Chapter 28

1.3K 105 7
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*SO KO W@H@L@H?*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕

*Dedicated to mum and dad*

*wattpad@Maamee Ja'afar*

*page 27~28*

――――Sosai hankalin Amal ya tashi, bata taba ganin dad dinta, ya hanata abun da take soba, kuma ya dage irin haka, don haka hankalinta ya tashi tana tsoron ta rasa majeed, tayi daki da gudu tana kuka, itako mummy ta rasa abun yi, dama tasan za'a rina, don jiya ya gama fada mata, yasa ayi odan kayan auran Amal din, tare da kayan da zai shirya ma ango na musamman,,,,,,

Ta bishi upstairs tana bashi hakuri, tare da rarrashinsa ya sakko, subi abin a hankali, amman yaki sauraranta, sai dada hawa ma, da yayi yana masifa, ta sakko ta dawo gun Amal da lallashi, itama taki sauraranta sai uban kuka da takeyi, ranan harya futo wajen 10am, amma bata futo tayi breakfast ba, yayi shiru sanda yazo har bakin site dinsu, yana jiyo kukanta, yaiji ba dadi, kaman ya shiga ya lallasheta, amma inya tuna da dukiya irin ta Alh.basheer, wanda wata rana zai zama mallakin na mubash, daga mubash kuma sai kan abin da mubash din zai haifa, don haka ya fasa, tare ta fuce fuwww, ya fita abinsh,,,,,,,,

tana hangoshi ta falonsu, inda take labe tana kuka harda na karya, taga wucewarsa ya futa, don haka ta kara saka sabon kuka, na gasken mai sosai, tunda taga ya wuce, bai lallashe taba, tasan akwai matsala babba ba karama ba, tasan kuma da gaske yakeyi, ta rasa yanda zata yie, tana tsoron ta rasa shi, ga daddy yana son yayi mata cikas da wani banzan mubash, wanda shi ke sonta ba itaba, tayi tsaki tana tunanin mafita, ta zabura da sauri, sanda ta tuno da abin da zata yi, don haka ta wuce ciki n sauri tayi kitchen, Allah ya taimake ta, mummy na barayinta, ta bude freezer tana daukan babban waken gwangwani, tare da dawowa falo, dinning area ta wuce, inda breakfast har yanxu ke jiranta, ta zauna kaman abin azziki ta bude gwanwanin, ta dibi madara, ta zabga a ciki sannan ta hada da soyayyan kwan dake wajen, ta zuba ruwan tea ta hada ta juya, tare da komawa ta dakko fanta mai sanyi, sannan ta wuce daki tana zama bakin gado, tana tsoron abun da take shirin a'ikatawa, can kuma tadan daga kafada, tana fadin, i have no choice, daga haka ta shiga tura waken da ker, tana hadawa da fantan, sosai take yin wani irin mahaukacin ci, tayi kusan rabi, cikinta ya soma juya mata, don haka ta boye waken, tana wanke bakinta, tare da komawa ta kwanta, kafun wasu yen mintoci, ta fara zagawa bayi, kafun ace me, sai amai, nan danan ta hautsine tana son fita daga hayyacinta, sanda mummy tazo ta ganta haka, hankalinta ya tashi sosai, don haka ba shiri ta dauketa sai asibiti, ko kan suje sai suma take, suna zuwa kuwa Allah ya taimaka ana samata drip hannu bibbiyu, ta dan dawo cikin hankalinta, lokacin da daddy kuwa yaxo hospital din, ya kasa sukuni, har ta rame, ita kanta Amal din tasan tasha wuya, tana ganinsa ta wani fara kuka, tana kiran sunan bro.majeed, daddy ya zuba mata ido, yana mamakin irin dunbin son da take ma majeed din, ya nisa tare da futa daga dakin, mummy ma ta biyo bayanshi, suka tsaya a wata yer corridor,,,,,,,

mummy na fadin, kaga jikin Amal ko, na rude sosai sanda naga halin da take ciki, da ker take numfashi,daddy yace, munyi magana da doctor yace, jikin nata da sauki, amman muyi gaggawan bata abin da take so, saboda komai zaya iya faruwa, indai bata samuba, ni kaina kuma na tsorata, da ganin yanayin jikin nata, mummy tai murmushi sanda ta tuno plan dinsu da doctor yana neman yin amfani, tayi kasa da murya, cike da rarrashi take fadin, daddyn babyna, don Allah kayi hakuri ka janye maganan auran nan da mubarak, kabarta ta auri wanda take so, tunda shine zabinta, kar yazo taje gidan mubarak, batai zaman so ba, tayi na wahala, pls ka duba lamarin, yayi shiru yana nufa wajen windown dake corridor, tare da juya mata baya, yana zagayo da hannayensa duka ta bayanshi, sannan ya nisa yana tuna irin dukiyar da zasu rasa, ya rasa abin da yasa mummy da Amal, suka kasa gane dunbin dukiyar da zasu rasa, yace, maizan fada ma Alh.basheer sa'adat, mai zance mishi, suna ta shirin aurad da dansu kwaya daya tal, mezan fada mishi, mummy tace, tunda ba a amshi kudin aure ba, ka bashi hakuri, ka fada mishi yanda abun yake, nasan zai fahimceka, shiru yayi da tunanin kalamata, kafun ya juyo yana sakin wani ajiyar zuciya da fadin, hakane, Amal nada right din da zata auri wanda take so, a matsayinta na darling daughter na, don haka ni mahaifin Amal, na yarje ta auri wanda take so, Allah yasa albarka a ciki, mummy ta saki murmushin cin nasara, tana fadin, Ameen daddyn babyna, Allah ya barmu tare, ya saki shima wani murmushi, ta wuce tana fadin, bari na duba babyn tamu, ta wuce, yana dan binta da kallo, yana tunanin yanda suke son maida shi karamin yaro da girmansa, da wayonsa, ya kuma juyawa yana facing waje ta windown, yana tuna irin kyaututtukan da Alh.basheer din ya mishi kwanan nan, tukan a'i auran ma kenan, ina ga anyi auren, shine mummy da Amal suke mishi bakin ciki, ya saki wani murmushin, sanda ya tuna, yanda lamarin zai kasance mishi da sauki, tare da tausaya ma mummy da Amal da suke neman mai dashi wani shashasha.

SO KO W@H@L@L@H ?Where stories live. Discover now