  na gold mai kyaun gaske, ta makala mun, tare da miko mun wata yer mannanniyar posse mai kirar ipad golden color, yana da kyau sosai, zatai mun dauri, nace, ta barshi, kawai ta yafa mun golden viel din, da yake kara mine, ta yafo mun bisa kaina, tare da makale mun a kafada, na mike tsaye ina kara kallon kaina, sai kace wata barbie princess, sai ranan na lura da irin jikin dake garen, dirin mu iri daya dana mummy ne, suka saka mun wani pencil shoe mai dan igiya ta baya, shima golden, naji dadin tsinin takalmin, don ya rage jan kasan da rigan keyi, kai kayan gaba daya sai spakling suke yie, ni kaina nasan na hadu, karshen haduwa, ina tunanin tunda nake banta ba yin kyau irin nayau  ba, maybe sai dai ina karama,,,,,,,

matan ta kalleni tana fadin, u are looking so beautiful, kinfi kowa kyau a wanda naima make up yau, ta dakko tab dinta, tana cigaba da fadin,pls let me give u snap,,,,,,,,

falo muka je, tana mun hotuna tace, kai gaskiya aunt dinki, ta futo dake, da sauri nake fadin, itace tazo da wannan kayan, tace, yes ita taxo dasi tun daga egypt, tare muka iso daga abuja this morning, shiru kawai nayi ina tunanin kalaman dazan yi amfani dasu, gun yima aunty jidda godiya, don gaskiya ta taimake ni, ta kuma wanke ni daga lafuzan da Amal tayi a kaina, na rika jin dadi, tare da kosawa in isa gurin, mukai sallama da matan tai nata hanya, nima na shiga mota muka wuce da driver.

Daddy da mummy sun tare manya manyan baki tare da abokan arziki, mubash ma yaxo,da abokansa, mummy tasa Amal tai mishi tarba mai kyau, mummy na sanye cikin wani swiss atamfa na riga da zani tasha dauri, tare da lullube jikinta da babban mayafi wanda yaji kyau da tsada, tana kusa da daddy daya sha malum malum, na wata shadda mai tsadan gaske, gaskiya sun shirya ma abun sosai, abin da wasu suke fada kenan, yayin da wasu ke fadin, ga inda kudinmu suke nan, program sosai akeyi, kafun mummy da daddy su taso zaya yanka cake, Amal biye a tsakiyan su, yayin da aunty jidda tayi tayi da Abdul ya taso, yace, dole sai da ni, zai futa, aunty jidda ta isa inda su daddy ke tsaye gaban wani katon cake, taje ta kusa da daddy, a hankali take fadin, senator a bari yeta meenal taxo sai a yanka cake din,plssalfarma, itama ye'ce, bayi da yanda zaiyi don yana matukar shakkan aunty jidda, dole mc ya sanar da karin minti biyar, yana bada hakuri, yayin da ita kuma Amal ke faman zumbura baki.

*pls kuyi hakuri da yanda page din yake*

so ko wahalah?
*2018*
comment&share

meemartjj💕......✍🏻

thanks💕

SO KO W@H@L@L@H ?Où les histoires vivent. Découvrez maintenant