🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**_Da sunan Allah mai rahma mai jinkai_*
*page 60*
――――Ta sulale bisa gado a hankali tana zama, cike da wani tashin hankali a fuskanta, dogayen yatsunta ta zuba bisa bakinta, lokacin da take kokarin maida hawaye, nan ko suka kwaranyo, tana tuna kalaman daddy ma rasa dadi, kawai saita tsinci kanta da sakin kuka,,,
shikam sanda escort ke bude mishi kofa, tsayawa yayi, yana kallon kofan futowa, har sanda ya shiga motan, yana son yaga ta futo, sun tafi, koba komai yasan ta iya lallashin Amal din, kuma Amal din zata fujin dadi, saidai har aka bude gate, suna futa daga gidan bata futo ba, suka dauki hanya ransa bace.
kuka tayi sosai, idanunta harsun kumbura sunyi ja, kafun ta mike tai site dinta, da wani ciwon kai dake damunta, gefen gado ta zauna, tana jingina bayanta, da jikin gado, tare da daga kanta sama, tana dafewa da yen yatsunta take fadin,,,
ya salam, lokacin da zuciyarta, ke raya mata,,,
sa'adatu har yaushe ne zaki samu soyayyan wanda kike so, meye wanda baki mishi da baxai so kiba, tai dan shiru da tunanin, kafun ta dago kai tana cigaba da tuna wani abu,,,
sa'adatu har soyayyan yeyenki kika watsar, duk don mijin naki ya soki, kiri kiri kike nuna musu rashin adalci, tsakanin su da yer da kuka zaba ku kafi so, wata lokacin bawai bata son yeyen bane,,,
tana sane take wasu abubbuwan, kuma duk don son da take ma daddyn ya jawo haka, amman haryau bata samu abin da take fata take buri ba, kawai saita sake sa sabon kuka, sanda wata zuciyar ke raya mata,,,
a'i kodan hakkin yaran nan, ba zaki samu abin da kike soba, suma suna da nasu hakkin a kanki, matsayinki na mahaifiya, ta nisa sanda take fadin,,,
wai wannan duk akan soyayyan wanda har yanxu baya ganinta da kima, har yaushe, gogan nata zai sanja haline, ita dai tana son daddy kuma har yau tana sonshi, sai dai dabi'unsa ne, wasu bata so, kwata kwat...... ringing din wayanta dake bisa mirror ne ya katse tunaninta, kaman ba zata dauka ba, sai kuma ta mike, sunan aunty salma ta gani jikin screen, ta dauka tana kara wayan a kunninta,,,
ta shiga rudu, iya rudu, sanda ake sanar da ita labarin abin dake wakana a zaria kuma, ta katse wayan da salati, tana fadin,,,
mubarak a can, A/majeed a nan, wanka ta shiga sauri sauri, ta futo tana kammala shiryawa cikin wata super, ta yafo gyalen nan babba na alfarma, tare da makale yer jaka, driver ke janta, dai dai zasu futa junction din arean su, tayi karo da wani standard vana, wanda ke dauke da hotan daddyn, a kasa an rubuta _vote Alh. sulaiman gidado Abba, for senate_
kauda kanta tayi, sanda take jin wasu zafafan kwalan nason futowa daga idanunta, tayi saurin maidasu, lokacin da take dada tabbatarwa, ita ba kowan kowa bane agun daddy, tunda harzai kara neman kujeran da yake kai, bai sanar da ita ba, koda wancan ma Amal ne taxo da takardan contesting din, tana nuna mata, ta numfasa lokacin da driver ya mika hanyan zuwa asibiti.