Chapter 79

2K 89 2
                                    


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 79*

――――Ya paka motar da wani cin birki, lokacin da sauran yen sanda suka paka nasu motar, duk suka futo, suna bin irin ta'asar da akayi a wajan da kallo, hannayensa bisa kugu yake kaiwa da dawowa, yana dana nazarin yanda lamarin ya kasance, lokacin da wasu daga cikin yen sanda suka fara aune aunen su, da bincike, yayi shiru da wani tunanin, yana bin barayin dama da kallo, kafun ya juya zuwa ga hagu,,

  ya nufa wajan motarsa, wasu yen sandan suka nufi motarsu, dama motoci uku ne, ya shiga nashi, lokacin da wanda suka dafa mishi baya, suka shiga daya daga cikin motocin, harya shiga mota, yake ba sauran umurnin su gaggauta kai wadaddan asibiti mafi kusa, kafun ya sharari hanya, yana ketawa ta site din hagu, tare da tracking shatar tayan motansu, gudu yake na tashin hankali,,,

   suna tsaye daga maboyarsu, lokacin da suke sa ido suka ta inda koda lamari zai baci, karan motocin kawai suka ji, suka juya suna antayawa a guje, sanda daya daga ciki yake dialing numbern dan lutta, wanda ke shirin sharara ma daddy fetur, bayan ya gama fitsaran da ransa yake so, kalman police kawai yake fada mishi, ya saki galan din a kasa, da wani karaji yake musu umurni, da duk subar wajan, ba shiri duk suka fada mota, ya fada cikin karaman honda din, yana fara musu jagora da fisgan mota, wanda yayi sanadiyar tashin hankalin Amal matuka, tana mai tsananin fargaba, a hanya suka hadu da sauran, da kasada suke shiga mota na tafiya, neman tsira suke ta halin kaka.

  sanda suka iso wajan kura ne kawai ke tashi, yaja motar yana pakawa, tare da futowa cikin hanxari, suma sauran suka futo daga nasu motan a tsorace, suna rike da bindiga tare da jujuyawa ta ko wani site, don tsaran lalura, ya karisa inda daddy ke kwance yana fidda numfashi da ker, jini ta hanci ta baki, da sauri yakesa wata yer wuka yana yayyanke igiyan, sanda suke taimakawa da sauri suke sakashi cikin mota, ya tsaya yana son koxai gano wani abu a wajan, sauri sauri yake kalle kalle, harya juya ya tsaya cak, da sauri yake juyawa, idanunsa suka sauka bisa wani design pen cover mai kyaun gaske, sabo dashi, da alamu dashi akayi artabu a wajan,,,

  pen cover, for what?shine abin da yake rayawa, kafun ya nisa yana fadin,,,

   A/majeed wannan ba lokacin tsayawa tunani bane, yasa farin handkerchief yana dauka, tare da wucewa mota, emergency suke saurin isa asibitin, don taimakon rayuwan daddy dake cikin hadari.

   suna isa sukai karo da yen jaridu dake jiran isowan su, nan ko sukai ca a kansu, bayi da lokacin su, har saida yaga anba daddyn daki na musamman, lokacin da akai mishi duk abin daya dace, saidai fa kawai kwance yake, yana numfashi so abnormal, police kawai ke kaiwa da dawowa a wajan, ya isa dakin da aka kwantar da driver da bodyguard din daddy, hankalishi ya tashi, sanda ranshi ya kuma baci, gani bodyguard da nashi ya riga gaba, drivern ne kawai yake halin da daddy yake ciki, har nashima yafi sauki, ya futo sanda yen jaridun suka karayo kanshi, dole wannan karon ya tsaya yana basu bayani.

  ――Lokaci kankani zance ya yada media, yen uwa da dama suka shiga tashin hankali, harda haj. dake faman zagawa bayi, yayin da mummynsu hankali tashe ta kirasa tana fadin,,,

  Abban da gaske ne, abin dana gani a labaru, meya faru ne, da fatan dai basu kashe sulaiman dinba ko?duk ta rude tana maganan, ya numfasa sanda yake fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now