Chapter 42

1.6K 100 2
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?~~~2*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻

*Dedicated to mum and dad* 
*wattpad@Meemartjj*

*page 41~42*

――――Idanu kawai yake faman bina dasu, lokacin da ni kuma, nake shirya mishi abincin a gabanshi, na kammala in zama gefe daya kusa dashi, tare da kauda kaina gefe,,,,,

ya jawo plate din dana zuba jalop kuskus din, tare da din ba a spoon, kawai sai naga yayo gun bakina dashi, na dago kai muka hada ido,,,,,,,

cikin sanyi na kada kai alaman a'a, ina fadin,,,,,,,,

na koshi, ya sauke spoon din,cikin plate din, yana kuma bin fuskana da kallo, kawai saijin tafin hannunsa nayi a kuncina, yana shafa gefen idona da fadin,,,,,,

   meya faru, kinyi kuka ne?iduna suka ciko da kwala, na dago kai cike da muryan kuka ina fadin,,,,,

    wani abu ya samu zahra koh?naga ya d'an zaro ido da mamaki, ina cigaba da fadin,,,,,,

tsoro nake jie, wani abu ya sameta, last da muka rabu bata da lfy sosai, na karisa maganan wasu hawaye shar na zuba,,,,,,

  da sauri naga ya saki fuskana, yana jawo wayanshi dake gefe, tare da shiga yana dialing number, ya kara a kunni, shiga biyu aka daga wayan yana fadin,,,,,,

  hello sagir, ya me jikin?kana kusa da ita ne?ya danyi shiru, sannan ya cigaba da fadin,,,,,,,


ok, zata iya magana da meenal?ya miko mun wanyan sanda yake karisa fadin,,,,,,

   ok thanks, amsa nayi ina karawa a kunni, na saki wani ajiyar zuciya mai sanyi, sanda najiyo muryanta a wahale tana fadin,,,,,,


  hello meenal, cike da kulawa nake amsawa da,,,,,

    hello zahra ya jikin naki?tace,,,,,

   naji sauki, nace,,,,,,

    Allah ya baki lfy, bansa baki da lfy ba, amman gobe in sha Allah, yaya majeed zai kawoni in gaisheki, tace,,,,,,,


   toh Allah ya kawoki, sai kinzo, daga haka mukai sallama ina mika ma yaya majeed wayan, shima ya dad'a gaisheta da jiki, sannan sukai sallama da ya sagir yana sauke wayan, yana kuma bina da kallo dake share hawayena, ina kuma tausaya ma zahra, daga maganan tama ya nuna tana jin jiki, ya nisa da fadin,,,,,,,

  duk kin damu kanki, yanxu dai kinji muryanta, kuma tana lfy, sai kici abincin ko?nabi kuskus din da kallo, bana jin cin komai, don haka nace,,,,,,

   nie bana jin yunwa, na rausayar da murya ina fadin,,,,,,,

   don Allah yaya majeed gobe ka kaini, in duba jikin nata, ya miko mun kuskus din a spoon yana fadin,,,,,,

   ok zan kaiki, amman sai kinci abinci, if not kuma, gobe ma in kara tafiya in barki, ba shiri nakai hannu zan amsa spoon din, ya kad'a mun kai alaman in amsa kawai,,,,,,



  ba yadda na iya, dole na amsa ya rika bani, inaci da ker duk na takura, sai gashi naci sosai, don yunwa ko ina jie, abincine na kasa ci, nace na koshi, da kanshi ya zuba mun drink cikin cup yana miko mun, sanda muka kammala, na fara tattara kayan abincin zankai kitchen, shi ya taimaka mun har kitchen da wasu kayan, ya rika bin kitchen din da kallo, naji yace,,,,,


SO KO W@H@L@L@H ?Onde histórias criam vida. Descubra agora