🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*wannan page din sadaukar wane ga masoyan wannan littafin, naji dadin comment dinku Allah ya saka da alkhairie, Allah ya bani ikon cigaba da rubuto muku wannan littafi cikin dubin alkhairie, comment dinku shine kwarin gwiwa ta a koda yaushe, ina godiya sosai🙏*
vote me on wattpad
*Maamee Ja'afar**page 12~13*
――――Garden site muka sameshi, da wasu abokan nan su, muka isa zarah na fadin, gani, fuska daure baiyi wata wata ba ya wanke ta da mari,cikin zafi yake fadin, uban waye sa'anki nie zan a'ika a kira ki, kicemun sai kin gama kwalliya, kwalliyar banxa ko an fada miki ni irin en iskan samarin kine, Auwal da MD ne suka dafashi suna bashi hakuri, niko tuni nai gafe jiki na rawa na boye a bayan ummee wanda suma suke cike da fargaba, tuni kuma idanuna suka kawo kwalla, ya cigaba da fadin, tell me uban waye ya baki right din daxa ki kawo mun wani dan isaka garden site dina, har ya zauna yaci abinci, who give u that opportunity?,ya karisa maganan cikin tsawa, zarah wacce ke dafe da kumatu tana rera kuka bakinta bai mutu ba gurin fadin, muhsin ba dan isaka bane, muhsin mijin da zan aura ne, kaji ko yaya sagir, an riga da ansa mana ran...wani marin ya kara kawo mata a zafafe, tai saurin hadiye raguwan maganan tana ja da baya, dai dai lokacin da yaya majeed ya kariso gurin shida yaya baffajo yana fadin, sagir pls cool ur temper, yaya baffajo ya kallenu yana fadin, kubar nan, yaya sagir wanda aka dafa, yace, na rantse bazata tafi ba sai tasa veil dinta ta goge gurin nan, su Auwal suna bashi hakuri amma yaki hakura, yaya baffajo yace, mu bashi hakuri da sauri nake fadin, pls yaya sagir kayi hakuri, ya wani ja tsaki, yana huci tare da samun gu yana zama kan daya daga cikin kujerun, ummee dake can gefe ta matso tasa baki, wani tsawa daya musu ba shiri suka bar gurin ya rage ni da zarah dake kallon gefe a zuciye tana zubar hawaye.
kwata kwata banson tashin hankali, don haka na karisa gurin, bisa table din na dauki dankwalina da nake rike dashi a hannu har yanxu, zan share, yaya majeed ne ya kariso inda nake tsaye da fadin, what are u doing? ansa wannan ki share dashi ya miko mun wani farin handkerchief dinsa, na amsa tare da goge gun tas, na kakkabe inda shinkafa ya bata, ina kuma gogewa, naji yaya baffajo na fadin, to gayinan dai sun gogema, yace ta dai goge amma tabbas sai na bata ma yarinyan can rai,baza ta sani azumi hakanan ba, yaya majeed yace, sagir pls kayi hakuri just let them go, wani cikin obokan su yace, cute pretty ta goge maka, SG kai hakuri mana,,,,,
yaya majeed ne ya kallemu fuska daure yana fadin, come on kuzo kuba mutane wuri, na mika mishi handkerchief dinshi zan magana, ya katseni cikin kosawa da fadin, jeki kawai dashi na baki, ku tafi daga nan, nai shiru tare da jan hannun zarah muka bar wajan.
Rai bace yaya sagir yake daura kafa daya kan daya tare dasa yen yatsun sa yana tallafe goshi ya dukar da kanshi alaman damuwa da yawa yake fadin, en iskan yara subar mutum yaji da abun dake da munsa sai sun kara maka dana su, yayi wata doguwar tsaki yana huci,,,,,
duk suka sami gu bisa kujeran suna zama, MD na fadin, wai meya faru ne?da alama an bata ma man dinnan rai, yaya baffajo na dan murmushi yace, inafa lfy, su uncle lamido ne suka baza mishi wuta mu futo da matan aure, Auwal na dan dariya yace, ku futo da matan aure kuma sai kace wasu mata, kasan sune akance su futo da miji, MD ya dubi yaya majeed yana fadin, harda mutumina a ciki, ya karisa maganan yana kallon ya baffajo, ya baffajo yace, a'i shi nashi yafi na kowa ma wai kaji sai ya zabi mata dole a cikin family, sagir kam ko kudin auran yace bashi dasu, MD ya danyi dariya yace, a'i hakan yayi su uncle sunyi dai-dai, don gaskiya kun girma da yawa ko ni nan kwanan nan zanyi aure,a'i hutune, yaya baffajo yace, yawwa mutumin abin da nake kokarin su gane kenan, nifa bani da wata mastala after all ina da wacce nake...cikin masifa ya sagir ya katseshi da fadin, don Allah malam kai ma mutane shiru, don kai kana da wanda kake so, sai kai tunanin wasu basu da matsala, ya baffajo ya dan ja baya alaman karka nushe ni, yace, to sagir naga kana da munira kuma kuna son...wani kallo da ya sagir yai mishi sai kasa da murya yayi yana fadin, uhmm nidai na samu nawa ba canxawa, tsaki yayi yana hararansa, MD na murmushi ya kalli yaya majeed yana fadin, ya abokina meye naka labarin, kaine koh yer girl friend dinnan baka dashi, ga matan su rushing suke akan ka, kaga da duk yazo maka da sauki, yai dantsaki yana fadin, ku wannan ya dama amma ba A/majeed ba, in yaso yau a daura auren, non of my business, Auwal yace, kana nufin ko wacce a baka koda baka sonta, akwai fa matsala ka auri wanda baka so, murmushi yayi yana kallon yanda suka dage da gaske suke suke maganan, shikam ko kadan abun bai da munshi, yace, so?yai wata yer dariya yana cigaba da fadin, *so ko wahalah?* da zaran lokacin daka nuna ma mace kana sonta to ka zama wahalalle, kawai ni abun dana sani, shine umurni, yarinya tai dai dai taga da kyau, in akasin hakan kuma tayi, da kanta zatai ma kanta hukunci, MD yace, hmmm lallai abokina sai a barka, to why not kawai ka fidda Basma matsayin mata kalar kace ita zaku dace sosai, babyn kuma tana sonka,,,,