🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?~~~2*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 40~41*
――――Kai tsaye yaa turo kofan, tare da furta kalman sallama a hankali, firgit na tashi ina kankamewa jikin gado kaman zan shige ciki, sai da muka hada ido naga shine, sannan na saki wata ajiyar zuciya ina dan lumshe ido na bude, naga yai wani murmushi yana kasa da kai tare da isowa bakin gadon ya tsaya,,,
sanye cikin wasu kananan kaya, jeans ne, sai wata riga na saki, kaman na sanyi, bata da kauri sosai, sai hannun rigan da yake dogo, ya zuba hannayensa cikin aljifan jeans din, yana zuba mun ido, naga ya wani dauke kai yana wani murmushin, cikin sanyin murya nake fadin,
yaya majeed sannu da zuwa, kallona yake da fadin,,,
yawwa scarry, kin cika tsoro, tsoron me kike jie, kaman zan kuka nace,,,,
tsoro nake nie kadai a gidan, yana kwaikwayon muryana yace,,,,
toh ki daina tsoron tunda gani na dawo gidan, nai dan murmushi, ya saki muryanshi yana cigaba da fadin,,,,
ba kiyi baki bane a gidan?nace,,,
nayi, amman sun tafi, yace,,,,
su waye suka zo?nace,,,,
aunty jidda ne da yaranta, ya dan yamutsa fuska yana fadin,,,,
ok, yayie, zan dan samu wani abu naci?, ina jin yunwa, na gaji sosai, da sauri na duro daga gado, ina tune da fadan da mummy tayi mun, kafun in baro gidan mu, ina fadin,,,,
eh akwai wanda aka kawo daga haunwa, na lunch hade da dinner, yace,,,,
ok muje, hope dai ke zaki serving d'ina, murmushi kawai nayi, naga ya wani d'auke kai yana rigani futa daga d'kin, sai lokacin na tuna, da doguwar rigan baccin dake jikina, duk da rigan na azziki ne, amma ta cika kama jiki, don bata da nauyi sosai, na danji nauyin futa a haka, don haka na saka wani karamin hijjab, kafun nabi bayanshi.
dinning area na sameshi zaune, bisa daya daga cikin kujerun da suke na dinning table din, yai folding hannayensa, yana jirana, white rice din da aka kawo na samishi, tare da stew din da yaji kayana lambu dasu hanta, na isa wajen standard fridge din dake nan dinning area ina dauko drink, tare da zuba mishi a wani glass cup, a hankali na gama jera mishi komai a gabanshi, ina komawa na zauna a dayan kujeran, ya dauki spoon yana kallona da fadin,,,,,
yawwa good girl, Allah miki albarka, nai murmushi, yace,,,
kice Ameeen, na fada kaman yanda yace, sosai naga yaci abincin, kafun ya dauki cup din,dana zuba mai drink ya dan sha, tare da saukewa yana fadin,,,,
Alhamdulillah, na koshi sosai, ya kalleni yana cigaba da fadin,,,,,
oh sorry na manta in miki tayi, nace,,,,,a'i naci nawa dasu Nuwairah, ya jawo tissue cikin kwali yana dan goge bakin shi tare da fadin,,,,,,
ok, kinsan kuwa zarah bata da lfy?sosai na rude ina tambayarsa abun dake damunta, ya dan bini da kallo kafun yace,