Chapter 50

1.9K 108 6
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj*

*page 49~50*

――――Banda nadama ba abun da takeyi, tare da dana sanin dawowanta kasan nata na haihuwa, tana cikin halin bakin ciki, ba abun da bata yiba don ta gudu ta koma india, tare da alkwarin bamai kara ganinta, inhar ta tafi can, sai dai mahaifin nata har passport dinta na barin kasan ya kwace, aure kuma gadan gadan shirinsa akeyi,,,

tayi nadama yafi a kirga, tana data sanin hakura, taje gidan masoyin nata ana biyu, ko don ta samu abin da take so, amman sharrin zuciya ya kaita ya baro, bata ga tsunsu, bata ga tarko, ga wanda ke shirin zama mijin nata ba wani sonshi take yiba, hasalima tana ganin tafi karfin auranshi, ko a wasa bata taba kawowa shi zai zama mijinta ba, sai gashi an daura aure, sati daya ne aka cala da ita can south africa, inda mijin ke a'iki, tai kuka tai bakin ciki, tare da furta kalman *so ko wahala

――Tun sanda na dawo, yake faman rawan jiki dani, tare da bani kulawa na musamman, da farko na tsorata don na gane inda ya nufa, sanda period dina yaxo na lura kwata kwata hakan bai mishi dadi ba, gashi tafiyanshi kwanaki kalilan suka rage, hakanan ya cigaba da gabatar da shirye shiryen tafiyan nashi, ina taimaka mishi da wanda ba'a rasa ba, har zuwa ana gobe zai tafi.

Zaune ya sameni a falon dake site dina, ina bitar karatun hadda, ta wajen kofan site dinshi yaja ya tsaya, yana zuba mun idanuwa, tare da lumshesu sanda yake sauraran kira'an da nake karatun dashi,,,,

kaina na kasa ina karatu, don haka ban lura saya shigo falon ba, sai da nayi mistake, sannan naji yayi knowking jikin kofa, da sauri na dago muna hada ido, ya sakar mun murmushi sanda yake karisowa cikin falon, ina fadin,,,

yaya majeed sannu da zuwa, ya zauna nan kusa dani, jikin mu na gogan na juna da fadin,,,

yawwa sannu da karatu, ya kalleni yana cigaba da fadin,,,

ki kara maimaita ayan da kika biya muji, ba musu na dawo farkon ayan, sanda naxo wajen mistake din kagewa nayi, donni kaina nasan da kuskure, tafin hannuna ya kama cikin nashi, kaman koda yaushe indai muna zaune, yana kallona yace,,,

meya faru ne?cikin sanyin murya nake fadin,,,

tun last week nake samun matsala a nan wajen, yace,,,

ok, to kisamun wani exercise book saiki rubuta ayan da ka, za kiji ya zauna, yanxu zan iya gyara miki, kai na daga alaman eh, sanda ya fara karatun gaba daya tunanina yabar jikina, wani irin kira'a ne mai dadi dashi, yana fidda ko wani harafi yanda ya dace, tare da ba tajweed hakkinsa,,,

ya gama yace in maimaita, haka na maimaita, ya taimaka mun harna kammala karatun suran, na kallesa ina fadin,,,

yaya majeed kira'a mai dadi, murmushi yayi sanda yake janmun hanci da fadin,,,

naki yafi nawa dadi a'i, sanda naji kina karatu, bacci na kusa yie a tsaye, saboda dadin muryanki, ina murmushi nace,,,

kai yaya majeed, da kwaikwayon muryana yake fadin,,,

yes kanwa meenal, ya saki muryanshi yana cigaba da fadin,,,,

yanxu ki fadamun, me kika gani, idan muka sami lokaci na musamman mu rika zama muna musaffa, koda ba hadda bane, inda nake da matsala ki gyaramun, inda kike dashi na gyara miki, ina ganin hakan zai taimaka, rayuwa mai albarka ko?cike dajin dadin kalamansa nake fadin,,,

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now