🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W @H@L@H?~~3*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Meemartjj**page 68*
――――Da gudu ta fada jikin mummyn tana mai tsananin farin,ciki, kan kujera suka zauna sanda mummy ke binta da kallon yanda ta sanja, duk tayi baki ta kode, ta shiga bama mummy labarin duk abin daya faru, tana gaya mata yanda ta sha wuya gidan mubash, yanda take tsara maga ke zaki yanke hukuncin ita keda gaskiya, dari bisa dari,,,
ba abun da yafi bata ma mummy rai, irin labarin mutuwar auran Amal, lokaci na farko da taji tana takaicin auran daddy a rayuwanta, mai maimakon ya bi a hankali, cikin lallami, a samu a daidaita zaman auran Amal, shine ma yaje ya zake wajen raba auran, lallai daddy ya wuce duk inda take tunani, ta bi Amal din da kallo sanda take cigaba da fadin,,,
mummy kuma don rainin wayau wai sai daga baya, mubash yake wani kukan munafuncin wai baya so mu rabu, ta dan daga kafada alaman ko a jikinta, tana cigaba da fadin,,,,
nidai koma me, shiya sani, nidai tunda na rabu da virus, na dawo gida, ta marairaice fuska tana kuma fadin,,,
mummy a'i zaki taimakamun anan ma, in samu abin da nake so, tunda kinga daddy ya taimakamun a can, plsss mummy nah nasan kuna son farin cikina, mummy haryau ba wanda zuciyana ke so irin bro. m.....
da sauri mummy ta katseta, don ta tsani taji Amal na ambaton wannan shiriritan, tama rasa inda Amal din ta gado wannan haukan, mijin kanwarta ta rika wannan haukan, cikin takaici ta kalli Amal amman a zahirin gaskiya, saita bata tausayi, ta sani tana son Amal cikin yeyenta, ko don tausaya ma yarinyan da takeyi, ta yanda aka sameta, don haka cikin sanyi take fadin,,,
Amal kinga duk ba wannan ba, yanxu burina bai wuce ki dawo real Amal dinki ba, kinga yanda kika koma, duk kin wani sanja kala, tayi dan murmushi tana fadin,,,
mummy karki damu, tunda yanxu ina kusa dake zan dawo yanda nake, sai nafi dama, ko a can ma, kullum bana iya bacci, tare da cin abinci, koda yaushe ina cikin kuka da tunani, mummy gidan nan ya koma mun kaman prison, shi yasa na koma haka, dai dai nan daddy ya shigo, mummy na masa sannu da zuwa, ina, hankalishi na wajen kalaman Amal, sanda yaji kaman hawaye zasu zubo mishi, sanda take maganan prison, da sauri yayi hanyar up stairs dinshi, yana maida yer kwallanshi, lokacin da yake kara tsanan asirin da yayi ma Amal, duk akan son zuciya, itako tana kwanciya bisa kafadan mummyn take cigaba da fadin,,,
mummy nason yanxu zan dawo Amal dina, tunda inada parent masu sona da kaunar farin ciki na, zaku sha mamakin yanda rayuwana zata sanja, a duk lokacin da kuka mallaka mun abin da nake so, ta karisa maganan cike da farin ciki a fuskanta, lokacin da mummy ke dan dafa kafadan Amal din, da ayyana,,,
a'ikam kina tare da wahalah, babynmu.
――A wannan dare ma, tsoro na rika nuna mai, amman yaya majeed sai da yayi mun wayau, yai amfani da salo salo na soyayyanshi, ya mantar dani wani abu tsoro, lokacin da muka kara lulawa duniyar ma'aurata, sai dai yau kam mai cike da nishadi dajin dadi, dukkan mu mun kasance cikin farin ciki, lokacin da yake kara samun albarka, yana fadin, nita dabance.
Safiyar ranan ma, na shirya cikin wani tsadaddan yadin material, pusher pink, sai kwalliya, mint green a jiki, riga da skirt ne, suma sunmun kyau sosai, na gyara gashina, ina barinshi a bude, rayuwa muka dasa mai cike dajin dadi, lokacin da yace, inbar wani batun girki, sai mun gama cin amarcin mu, ko da yaushe, yana faman yin mana ordern abinci,,,