🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*SO KO W @H@L@H?~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 82*
――――Haraban gida sukai packing din motocin, ya futo yana bin gidan da yayi mishi so strange da kallo, ranshi ya baci sanda ya kalli balcony din upstairs dinshi, Amal kawai yake tunawa sanda sukan zauna suyi ta hira, ya dan rutse ido kafun su karisa ciki,,,
main falo din gidan suka zaune, uncle ibrahim da uncle lamido sai dad dinsu yaya majeed suna tare dashi, gefe kuma aunty mariya ne, suna mishi yer nasiha tare da shawarwari, suka mike sanda yake fadin su karisa upstairs din, yana fama da babban riga, yayi taku biyu kenan, daga kan da zaiyi ya hangeta sanye cikin shigan mutuncin tah, kaman kullum, tasha tsadaddan mayafin nan bisa ka, da swiss lace din da yake kyalli yana kuma kyalli, duk ya rude, da farko yasha gixo take mishi, sai daya ga suna mishi dariya, ya kallesu yana fadin,,,
ammm wai da gaske sa'adat ne? wani dariyan suke mishi, aunty mariya na fadin,,,
kwarai kuwa, ba nace maka ka kwantar da hankalin kaba, indai nie mariya ina raye babu mai dauke maka ita, yana wani yer murmushin farin ciki yake fadin,,,
kai babban yaya tah Allah saka miki da alkhairi, ya kalli su uncle ibrahim yana cuku cuku da malum malum da fadin,,,
tah ina zan fara saba babban rigan nema, hagu ko dama? dariya suke mai shima yana dariya, uncle lamido na fadin,,,
a'ah ka fara ta hagu zaifi, uncle ibrahim yace,,,
no, kadai barshi yafara ta hannun daman, mummy dai ta kariso suna gaisawa, sai binta yake da kallon, dad din su yaya majeed na fadin, kodai su koma ne, sa dawo, haka dai suka karisa ciki suna yer dariyansu ta manya, yana cigaba da amsan manya baki dake zuwa gaisheshi, yayin da mummy tasa masu a'iki ana shirya abin ci dana sha.
Zaune take cikin wani kayataccan purple din rigan bacci doguwa har kasa, mai hannun vest, rigan taji tsada,ta yafo wani karamin viel mare nauyi bisa ka, kala daya da kayan baccin, sai kamshi take na alfarma,,,
tana zaune bisa gadon, tai shiru sai faman tunani take, ya budo kafan bayin ya futo sanye da arebain jallabiya mai tsada, ya dan rage kiban nan, rufo kofan bayin da yayine yasata yin firgigit, tun akan fuskanta ya gane damuwan, ya kariso jiki a sanyaye, bisa site drower da mummy ke zaune kusa dashi ya zauna, tare da dan rankwafowa, yana kamo tafin hannunta cikin nasa, cike da nadama da tausayi yake fadin,,,
sa'adat ki taimaka mun, kiban shawara kan laifukan dana dade ina a'ikatawa, na nuna ma yarana rashin adalci, tsawon shekarun nasa zuciyarki cikin kunci, nayi sanadiyar fasuwan auran Amal, duk akan son zuciya da abin duniya, da wani irin mamaki take zare hannunta, ya kuma rudewa yana fadin,,,
sa'adat plss na tuba, karki gujeni kiban shawara, inajin kunyan laifukan dana a'ikata a baya, musamman wannan yana damuna da yawa, na tsorata sosai lokacin da mutanan nan suka tarfani, ina tsoron in koma ga mahaliccina da wannan zunubin, lokacin biki..... ta katseshi da fadin,,,
lokacin bikin su Amal ko?kai ya daga alamar eh, mummy ta zuba yatsu saman kanta da hawayen dake saukan mata, lamarin daddy harya kai haka, ya rude yana kuma fada mata yayi nadama baxai karaba, ta bashi shawara, dago kai tayi da fadin,,,
daddyn Amal kayi kuskure sosai, amman karka damu, shi Allah mai yafiyane ga bayinsa, mudim bawan nan yayi nadama da tuba irin ta gaskiya, ba abin daya rage maka yanxun daya wuce ka tuba zuwa ga Allah, tuba na gaskiya, da kuma nufin ba zaka kara komawa ga a'ikin sabon nan ba, sannan ka yawaita istigfari, da kuma sadaka, ka gode ma Allah daya kara baka daman cigaba da rayuwa, don ka gyara kuskuren da kayi a baya, saika dage wajen yin amfani da damanka a yanxun, ya numfasa da fadin,,,