🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*SO KO W@H@L@H?*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍🏻by Haleematu💕meemartjj💕
*Dedicated to mum and dad*
*wattpad@Maamee Ja'afar*
*page 33~34*
――――Tun karfe tara suka dauki hanya, basu suka isa ba sai karfe hudu na rana, can cikin wani kauyen, mai suna bagudu, a cikin garin niger, mutanan kauyen duk maguzawa ne, suka nufi can cikin wani kuryan daji, sunyi tafiya mai dan nisa, sannan suka ja suka tsaya, Alh. sulaiman ne ya futo daga gidan baya, yana faman saba malum malum, amintaccan drivern nashi daya kasance christian, shima ya futo ta barayin zaman driver, ta gaban daddy yazo yana fadin, sir, this is the village, sannan mutumin yana zaune a wancan hut din, ya karisa maganan da nuna wata yer karaman gidan jinka, dake can dan nesa da dasu, daddy ne ya nisa da fadin, ok that's alright, yanxu meye abun yi, driver yace, no problem sir, just wait, am coming, daga haka, yabar wajan, yana zagawa ta bayan gidan jinkan, yabar daddy na faman zare idanu, sai gashi ya dawo yana fadin, sir, ka shiga daga ciki, daddy yai dara dara yana fadin, nan zanje ko?yace, yes sir, karka bari komai ya firgita ka, daddy ya wuce yana fadin, tom, wata yer karaman daki ya gani, shidai baiga kofa ba, amman yaga yen mata biyu rabin jikinsu tsirara, sun juya baya, rike da wata yer kwarya, sai da suka juyo yaji sunce wata kalma, sai gashi cikin dakin zaune, wani jan labule ya raba dakin biyu,,,,,,,,,,,,
can yaji an wani kece da dariya, tare da fadin, welcome to the shirine of maxxi lolo, sannan ne, labulen ya bude, saiga wani kasurgumin kato, tun daga kan fuskarsa har jikinsa zanun nukane, harda gefen idanunsa da yaji farin ali, yasa wani dan bante amman jikinsa ko kaya babu, daddy zaiyi magana ya dakatar dashi da hannu, yana wani yake baki, yake wasu irin magana, ya rika haukata ballanshi, kafun ya kare ya koma ya natsu yana wani dakewa,,,,,,,,,,,,,,
cikin muryan gwaranci, yake fadin, mun sani, munsan abun daya kawoka, money!money!money!in kana dasu ka huta, koma menene bukatanka, anyi anwuce, daddy murya na rawa yake fadin, to nawa kuke so, ya karasa dariya sannan yayi shiru na wasu minutes, kafun ya kalli daddy da fadin, na yanxu just 1million, daddy ya zaro ido, cikin tsawa yake fadin, u are very lucky, a'ikinka bayi da yawa, daddy yace, yes maxxi lolo, naji kace na yanxu 1million,,,,,,,,, ya katse daddy da daga yatsun hannayensa duka, yana lankwasa guda daya, yace, a'kinka na 10million, zaka bamu 1million for now, after the wedding kuma zaka zo mana da cash na million haka, ya fadi maganan yana kuma daga yastunsa guda tara, ba tare da ya kalli daddy ba, ya cigaba da fadin, in babu kudin after the wedding, komai zai iya faruwa da auran yaronka!, ya karisa maganan cikin tsawa, cikin daddy ya wani kulle, amman daya tuno da dukiya irinta Alh.basheer, sai yace zaije mota ya kawo musu, haka kuwa akayi, ya ije kudin bisa wani jan kyalle, mutumin ya soma fadin, just go!a'ikinka an gama, sai wanda kakeso yaronka zai aura, ask her one more time, just remember our balance of 9million, ko kuma, yaronka after six month, komai zai faru da auranshi, da wannan daddy ya tattaro yer malum malum dinshi suka bar kauyen, da fatan samun nasara, duk da wani sako a zuciyarsa, na raya masa bai kyauta ma darling daughtern nashi ba, na rabata da abin da takeso, sannan kuma laifine babba ya a'ikata a addininsa, amman son zuciya da abin duniya sun rufe mishi ido, yana raya nan gaba zataji dadi, buri da fatansa kenan, sannan zai dage da istigfari, bazai kara a'ikata laifi irin wannan ba, dama bai taba yiba, wannanne na farko kuma na karshe, burinshi kawai Amal ta amsa auran wanda yake son ta aura, wa'iyazubillah, daday an kauce hanya.
Bayan an kammala walima kuma, Amal da kwayenta suka nufi boys quarters, suka saka waka, kowa ta tsuke, rawa sosai suke, harda Amal dasai dai kaji ana saka ihu, lokacin nida zarah muna zaune, a dan gurin wani shakatawan mu, dake compound din gidanmu, wanda ke facing barayin packing space, dama ita ummee nacan cikin manya sa'aninta matan aure, tasha gorin manyancenta gun zarah harta gaji, muna jiyo sautin waka daga BQ, zarah na fadin, bacin aurena da yanxu inacan, mu kasa dariya, ina fadin, lallai ya sagir yaji ance kinyi rawa, a'i sai ya dakeki, tayi murmushi da fadin, swedie na sarkin rigima, yanxu muka gama waya dashi, wai after isha'i zaizo hira, wani dariyan mukasa ina fadin, hira kuma, tace, ehmana kinsan har yanxu saurayi yake ni kuma budurwa, sannan nayi missing dinshi sosai, wannan karon 4month yayi a wajen a'iki fa, yanxu ma bikin nan ya dawo dashi, nai dan murmushi da fadin, kinji dadi, ke naki ya kare da kyau, tace, me yasa kikace haka?na mike ina fadin, mu shiga ciki an kusa kiran sallan magrib, ta mike mukai cikin gida.