Chapter 56

1.8K 92 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*

*page 56*

――――Sosai suka sa ihu suna makalkaleshi, don kwata-kwata basu sanda dawowar shiba, harda sister kausar dake sanye da cikin kayan NYSCE, ya bata hannu suka kashe yana fadin,,,

   wow miss copper, nan falo muka zauna momyn na rasa inda zata sa dan nata fadi take,,,

   Abban irin wannan bazata, yai dan murmushi da fadin,,,

   dady bai fada mukuba?munyi waya dashi nace mai jiya zan dawo shi kuma yace mun yayi tafiya yana Abuja, momyn tace,,

   aiko shima ya tafi Abuja jiya, kuma bamuyi hiran dashiba, dama kun saba ku kitsa abunku ku warware, yai dan murmushi yana shafan kai da fadin,,,

  a'ah mommy ba haka bane, ita dai sister kausar ta zuba mana ido, juyi daya sai tace 'kai bro. kunmun kyau', can ta kalli salima tana fadin,,,

   ke salima maza dakko mun phone dina a bedroom, in kwashe red dressing dinnan, kaman ranar val., maryam kuwa na makale tana fsman fadin,,,

  bro. ina tsaraban dana ce ka siyo mun?, ya ciro key zai basu sai kuma ya fasa yana fadin,,,

    ina salim yazo ya ciro jakan, dai-dai nan salim din  ya shigo da sallama, yana ganin yaya majeed din ya fara yin mishi sannu da zuwa, ya amsa yana fadin,,,


  campus student, zauna ka fada mun labarin, first day at college, yana dan dariya ya kalleni da fadin,,,


aunty meenal ina wuni, muka gaisa, ya majeed na mika mishi key su ciro kaya a mota, itako sister kausar sai fadi take munyi kyau, tare da cewa zata bada kayanta a'i mata irin dinkina, aunty mariya ne ta kalleni da fadin,,,

  meenal kunje kun gaida Amal kuwa?, zaro ido na shiga yi ina fadin,,,

  ai bansan bata da lfy ba, yaya majeed ya amsa da fadin,,,

   tayi ciwone?, so serious momyn ke fadin

  harta kwanta asibiti, gaskiya ya kamata kuje ku duba jikin nata kafin ta koma can gidan mijin nata, don ina tunanin tana nan a GRA din, a zuciyarsa yaya majeed e ke raya,,,

    a'i yafi ta koma gidan mijin nata, a fili kuwa sai yace,,,

   in sha Allah, za muje mu dubata, ina tunanin daga nan can zamu wuce, tace,,,

    ok, ku kokarta plss, katuwar jaka ne su salim suka shigo dashi  yaran gidan sai murna sukeyi, don sunsan zasu sha tsaraba,,,

    mun jima a nan don sai bayan isha'i, muka kamo hanya, har mun dauki hanyar GRA, yaya sagir ya kirashi a waya wai suna asibiti, zahra ta haihu, da mamaki ya sauke wayan yana kallona da fadin,,,

    wai kinji zahra ta haihu, nima mamakine ya cikani, har bansan lokacin da nake fadin,,,


  haihuwa kuma, dama haka haihuwan yake sa sauki, murmushi ya saki yana fadin,,,

   bari dai muje, mu gani, hope dai komai lfy, sanda muka isa asibitin, daki na musamman muka samu an bata, domin hutawa, zahra ido ya furfuto, daga gani tasha wuya, duk da haka haj. tace, angode Allah, don bata dade tana nakuda ba, ta haihu, ya sagir kuwa baki yaki rufuwa,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now